Muhimmancin dokar tsaron yankin Hong Kong na kasar Sin
2020-07-16 09:19:02 CRI
A kwanakin baya ne zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin ya jefa kuri'ar amincewa da dokar tsaron kasa da aka samar, domin tabbatar da tsaro a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Dokar ta samu amincewar majalisar ce, yayin zama na 20 na zaunannen kwamitin kolin JKS ta 13 ya da gudana ranar Laraba 30 ga watan Yunin shekarar 2020.
Kaza lika zaunannen kwamitin kolin ya amince da sanya dokar ciki sashe na III na Babbar Dokar da ake amfani da ita a yau da kullum a yankin na Hong Kong.
Sai dai a yayin da wasu kasashe da ma wadanda suka san ya kamata ke maraba da kafa wannan doka a yankin musamman na Hong Kong, a hannu guda kuma wasu 'yan siyasar Amurka da 'yankorensu dake neman fakewa da 'yancin demokiradiya don kawo baraka a kasar Sin, ke adawa da dokar. A ganinsu, idan har gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kara inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin Hong Kong, ba za su samu damar yin shisshigi a harkokin yankin ba, sannan yunkurinsu na kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da yankin na Hong Kong ba zai yi nasara ba.
Sanin kowa ne cewa, kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya. Kuma tun bayan da yankin Hong Kong ya dawo hannun kasar Sin, bisa ka'ida ta 23 cikin babbar dokar Hong Kong, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta damkawa yankin izinin kafa dokarta ta fannin kiyaye tsaron kasa
Jagororin yankin na Hong Kong sun sha nanata cewa, masu bin doka za su yi maraba da dokar tsaron da aka kafa, kuma matakin zai kara janyo masu sha'awar zuba da kara dawo da martabar yankin a idon duniya, da kara inganta aiwatar da tsarin kasa daya, tsarin mulkin biyu a yankin. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)