logo

HAUSA

Sabuwar rayuwar al'ummar gundumar Xide

2020-07-11 17:53:58 CRI






Bana shekara ce da ke da muhimmiyar ma'ana ga al'ummar kasar Sin, wato shekarar mahukuntan kasar Sin suka tsara don kammala aikin fitar da dukkanin al'ummar kasar da ke fama da talauci a sassan karkarar kasar da ma dukkanin gundumomin kasar da ke fama da matsalar daga kangin da suke ciki.

Gundumar Xide ta yankin Liangshan mai cin gashin kansa na kabilar Yi da ke lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin tana daya daga cikin gundumomi 7 da har yanzu suke fama da talauci a lardin. A biyo mu cikin shirin, don mu leka yanayin da gundumar ke ciki.(Lubabatu)