Ya kamata 'yan jaridun Sin da Afirka su karfafa hadin-gwiwa wajen ruwaito rahotanni masu inganci dangane da ayyukan yaki da COVID-19 <?xml:namespace prefix = "o" ns = "urn:schemas-microsoft-com:office:office" />
2020-07-21 12:25:22 CRI
A kwanakin baya, an yi wani taron karawa juna sani tsakanin 'yan jaridun kasar Sin da kasashen Afirka a Beijing, inda shugabannin kungiyoyin 'yan jaridun Sin da Afirka, da wasu gogaggun manema labarai na bangarorin biyu suka hallara, domin bayyana yadda suke ruwaito rahotanni dangane da ayyukan yaki da cutar mashako ta COVID-19 a kasar Sin da kasashen Afirka, a wani kokari na inganta hadin-gwiwar kafafoin watsa labaran bangarorin biyu domin bada gudummawa ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya na Sin da Afirka. Taron, wanda aka yi shi ta kafar sadarwar Intanet, ya samu halartar 'yan jaridun kasar Sin da na kasashen Najeriya da Sudan da Masar da Rwanda da Kenya da Tanzaniya da Cote D'ivoire da sauransu.
Sakataren sakatariyar kungiyar hadin-gwiwar 'yan jaridun kasar Sin, Mista Tian Yuhong ya gabatar da jawabi, inda ya ce, cutar numfashi ta COVID-19, cuta ce mai kamari wadda ta bulla ba zato ba tsammani, kuma tana haifar da babbar matsala ga lafiyar bil'adama da harkokin watsa labarai na kasa da kasa. Domin karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin 'yan jaridun Sin da Afirka, kungiyar hadin-gwiwar 'yan jaridu da aka kafa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kira irin wannan taron karawa juna sani. A watan Satumbar shekara ta 2019, kungiyar 'yan jaridun kasar Sin da kungiyoyin 'yan jaridun kasashen duniya da suka shiga cikin ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya" suka hada kai domin kafa irin wannan kungiya, wato kungiyar hadin-gwiwar 'yan jaridu da aka kafa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya".
A cewar Mista Tian Yuhong, a halin yanzu annobar COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya, inda kafafen yada labaran kasa da kasa suke taka muhimmiyar rawa wajen gabatar da rahotanni masu inganci da labarai na gaskiya dangane da ayyukan yaki da cutar, da yadda za'a raba fasahohin dakile cutar, a wani kokari na karfafa gwiwar al'ummomin kasashen duniya kan ganin bayan annobar.
Mista Tian ya kuma gabatar da wasu muhimman shawarwari uku game da yadda za'a karfafa hadin-gwiwa tsakanin kafofin watsa labaran Sin da Afirka wajen ruwaito rahotanni game da cutar COVID-19. A cewarsa, na farko, ya kamata a goyi-bayan ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya, wato kin yarda da ra'ayin nuna bangaranci da wariyar launin fata. Tian ya yi kira ga kafafen yada labaran Sin da Afirka su nuna adawa ga aikin bata sunan wata kasa, da kare muradun kasashe masu tasowa, da shimfida adalci a duk duniya. Na biyu, Tian ya ce ya kamata a ruwaito rahotanni bisa kimiyya da fasaha. Wato a cewarsa, tun bullar cutar, akwai wasu 'yan siyasar kasashen yammacin duniya wadanda suka yi karya da yada jita-jita dangane da asalin cutar, kuma abun da suka aikata, ya rura wutar rikici tsakanin al'ummomin kasa da kasa, har ma ya illata matukar kokarin da suka yi wajen dakile annobar. Shi ya sa ya zama dole kafofin watsa labaran Sin da Afirka su dauki nauyin kaucewa yada labaran bogi, da gabatar da sahihan labarai dangane da yadda kasashen suka hada gwiwa wajen ganin bayan cutar. Na uku wato na karshe shi ne, ya kamata a nuna himma da kwazo wajen kare lafiyar 'yan jaridu, inda Mista Tian Yuhong ya yi kira da a inganta mu'amala tsakanin kungiyoyin 'yan jaridun Sin da Afirka, musamman kiyaye tsaronsu da ba su kayan rigakafi lokacin da suke bayar da rahotanni dangane da ayyukan yaki da cutar COVID-19.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar 'yan jaridun tarayyar Najeriya wanda ya halarci taron, Mista Ikechukwu Christopher Isiguzoro shi ma ya gabatar da jawabi, inda ya ce, kamar sauran wasu sana'o'i, bullar cutar COVID-19 ta haifar da babbar barazana ga sana'ar watsa labarai wadda ba'a taba ganin irinta ba a tarihi. Ya ce, daina watsa labaran karya yana da matukar muhimmanci ga ayyukan dakile cutar a duk duniya, saboda labaran bogi tamkar cutar ce da kanta, wadanda ke da hadarin gaske. Mista Ikechukwu ya kuma yi kira ga manema labarai, da su yi taka-tsantsan a lokacin da suke bada rahotanni dangane da cutar COVID-19, wato ya kamata su yi bincike a tsanake kafin su ruwaito rahotanni. Ya kuma yi kira ga gwamnatocin kasashe daban-daban su tabbatar da 'yancin bada labarai da samun bayanai, saboda wannan shi ne muhimmin sharadin aikin jarida. A karshe, Ikechukwu ya yi kira a kara bunkasa kungiyar hadin-gwiwar 'yan jaridu da aka kafa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", domin bada babbar gudummawa ga ci gaban daukacin bil'adama na duniya.
Shi kuma a jawabinsa, Al-Sadig Ibrahim Ahmed Ibrahim, shugaban kungiyar hadin-gwiwar 'yan jaridun kasashen Afirka, kana shugaban kungiyar 'yan jaridun kasar Sudan, cewa ya yi, akwai kyakkyawar alaka tsakanin kungiyar 'yan jaridun kasar Sin da kungiyoyin 'yan jaridun kasashen Afirka daban-daban. Har ma a cewarsa, ya taba kai ziyara kasashen Afirka da dama, kuma duk inda ya je, ya ga wasu alamun kasar Sin, wadanda suka shaida dadadden zumunci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Kamar a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, kasar Sin ta taimaka wajen gina babban hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka. A birnin Malabon kasar Equatorial Guinea, kasar Sin ta taimaka wajen gina cibiyar taro ta kasa da kasa. A sauran wasu manyan biranen nahiyar Afirka ma, ana iya ganin gine-gine da gadoji da layukan dogo da filayen gona da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa, wadanda suka amfani ci gaban nahiyar kwarai da gaske.
Sadig Ibrahim ya kara da cewa, ayyukan kandagarkin annobar COVID-19 na kasar Sin abubuwan koyi ne ga duk duniya, kuma babban sirrin kasar shi ne, jama'ar kasar sun zama tsintsiya madaurinki daya a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar. Har ma abun burgewa shi ne, kasar Sin ta bayyanawa kasashe da dama fasahohinta na yakar cutar da ba su taimakon kayayyakin aikin jinya da dama, musamman kasashen Afirka. A cewarsa, a wajen taron koli na musamman na hadin-gwiwar Sin da Afirka wajen dakile annobar COVID-19 wanda aka yi a ranar 17 ga watan Yunin bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, kasarsa ta samar da agajin kayan aikin jinya da tura rukunonin kwararrun likitoci zuwa kasashen Afirka sama da 50 da kungiyar tarayyar Afirka. Har ma kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasashen Afirka, wajen fadada hadin-gwiwa a fannonin da suka shafi raya birane bisa fasahohin zamani, da amfani da makamashi mai tsafta, da fasahar sadarwar 5G da sauransu. Bugu da kari, jami'an kula da ayyukan jarida na kasashen Kenya da Tanzaniya su ma sun gabatar da muhimman jawabai a wajen taron, inda babban sakataren kungiyar hadin-gwiwar 'yan jaridun kasar Kenya, Mista Erick Oduor ya ce, akwai bukatar kara hada kai tsakanin kasa da kasa domin yakar cutar COVID-19. Kuma ya kamata a tattauna kan yadda za'a farfado da aikin jarida da sauran wasu ayyukan yau da kullum idan aka kawo karshen yaduwar cutar. Ya kuma yi kira a inganta hadin-gwiwa tsakanin kungiyoyin 'yan jaridun kasashen Afirka da kungiyar 'yan jaridun kasar Sin, domin tinkarar kalubale kafada da kafada. A nasa bangaren kuma, babban sakataren majalisar kafofin watsa labaran kasar Tanzaniya, Mista Kajubi Mukajanga ya bayyana cewa, tun bayan bullar cutar COVID-19 a kasar, majalisar ta tsara ka'idojin bada rahotanni game da cutar ga kafofin watsa labarai daban-daban a kasar. Amma yaduwar annobar ta haifar da babban tsaiko ga ayyukan jarida a Tanzaniya, kuma 'yan jarida suna fuskantar babban hadarin kamuwa da cutar. Kuma wasu 'yan jaridun kasar ba sa iya tantance labaran da suka samu daga bangarori daban-daban, wato ba su san wanene na gaskiya wanene na jabu ba. Don haka yana fatan irin wannan taro zai tattauna kan yadda 'yan jaridun kasar Sin da na kasashen Afirka za su yi, domin kaucewa yarda da labaran jabu da ake yadawa, wadanda suka rura wutar rikicin kabilanci. Ya kara da cewa, yunkurin dora laifin yaduwar cutar kan wata kasa ko wasu gungun mutane, ba daidai ba ne. Ban da masu aikin jarida daga kasashen Afirka, manema labarai na kasar Sin daga kafofin yada labarai daban-daban su ma sun tofa albarkacin bakinsu game da yadda suka ruwaito rahotanni dangane da ayyukan yaki da cutar COVID-19.
Xu Zeyu, dan jarida ne daga kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin. A jawabin da ya gabatar, ya bayyana yadda ya bada rahotanni a birnin Wuhan tun farkon bullar cutar COVID-19, wato inda cutar ta fi kamari a kasar Sin. A cewarsa, tun farkon killace birnin Wuhan, akwai wasu kafofin watsa labaran yammacin duniya da suka ce, wai an keta hakkin dan Adam kuma babu isasshen abinci a Wuhan. Amma abun da ya gani da idonsa ya sabawa hakan. Ya ce ya je kasuwanni da dama a Wuhan, inda ya ga gwamnatin wurin ta yi kokarin samar da isasshen abinci da sauran wasu kayayyakin zaman yau da kullum. A asibitocin birnin Wuhan ma, ya ganewa idanunsa yadda likitoci da nas-nas suka nuna himma da kwazo wajen kulawa da wadanda suka kamu da cutar, wadanda suka burge shi kwarai da gaske.
Xu Zeyu ya kara da cewa, annobar COVID-19 na ci gaba da bazuwa a duk fadin duniya, abun da ya yi ajalin mutane masu tarin yawa, amma kasa da kasa suna kara hada kansu domin tinkarar matsalar. A cewar Xu, duk wani labarin da ya jirkita gaskiya zai lalata amincewar juna tsakanin kasa da kasa, al'amarin da ya fi cutar ita kanta haifar da illa. Shi ya sa kafofin watsa labarai suke da nauyin watsa labarai masu inganci da gaskiya, kuma a cewarsa, karfafa hadin-kai domin dakile yaduwar annobar kafada da kafada, ita ce mafita ga tinkarar annobar.
He Weiwei, 'yar jarida ce wadda ke aiki a sashen Turancin Ingilishi na babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice. He Weiwei, ta taba zuwa aiki kasashen Najeriya da Rwanda da Kenya da Tanzaniya. Ta ce, a shekarar da muke ciki, ta je kasashen Aljeriya da Sudan domin bada rahotanni kan yadda rukunonin kwararrun likitocin kasar Sin suka gudanar da ayyukansu. Ta yi amfani da wasu kalmomin Turanci guda biyar domin bayyana ayyukanta a nahiyar Afirka, wadanda suka hada da, Garment, Gesture, Goat, Guest da Goal. Garment na nufin tufafi. He Weiwei ta ce, kwararrun likitocin da gwamnatin kasar Sin ta tura zuwa kasashe daban-daban suna da riga iri daya, ita ma tana da guda daya, wanda shi ne abun alfahari gare ta. Gesture na nufin alamar hannu. He Weiwei ta ce, a wani asibitin dake kasar Aljeriya, ta gamu da wata tsohuwa wadda ta harbu da cutar COVID-19. Da ta ga likitocin kasar Sin, ta nuna musu wata alamar hannu wadda ke nufin "aboki". A cewar wannan tsohuwa, Sin da Aljeriya aminan juna ne na kwarai, kuma Aljeriya ta godewa kasar Sin bisa taimakonta.
Sa'annan kalmar goat na nufin akuya. He Weiwei ta ce, aiki tukuru da kwararrun likitocin kasar Sin suka yi ya samu babban yabo daga gwamnati gami da jama'ar kasashen Aljeriya da Sudan. Kuma akuya ita ce wata kyauta da hukumar wata jiha a Sudan ta baiwa likitocin kasar Sin domin yi musu godiya. A karshe, kalmar guest na nufin bako. He Weiwei ta ce tana jin harshen Turanci da Larabci, shi ya sa a lokacin da take aikin jarida a Aljeriya, gidan talabijin na Ennahar ya gayyace ta shiga wani shirin TV cikin yaren Larabci, domin ta bayyana yadda kwararrun likitocin kasar Sin suka gudanar da aikin yaki da cutar COVID-19 a kasar.
He Weiwei ta bayyana cewa, a matsayinta na 'yar jaridar kasar Sin wadda ta je nahiyar Afirka domin ruwaito rahotanni game da yadda aka gudanar da ayyukan yaki da cutar COVID-19, ta kara fahimtar muhimmancin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya.(Murtala Zhang)