logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi kira da a mayar da AIIB sabon dandalin ingiza cigaban mambobinsa da ma gina al'umma mai makomar bai daya ga bil Adama

2020-07-29 13:57:04 cri

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi ta kafar bidiyo a yayin bikin bude taron shekara shekara karo na 5 na bankin zuba jarin samar da ababen more rayuwa na Asiya ko AIIB a takaice. Inda ya jaddada cewa, a karshen shekarar 2013, a madadin al'ummar Sin, yana ba da shawarar kafa bankin AIIB, a kokarin sa kaimi ga ci gaban muhimman ayyukan more rayuwa na yankin Asiya, da inganta hadin kai da cudanyar juna, ta yadda za a iya samu bunkasuwa baki daya. A karon farko cikin shekaru fiye da 4 da suka gabata tun bayan kafuwarta, yawan mambobin bankin AIIB ya karu daga 57 zuwa 102 daga nahiyoyi shida a halin yanzu. Lamarin da ya nuna kwarewar bankin a fannin aiki, inganci, da ma rashin cin hanci da rashawa.

Shugaba Xi Jinping yana mai cewa,

"Yadda daukacin duniya ke dakile yaduwar annobar numfashi ta COVID-19 ya nuna cewa, dan Adam yana da makoma ta bai daya. Ko shakka babu, ta hanyar nuna goyon baya ga juna, da hada kai tare ne kawai za a iya warware matsalolin da ake fuskanta. A yayin da ake kokarin warware matsalolin da suka bullo, a yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, ya kamata kasashe daban daban su kara yin hakuri da juna wajen gudanar da harkokin duniya, kana su kare tsarin cudanyar bangarori da dama da ya dace, da kuma yin hadin kai mafi yakini a yankin. Kamata ya yi bankin AIIB ya kasance wani sabon dandali tsakanin kasashe mambobinsa, wanda zai inganta samun bunkasuwa tare, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dan Adam."

A cikin jawabin, shugaba Xi ya ba da shawarwari guda hudu kan ci gaban bankin AIIB, wadanda suka hada da na farko, ya kamata a mai da hankali kan batun samun bunkasuwa tare, a kokarin ganin bankin ya zama wani sabon dandali da ke iya ba da gudummawa kan ci gaban duniya. Don haka ya kamata bankin ya dukufa wajen biyan bukatun dukkan mambobinsa, da ma zuba jari kan wasu manyan ayyukan more rayuwa masu inganci da dorewa da ba a kashe makuden kudade. Ban da goyon bayan raya tsoffin manyan ayyukan more rayuwa, ya kamata bankin ya mara baya ga wasu sabbin nau'o'in ayyukan, a kokarin samar da sabon karfi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen Asiya da sauran yankunan duniya.

Na biyu, ya kamata a dukufa kan kirkire-kirkire, a kokarin ganin bankin ya kasance wani sabon dandalin raya duniya da ke tafiya tare da zamani. Domin cimma wannan burin, ya kamata bankin AIIB ya sabunta matakansa na ci gaba, da salon gudanar da ayyukansa, da hanyar tafiyar da harkokinsa, da ma raya abubuwan hada-hadar kudi bisa hanyoyi daban daban, ta yadda za a iya sa kaimi ga cudanyar juna, da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da ma goyon bayan ci gaban fasahohi.

Shawara ta uku da Shugaba Xi ya bayar ita ce, a gudanar da wasu ayyuka masu inganci, a kokarin ganin bankin ya zama wata ingantacciyar sabuwar hukumar hadin kan kasa da kasa da babu kamarta. Ya kamata bankin ya hada ra'ayin martaba ka'idojin duniya da bukatun ci gaban mambobinsa tare, domin gudanar da wasu ayyuka masu inganci da za su iya amfana wa jama'a sosai.

Shawara ta karshe ita ce, a ci gaba da bude kofa da yin hakuri da juna, a kokarin ganin bankin AIIB ya kasance wani sabon abin koyi ta fuskar hadin kan kasa da kasa. Domin cimma wannan burin, Xi ya ce, ya kamata a martaba ka'idar yin shawarwari tare da raya ayyuka tare da more sakamako tare, da dacewa da sauye-sauyen da duniya ke fuskanta, da ma hadin kai tare da karin abokai, a kokarin da ake na dunkulewar tattalin arzikin shiyya-shiyya gu daya, da ma taimakawa duniya wajen samun ci gaba bisa hanyoyin bude kofa ga juna, da hakuri da juna, cin gajiyar juna, samun daidaito, da cimma nasara tare.

A karshe Xi ya jaddada cewa,

"Ko da yaushe kasar Sin na tsayawa kan nuna goyon baya, da martaba ra'ayin kasancewar bangarori da dama, da kuma bin tunanin bude kofa ga kasashen waje, da hada kai da samun nasara tare, a kokarin samun ci gaba tare da kasashe daban daban. Haka kuma kasar Sin za ta ci gaba da kokari tare da kasashe mambobin AIIB, don nuna goyon baya da gudanar da ayyukan bankin yadda ya kamata, kana za ta kara taka rawa a fannin tinkarar kalubalolin da kasashen duniya ke fuskanta, da tabbatar da samun bunkasuwa tare."(Kande Gao)