logo

HAUSA

Wasu masu tallafawa 'yan wasan kungiyoyin kwallon kafar Sin sun samu dawowa kasar

2020-07-16 14:40:07 CRI

Tun bayan fara aiwatar da matakan dakile bullar cutar COVID-19 cikin kasar Sin, ta hanyar matafiya dake shigowa kasar daga ketare, wasu jami'ai masu tallafawa harkokin wasanni a kasar ta Sin sun samu damar dawowa kasar, inda a baya bayan nan jami'in horas da kwallon kafa a kungiyar guangzhou Evergrande poly inho, da mai horaswa a kungiyar Dalian benitez, da wasu masu tallafawa 'yan wasa su 3, sun samu zarafin shigowa kasar ta Sin ta jirgin shata. Majiyar mu ta bayyana cewa, nan da 'yan kwanaki masu zuwa, akwai karin masu tallafawa harkar wasanni da ake sa ran za su shigo kasar, ciki hadda wadanda ke aiki da kungiyar Shanghai shenhua, Mr. moreno da na Jiangsu suning. Domin dakile yiwuwar sake shigowar cutar ta COVID-19 daga ketare, Sin ta aiwatar da matakan dakatar da ba da VISA, matakin da ya hana da dama daga jami'ai masu aiki a tsarin buga gasannin kwallon kafa na ajin CSL shigowa kasar daga ketare. Bayan fara aiwatar da manufar, sau biyu hukumar CFA ta gabatar da bukatar neman VISA ta musamman, domin masu koyarwa na wasu kungiyoyin kwallon kafar kasar, amma "hakar su ba ta cimma ruwa" ba. Don haka, ana iya cewa, dawowar kadan daga masu tallafawa harkar kwallon kafar kasar bakin aikin su, na zama wani muhimmin batu dake jan hankali. A ranar 28 ga watan Maris, Sin ta fara aiwatar da matakan hana shigowar baki na dan wani lokaci, wanda ya shafi masu VISA, da masu takardun zama. Amma wannan mataki bai shafi jami'an diflomasiyya, da na gwamnati, da masu ziyarar aiki da masu VISA nau'in C ba. Kaza lika, 'yan kasashen waje dake zuwa kasar domin gudanar da harkokin tattalin arziki, da cinikayya, da binciken kimiyya da fasaha, ko don gudanar da ayyukan gaggawa na jin kai, suna iya neman VISA daga ofisoshin jakadancin Sin dake kasashen su. A wancan lokaci, yawan irin wadannan jami'ai da ba su samu dawowa kasar aiki ba, sun kai mutum 34, suna kuma aiki ne a tsarin gasar CSL da kungiyoyi 16 ke bugawa, da ma masu horasa da kungiyoyin Beijing Guoan, da Jiangsu Suning, da Tianjin Teda da Qingdao Huanghai, wadanda dole su dakata a kasashen su. A wannan lokaci, hukumar CFA ta Sin, ta tura jadawali biyu na sunayen irin wadannan ma'aikata na waje, ga hukumomin da abun ya shafa, domin nemawa jami'an damar shigowa Sin domin ci gaba da gudanar da ayyukan su, to amma wannan dama ba ta samu ba, kamar dai yadda kafafen labarai na harkokin wasanni suka bayyana. A daya bangaren ma, hukumar kwallon kafar kasar ta tsara bude buga wasanni na kulaflikan ajin kwararrun kasar, tare da jami'an waje, da masu horas da 'yan wasa, amma sakamakon rashin samun wannan dama, kungiyoyin kwallon sun soke bude wasannin da aka tsara, tun daga ranar 5 ga watan nan. Ko da a baya bayan nan ma, hukumar CSL ta daga matsayin kungiyar kwallon kafa ta "Qingdao yellow sea", kana kungiyar ta sanar da daukar koci dan asalin kasar Sifaniya. To sai dai kuma sabon kocin ya bayyana cewa, ba zai iya tallafawa horon 'yan wasa na yau da kullum ba, kasancewar mahaifiyar sa na fama da rashin lafiya mai tsanani, wanda hakan ya tilasa masa neman izinin "Qingdao yellow sea" samun damar ci gaba da kasancewa a gida. A ranar 13 ga watan Yuni, kungiyar "Dalian People's Club" ta shige gaban sauran kulaflika masu buga babbar gasar kwallon kafa a Sin, inda kungiyar ta samawa kociyan ta damar dawowa cikin Sin bisa doka. Kocin Dalian Rafa Benitez, da masu taimakawa kungiyar 'yan kasashen waje su uku Longdong, da Larsen, da Danielsen, sun isa birnin Dalian ta jirgin shata daga kasar Sweden. An ce bayan shigowar jami'an, an bukaci su yi gwajin cutar COVID-19, kana za a kebe su har tsawon kwanaki 14. Bisa tsarin dokar shigowar baki daga waje, Benitez da sauran jami'an 4, sun nemi VISA ne karkashin Wanda Sports, wanda kamfani ne mai zuba jari a kungiyar ta Dalian People's, wanda hakan ya dace da ka'idojin shigowar baki 'yan kasar waje cikin yankunan Sin, don gabatar da harkokin tattalin arziki, da cinikayya, da binciken kimiya a irin wannan yanayi. Paulinho ya shigo kasar Sin don ci gaba da bugawa Guangzhou Evergrande wasa Tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafar guangzhou Evergrande, Paulinho, ya shigo kasar Sin da sanyin safiyar ranar 16 ga watan Yuni, inda aka yi masa gwajin cutar COVID-19, tare da kebe shi tsawon kwanaki 14. Wata majiya ta bayyana cewa, kungiyar Evergrande ta Guangzhou, ta shafe wata guda kafin cike sharuddan sake nemawa 'yan wasan na ta paulinho da talisca VISA shigowa kasar, bayan da suka makale a Brazil. Da farko sun fara ne da neman izini daga ofishin ma'aikatar wajen Sin dake lardin Guangdong, sannan suka mika bukatar su ga sashen lura da birni don neman izinin amincewa da takardun su a mataki na lardi. Bayan samun amincewar ofishin, sai Paulinho da Talisca suka mika takardun neman VISA ta aiki a ofishin jakadancin Sin dake Brazil. Daga karshe, sassan hukumomin da batun ya shafa suka amince cewa Paulinho da Taliska sun cika sharuddan neman VISAr shigowa Sin. To sai dai kuma, Taliska bai samu shigowa Sin tare da Paulinho a jirgin shata ba, sakamakon tsanantar cutar COVID-19 a jihar da yake da zama. Wasu majiyoyi sun ce kungiyar ta lardin Dalian, ta kashe kudi har dala miliyan 3.57 wajen hayar jirage domin sufurin jami'an ta. Ko da yake ba wata majiya daga kungiyar da ta tabbatar da hakan. Bayan jami'ai 4 'yan kasashen waje dake taimakawa Dalian, akwai kuma Poly na Guangzhou Evergrande, cikin wadanda suka dawo Sin. A karo na gaba kuma, ana sa ran zuwan karin irin wadannan jami'ai cikin kasar ta Sin. Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa, kyaftin din kungiyar Shanghai Shenhua Moreno, ya baro kasar Colombia, inda ya yada zango a birnin Los Angeles na Amurka, a kan hanyar sa ta isowa Shanghai. A hannu guda kuma ana hasashen cewa, mai yiwuwa dan wasan Shenhua mai suna Mbia, zai dan jira kafin kammala shirin sa na dawowa wasa a kungiyar. Majiyar ta kuma shaidawa kafar "Red Star news" cewa, kungiyar Shenhua na matukar biyayya ga ka'idojin kasa game da yadda Moreno zai nemi izinin shigowa Sin. Inda aka bayyana cewa, tuni wasu kafofin labarai na birnin Shanghai, suka fara kira ga magoya bayan 'yan wasa, da su kauracewa zuwa taro Moreno a filin jirgi, inda ake sa ran daga isowar sa zai wuce wurin killacewa. Shi ma kulaf din Jiangsu Suning zai aike da jirgin shata zuwa kasar Italiya da Romania, don dauko jami'an kungiyar Santini, Miranda da Eder, da kocin kungiyar Olaroyu, da mataimakin sa don dawowa da su Sin. Daga nasarorin da aka samu a baya na dawowar jami'ai, ana bin tsari ta hanyar cike ka'idojin neman VISA na musamman, baya ga hayar jirage na musamman domin wannan aiki, wanda hakan na faruwa ne kawai ga kungiyoyi masu kudaden shiga da yawa. Wata kafar labarai ta Italiya, ta ce, kungiyar Dalian People's Club ya tura jirage domin dauko jami'an dake tallafawa kungiyar, inda aka yi hayar jiragen da suka lashe kudi har euro 450,000, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 3.57. To sai dai kuma kafar "Red Star news" ta ce ba bu tabbas game da yawan kudaden da aka ce an kashe. Sai dai a zahiri take cewa, tafiya tsakanin Sin da Brazil wadda Paulinho ya yi tana da tsayi sosai, musamman ma tsakanin Brazil da Guangzhou, da yada zango a London, tafiya ce da za ta bukaci kasha kudade masu tarin yawa. Bayan 'yan wasan da suka samu komowa Sin daga ketare, a yanzu kuma akwai karin jami'ai da 'yan wasa na kulaflika kamar Henan Jianye, da Tianjin Teda, da Chongqing Contemporary da suka fara shirin dawo da masu horaswar su daga ketare, suna masu fatan jami'an na su, za su samu VISA da suke nema. Sai dai kuma tsarin neman VISAr ya danganta daga kungiya zuwa kungiya, da ma tasirin masu zuba jari.

Bugu da kari, akwai wasu daga irin wadannan jami'an, da mai yiwuwa su samu VISAr dawowa Sin, amma saboda yanayin kulle a kasashen su, ko biranen da suke da zama, ba za su samu damar dawowa a kan lokaci ba. Masharhanta na ganin cewa, idan har wadannan jami'ai suka samu zarafin dawowa kasar Sin, suka kuma koma bakin aiki yadda suka saba kafin fara gasar CSL ta bana, hakan zai taimaka matuka wajen samar da daidaito, da armashi ga sabuwar kakar wasa ta bana.