Ya kamata Sin da Amurka su kai zuciya nesa
2020-07-29 09:44:22 CRI
A kwanakin baya ne, mahukuntan Amurka suka bukaci kasar Sin da ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake birnin Houston, wannan mataki tamkar takala ce irin ta siyasa, kuma maras dacewa, da ka iya kara lahanta dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.
Gwamnatin Amurka dai ta bukaci dakatar da dukkanin ayyukan da ofishin kasar Sin dake Houston ke gudanarwa cikin wani kankanin wa'adi, wanda hakan ya yi matukar sabawa dokokin kasa da kasa, ya kuma yi karan tsaye ga ka'idojin cudanyar kasa da kasa, da ma yarjejeniyar da sassan biyu suka amincewa a fannin ayyukan diflomasiyya.
Bangaren Sin dai ya yi matukar Allah wadai da wannan mataki, kasancewar har kullum, Sin na iya kokarin ta wajen martaba ka'idar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya. A duk tsawon shekarar nan ta bana, ofisoshin jakadancin Sin dake Amurka ciki hadda na birnin Houston, na gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, bisa tanadin yarjejeniyar Vienna mai nasaba da cudanyar diflomasiyya, da burin kyautata yarjejeniyar dake tsakanin Sin da Amurka, da musaya da hadin gwiwa, tare da fadada fahimtar juna, da kawance tsakanin al'ummun sassan biyu.
Bayan wannan mataki na Amurka, kasar Sin ta fitar da sanarwar da ta bayyana dukkan zarge zargen da Amurka ke yi wa Sin, a matsayin marasa tushe ko makama, sai dai idan har burin Amurka bai wuce tsangwamar kasar Sin ba, to kuwa har kullum ba za ta gaji da zakulo dalilai marasa tushe na yin hakan ba.
Sai dai, ita ma kasar Sin ta mayar da martani kamar yadda doka ta tanada, inda ita ma ta bukaci Amurkar da ta dakatar da ayyukan karamain ofsihin jakadancinta dake Chengdu. Masu fashin baki na cewa, kamata ya yi kasashen biyu, kasancewarsu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, da su kai zuciya nesa, tare da nemo bakin zaren warware wannan takaddama. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)