logo

HAUSA

Burin kasar Sin shi ne tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya

2020-07-22 18:53:36 CRI

A kwanakin baya ne jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ta cika shekaru 99 da kafuwa. Jam'iyya da ta fara da mambobi sama da hamsin, yanzu ta zama jam'iyya mafi girma a duniya.

Burin kasar Sin shi ne tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya

A yayin da wannan jam'iyya da mambobinta ke ci gaba da inganta rayuwar al'ummar Sinawa da ma ba da gagarumar gudummawa ga ci gaban duniya. Sai ga shi takun saka na kokarin kunno kai tsakaninta da mahukuntan Amurka bisa dalilai na kare muradun kasa.

Tun lokacin da gwamnatin kasar Sin ta fara daukar matakan aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin musamman na Honk Kong na kasar ta Sin da matakan yaki da ta'adaddanci da tsattsauran ra'ayi a yankin Xinjiang, sai na baya-bayan nan batun aikin samar da fasahar 5G na kamfanin Huawei, kasar Amurka ke ganin irin wadannan matakai, sun ci karo da muradunta ko kuma za su hana ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, wannan ya sa, Amurka ta aiwatar da dokoki da sunan kare hakkin dan-Adam ko demokiradiya a yankin Xinjiang ko yankin Hong Kong, har ma take cewa, tana duba yiwuwar sanyawa jam'iyyar kwaminis da mambobinta takunkumin hana su shiga kasar ta Amurka.

Burin kasar Sin shi ne tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya

Koma mene ne, abu mafi dacewa shi ne hadin kai tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, maimakon sanyawa juna takunkumi ko shiga harkokin cikin gidan juna. Kasar Sin dai ta sha nanatawa cewa, burin ta shi ne tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya, ba yin fito na fito ko takalar juna ba. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)