logo

HAUSA

MAYAR DA FILIN WASA GIDA

2020-07-23 15:07:42 CRI

MAYAR DA FILIN WASA GIDA

 

A duk lokacin zafi, lokaci ne da Zhang Hui ke mike kafa, lokaci ne na samun karin bacci, da kallon TV, da zaman kan kujerar mike jiki. Amma a bana Zhang na da wata dabara: "A wannan karo, Ina so na 'kawo filin wasan motsa jiki cikin gida, ta yadda zan samu hutu daban da na baya."

Bullar cutar numfashi ta COVID-19, ta sa ba bu daliban Zhang hui ko daya da suka samu damar komawa jami'a. Tun daga lokacin hutun hunturu zuwa lokacin bazara, mafarkin sa na zuwan lokacin hutu bai cika ba, duba da cewa fatan Zhang Hui, na Allah-Allah da zuwan wannan lokaci ya bi ruwa, sakamakon wannan yanayi na murna da ya sauya, saboda bullar cutar COVID-19. Zhang Hui ya fara rasa damar zuwa filin wasan kwando da yake halarta. A yanzu ya fadawa kan sa cewa "Na jima a gida, yanzu lokaci na motsawa ya yi". Rahotanni daga majiyoyi na al'umma. Bisa tanadin dokokin yaki da wannan annoba, mafi yawa daga daliban kwalejoji, ba su koma makaranta ba, kuma filayen wasa, wadanda a baya ke cika da dalibai a yanzu haka sun koma ba kowa. A gida kuwa, manya da matasa, ba sa samun isasshen wuri mai wadatarwa domin motsa jiki. A hannu guda kuma, da yake akwai damammakin samun horo na dabarun motsa jiki ta yanar gizo, al'adar koyon karatu cikin rikunonin dalibai na nan na gudana, sai dai kuma abu ne mai wahala a samu damar gudanar da motsa jiki ta hanyoyi na zahiri. Bisa hakan kuma, dalibai da dama suka tara kiba, kuma za su rasa karsashin su na wasanni bayan sake bude ajujuwa. Wannan ne kuma ya sa ake da bukatar gaggauta zaburar da rukunonin dalibai, su shiga harkokin motsa jiki. A yau, da yake daukacin matakan dakilewa, da na shawo kan wannan annoba sun bunkasa, dukkanin sassan rayuwa na Sin na komawa bakin aiki, ana kuma ci gaba da sarrafa hajoji bisa tsari, yayin da kuma rayuwar mutane ke komawa yadda aka saba sannu a hankali. Hakan ya sa a 'yan kwanakin da suka gabata, babbar hukumar wasanni ta kasar Sin, ta fitar da wani tsari na yayatawa, da komawa bakin aiki a fannin wasanni, ta hanyar shirya gasanni da ayyuka na kimiyya masu nasaba, don gaggauta komawa bakin aiki, da samar da hajojin wasanni da ake bukata. Da yake matasa ne mafi yawan masu halartar wasanni da ake shiryawa, sake bude wasannin a makarantu shi ne mafi muhimmanci. A baya bayan nan, kamfanonin Tencent na wasanni, da Tencent na bidiyo sun yi hadin gwiwar shirya kashi na 3, na gasar "Supernova sports", inda cikin tsarin suka bayyana "shirin sake bude filayen wasanni ", kana suka gayyaci Yang Yunqing, da Yu Xiaotong, da wasu karin taurarin 'yan wasa 10 a matsayin jakadun sake bude wasanni a filayen da ake da su, inda suka rika aikewa dalibai gayyata, mai dauke da sakon "Mu yi Shewa don nuna kauna!.A lokaci daya kuma, shirin ya nufi jami'ar "southwest Jiaotong", da jami'ar "Electronic Science and Technology", inda ya yi kira ga malamai da dalibai, da su sake bude wasanni da ake gudanarwa a filayen su. A wurin da aka kaddamar da wannan shiri, Mr. One, wanda ke wakiltar jagorancin taron "Supernova sports", ya samar da wata tabarmar YOGA iri daya, a matsayin kyauta ga daliban da suka kammala karatu. Yana mai kira gare su, da su tafi da harkokin wasannin su gida, ta yadda daliban ba za su yi watsi da batun wasanni ba a lokacin da suke yin hutun lokacin zafi, za su kuma shirya sake bude filayen wasanni da zarar an shiga kaka ta gaba. AN GAMA DUKKANIN SHIRI Alal hakika, na jima ina zaman gida, har ta kai bana iya motsawa da sauri. Wannan ya zaburar da ni, tsarin ya bani damar sauya tunani na komawa makaranta cikin kyakkyawan yanayin jiki. "Ma Li ke nan, dalibi a jami'ar "Southwest Jiaotong" wanda ke bayyana shirin sa na komawa motsa jiki a wannan lokaci. Ma Li ya ce "Wannan tabarmar YOGA ba ta yi kama da suffar filin wasa ba? Saboda zafi abu ne mai wahala yin motsa jiki a waje, don haka zan rika yin YOGA a cikin gida." Shi kuwa Wang Peng, dalibi a jami'ar "Electronic Science and Technology of China", yana daf da fara karatun digiri na 2 a watan Satumba. A wannan lokaci na zafi, ya halarci shirin "mayar da wasa gida " ya kuma maye gurbin aniyarsa ta zuwa yawon bude ido da wasan motsa jiki. Ya ce "Tabbatar da karfafa jiki, shi ne buri na a wannan karo!" A lokaci guda kuma, Wang ya yi kira ga sauran al'umma dake kusa da shi da su yi aiki tare. Ya ce "Muna sanya ido, da karfafawa juna gwiwa a fannin wasanni, ta haka za mu samu karfin halin ci gaba da himma." A matsayin masu bunkasa wasanni a makarantu, rukunonin malamai sun gamsu da shin "sake bude filayen wasanni ". Wani malami ya bayyana cewa, sake bude wasanni a kwalejoji, wanda aka dage tsawon lokaci, a ra'ayi na ya ja hankalin al'umma, ya kuma tunatar da dalibai bukatar sake mayar da hankali ga komawa wasanni a filayen makarantu da ake da su. Ya ce hakan kyakkyawar dama ce ga dalibai, ta gano irin nishadantarwa da ma'ana da wasanni ke iya bayarwa. Wannan shi ne makasudin shirin na ainihi. Daga jami'ar "southwest jiaotong" zuwa ta "electronic science and technology", burin shi ne daliban kwalejoji da na jami'oin, su rungumi wannan shiri na "Sake bude filayen wasanni ". Gasannin "Supernova" na ingiza damar samun kuzari ta hanyar jan hankalin matasa su koma filin wasa, suna farkar da matasa su shiga a dama da su a harkokin wasanni, ta yadda za su zama zakaru, masu cike da kwarin gwiwar motsa jiki a gabar da ake kara azamar yaki da COVID-19, matasan za su kara karfafa lafiyar su da lafiyar kwakwalwar su, don tunkarar kalubalen rayuwa yadda ya kamata. HADE WASA DA KOYO DAGA GIDA Duk da kirarin da ake wa matasa da masu jin karfi a jikin su, wasu alkaluma sun nuna irin yadda yara da matasan Sinawa ke fuskantar kalubale a fannin karfin jiki. A cewar hukumar lafiya ta kasar, matsalar ido tsakanin yara kanana da matasan kasar ta kai kaso 53.6 bisa dari a shekarar 2018, kana adadin masu nauyi fiye da kima, da kiba ya kai kaso 16 bisa dari. Cheng Hong, mamba ne a kwamitin kasa na majalissar ba da shawara kan harkokin al'umma ta kasar Sin ko CPPCC a takaice, shi ne kuma mataimakin shugaban kwamitin "Democratic League" na kasar. Ya ce yayin taruka biyu na bana, an bayyana cewa, alkaluman auna kuzarin yara kanana da matasa na kasar Sin sun ragu, cikin sama da shekaru 20 a jere, inda kaso 33 bisa dari na rukunin su ke fama da matakai daban daban na kalubalen kiwon lafiya. A gabar da ake samun irin wannan raguwa ta alkaluman kuzarin yara da matasa a Sin, abu ne da dukkanin al'umma ta amince da shi, cewa dole a farfado da al'adar shiga wasanni, ta yadda za a zaburar da matakan samun karfin jikin wannan rukuni na yara. A matsayin su na hanyoyin gina al'adar shiga wasanni a zukatun matasa, wasanni da ake gudanarwa a filayen makarantu suna da matukar muhimmanci, sai dai kuma sun dasa aya ga wannan manufa sakamakon bullar COVID-19, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen rage kuzarin wasannin da matasa ke shiga. A yau, yayin da yanayin yaki da wannan annoba ke kara kyautata, ya zama dole a kara azama wajen karfafa gwiwar matasa, wajen zage damtsen shiga wasannin motsa jiki da na inganta lafiyar su. Zhang Wenhong, shi ne darakta a sashen lura da cututtuka masu yaduwa a asibitin Huashan dake karkashin jami'ar Fudan. Yayin wata tattaunawa da manema labarai, ya ce game da batun matsayin yaki da wannan annoba, ana iya cewa mafi yawan mutane suna da damar sake fita su yi zirga zirga kamar yadda suka sama a baya. Ga wadanda matasa ne, ya dace su zamo cikin kuzari. Domin dacewa da bukatun kandagarki, da na shawo kan wannan annoba, an samar da dabarun gudanar da motsa jiki da ake iya yin su, ana kuma iya kirkirar wasu hanyoyin motsa jikin." Shirin "sake bude filayen wasanni" hanya ce ta amsa kiran mahukunta, na sake komawa wasanni a makarantu cikin kuzari, tare da zaburar da karsashin matasa a fannin wasanni. Wadannan matakai masu muhimmanci, su ne za su hore damar zurfafa dabarun sake farfado da wasanni bisa tsari cikin wannan al'umma. A matsayin mafari na wannan manufa, Gasannin "supernova" na kunshe da tarin ababen mora a yanar gizo, da karfi na zakarun dake marawa shirin baya, da inganta hadin gwiwa tsakanin sassan, wanda hakan ke baiwa bangarorin masu ruwa da tsaki damar taka rawar da ta dace, za kuma ta baiwa karin matasa damar ba da gudummawa a ciki, hakan yana karawa su kan su wasanni armashi, da wuraren yin su, kamar filayen wasannin lokacin sanyi, da farfado da dukkanin fannin wasan, da ma zaburar da fannonin da suke da nasaba da hakan, wajen ba da gudummawa ga ci gaban daukacin al'umma. Yayin da ake kara fitar da tsare tsare irin su "Sin mai cike da lafiya nan da shekarar 2030" da shirin aiwatar da "ka'idojin gina karfin wasanni", batun gaggauta karfafa lafiyar jikin matasa ta hanyoyin motsa jiki na kan gaba, wajen samar da al'ummar kasa mai kuzari, mai kuma cike da koshin lafiya.

Idan an yi hangen gaba, ana iya lura da cewa "Sake farfado da shirin bude filyayen wasa "baya ga kiran dalibai da zai iya yi "su mayar da wasanni gida ", a hannu guda kuma, zai taimakawa matasan su sake farfado da halayyar su ta motsa jiki da samun kuzari. Bugu da kari, ana fatan hakan zai sa al'umma kara kaunar wasanni, wanda hakan zai haifar da bunkasuwar kuzari, da inganta lafiyar jikin al'ummar Sinawa baki daya.(Amina, Saminu)