logo

HAUSA

An Yiwa Gine-Ginen Gargajiya Gyaran Fuska Ba Tare Da Lalata Al'Adu Ba Don Kara Ingancin Zaman Rayuwar Jama'A

2020-07-20 14:55:35 cri

An Yiwa Gine-Ginen Gargajiya Gyaran Fuska Ba Tare Da Lalata Al'Adu Ba Don Kara Ingancin Zaman Rayuwar Jama'A

Shekarar 2020 shekara ce mai muhimmanci dangane da kawar da talauci a duk fadin kasar Sin . Yankunan dake fama da talauci a nan kasar Sin na canja matuka karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, matakin da ya sa al'ummar Sinawa na hadin kansu don yin zaman rayuwa cikin wadata. Shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa, lokacin da ake kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a, bai kamata an yi asara da al'adun gargajiya ba, wato an yiwa wasu gine-ginen gargajiya gyaran fuska ba tare da lalata al'adu ba. Yauzu, ana kokarin kyautata wasu titunan gargajiya dake birnin Guangzhou.

Kwanakin baya-bayan nan, an yiwa titin gargajiya da aka gada daga kaka kakkani na farko na birnin Guangzhou kwaskwarima, wanda shi ne muhimmin mataki daga cikin titunan Yongqingfang na yankin Xiguan da ake yiwa musu gyara fuska a mataki na biyu, za a kammala wannan aiki cikin gajeren lokaci. Mazaunan wuri ta ce:

"Muna zama a wannan wuri tun lokacin da muka karami, har zuwa yanzu shekaru 60 ne suka gabata, muna farin ciki matuka domin ganin irin wadannan canje-canje."

Titunan Yongqingfang suna kudu maso yammacin birnin Guangzhou, shi yanki mafi wadata ne a lokacin da. Amma suna kasa samun gyarawa sabada tsakiyar birni ya sauya zuwa gabas. Yiwa wannan wuri gyaran fuska ba ma kawia aikin zamanitar da birni ba, har ma mataki ne dake kyautata zaman rayuwar wurin. Shekarar 2016, an yanke shawarar yiwa wadannan tituna gyaran fuska a mataki na farko ba tare da lalata wasu gine-gine na gargajiya ba. Mai nazari Jiang Wanghui ya ce:

"Ka duba, ba a cire wadannan tubali na gargajiya ba, mun yi musu jikin karfe don su kara inganta. Ta wannan hanya mun iya kiyaye halayen gine-ginen gargajiya."

Ran 24 ga watan Oktomba na shekarar 2018, shugaba Xi Jinping ya taba ziyaraci wannan wuri, inda ya nanata cewa, ya kamata an mai da hankali matuka kan kiyaye al'adu yayin da ake kokarin kyautata birane, kada a gudanar da wannan aiki cikin sauri. Dole ne an mai da hankali kan kyautata halin zaman rayuwar jama'a da yiwa wadannan wurare gyaren fuska ba tare da lalata gine-ginen gargajiya ba.

Bisa bukatun shugaba Xi, an yiwa wadannan wurare gyaran fuska, an kawar da koma baya kuma an kiyaye al'adu. Lokacin da ake yiwa wani gini gyaran fuska, an kiyaye halayen tagogi na ice da gilashi ta hanyar shafawa musu fenti kawai da kuma, kiyaye kayayyakin sassaka masu launuka ta hanyar sake yi musu launuka sannu a hankali. Jiang Wanghui ya ce:

"Muna gyara wadannan gine-gine na gargajiya sannu a hankali kamar aikin surfani da zummar kyautata zaman rayuwar jama'a a wurin, matakin da zai taimaka wajen dakatar da koman baya tiruna na gargajiya da samar musu kuzari bisa zamani."

An ce, titunan Yongqingfang, wuri ne da masu fasahar wasan kwaikwayo iri na lardin Guangdong wato Yueju suka taru a lokacin da, saboda haka ana da al'adun Yueju matuka a wurin. An gina wani dakin adana kayayyakin gargajiya na Yueju bisa salon gargajiya don biyan bukatun mazaunan wuri. Mutane da dama suna zo wannan wuri don shakata da wasan kwaikwayo na Yueju a ko wace rana.

Dadin dadawa, titunan da aka yiwa musu gyaran fuska a mataki na farko sun jawo hankali 'yan kasuwa har 60 a fannonin aikin kirkire-kirkire ta fuskar al'adu da gidajen kwana da dakunan cin aibnci da kamfanonin al'adu da dai sauransu, hakan ya sa wannan tituna sun zama mahada al'adu a bangarori daban-daban. Mai fasahar samar da kayayyakin tagula a yankin Xiguan Wu Daming ya ce:

"Gwamnatin ta kyautata muhalli da kuma wurare, abin da ya baiwa mana kwarin gwiwa matuka, abin dake gabanmu za mu yi shi ne gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata."

An ce, wannan aiki na mataki na farko ya kyautata tsoffin unguwo'i 380, inda a cikin mataki na biyu da ake aiwatar, iyalai dubu 490 masu mutane miliyan 1.57 za su cin gajiya. (Amina Xu)