Liu Guohong: Ta taimakawa manoman garinsu, ta hanyar amfani da intanet
2020-07-27 19:36:34 CRI
Yankin Pinggu yana arewa maso gabashin birnin Beijing na kasar Sin, ya kuma shahara ne sakamakon wani na'unin 'ya'yan itatuwa mai suna peach a Turance. Don haka, ake kiran yankin "Garin Peach na kasar Sin". Peach da ake nomawa a yankin Pinggu, yana da dadi sosai, saboda yadda Allah ya horewa yankin ruwa, kasar noma mai kyau da kuma hasken rana.
Mazauna wurin masu yawa suna samun kudin shiga ne, ta hanyar dogaro da noman peach. A da ko da yake suna shan wahala wajen noman peach, amma kudin shiga da suka samu ba shi da yawa, yanzu dai halin da suke ciki ya kyautatu sosai, sakamakon bunkasuwar intanet, da kuma wasu matasa dake da burin ciyar da garinsu gaba, ciki har da wata yarinya mai suna Liu Guohong. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da wannan matashiya.
Kafin a samu bunkasar sana'ar intanet, a kan sayar da peach ne ta hanyar gargajiya, liu Guohong ta yi waiwaye cewa,
"A lokacin da nake yarinya, iyayenmu ma suna noman peach sosai. Su kan fara tsinkar peach ne da karfe 2 na yamma har zuwa karfe 7 na dare, bayan sun kammala, sai su kwashe su zuwa cikin gida, kana washe gari daga karfe 3 zuwa 4 na safe, sai a saka su a mota, daga gidanmu zuwa kasuwar, tafiyar kusan awa daya ne, akwai 'yan kasuwa manya da kanana da suka fito daga wurare daban daban na kasar da suke jiran peach din. 'Yan kasuwan suna da yawa, haka masu sayar da peach din ma, wannan ya sa ba a samun kudin shiga da yawa."
Liu Guohong ta ce, mahaifinta ya taba gaya mata cewa, RMB yuan 50 kawai ya samu, bayan da sayar da peach da yawansu ya cika babbar mota. Ya yi bakin ciki sosai, don haka ya cire dukkan itatuwan peach dake gidansu. Lallai, kamar yadda gidansu yake, a lokacin yawancin manoman garinmu sun sha wahala sosai, amma kudin shiga da suka samu ba shi da yawa.
To, yaya aka canja irin wannan halin da ake ciki? Liu Guohong ta gaya mana cewa, bisa ci gaban sana'ar intanet, an bude wata sabuwar kofar sayar da kaya ta intanet, ko a sayar da kaya ta hanyar dandalin sada zumunta na Wechat, ko kuma ta kafar bidiyo kai tsaye, ta ce,
"Mun soma sayar da kaya ta kafar Wechat, aiki na shi ne sayar da kaya, na fito ne daga yankin Pinggu, don haka, na kan baiwa 'yan kasuwa kyautar peach. Peach din da na ba su yana da dadi sosai, kuma ya samu karbuwa sosai, daga baya, mutane da yawa su kan tambaye ni, ko za ki sayar mana irin wannan peach din?"
Ganin haka, sai Liu Guohong ta soma tunanin wannan shawara. A ganinta, kamfaninsu na gudanar da harkoki game da intanet, don haka abokan aikinta sun kware a wannan fannin. Liu Guohong ta gaya mana cewa,
"A watan Agusta na shekarar da ta wuce, wasu abokan aikina sun zo gidana mu hutu, a yayin da muke hira, sai na kawo musu wannan batu, nan da nan dukkansu sun nuna sha'awa sosai a kai. A don haka, tun da dukkanmu muna sha'awar aikin gona, kuma muna da kwarewa a fannin intanet, me ya sa ba za mu yi wasu abubuwan da za mu taimakawa manoma yankinmu ba?" Ba tare da bata lokaci ba, sai Liu Guohong da abokan aikinta sun soma tsara wata mahanja a dandalin Wechat, don sayar da 'ya'yan itatuwa bisa yanayin da ake ciki.
Liu Guohong ta bayyana cewa, tana gabatar da nau'o'in peach din da ta karba daga wajen manoma a fannonin yawau da girma da kuma nauyinsu. Bayan wani lokaci, sai ta amince da ingancin kaya na manoma, Game da wadancan ba ta saba da su ba, za ta dandana tukuna. Amma, saboda har yanzu tana aiki ne a kamfaninsu, don haka, ba ta da isasshen lokaci wajen duba ingancin peach, iyayenta su kan taimake ta.
A cewar Liu Guohong, bisa yaduwar intanet a nan kasar Sin, farashin peach shi ma ya karu, ya zuwa yanzu ya ninka har bisa na shekaru hudu da suka gabata. Ta ce,
"Ban da peach kuma, muna kuma sayar da wasu kayayyakin aikin gona na sauran wurare, saboda manoma suna fama da aiki sosai, muna fatan amfani da kafar intanet zai taimaka musu wajen kara samun kudin shiga."
Bayan haka kuma, Liu Guohong ta gaya mana cewa, a hakika, su kansu ba su samun kudi da yawa ta wannan hanyar sayar da kaya, sun yi haka ne domin su kware gami da sha'awar da suke da ita a fannin, musamman ma suna fatan taimakawa mutane da yawa ta yadda za su samu wadata.