logo

HAUSA

Rawar majalisar dinkin duniya na tabbatar da zaman lafiya a duniya

2020-07-09 09:08:03 CRI

An dai kafa Majalisar dinkin duniya ce bayan yakin duniya na biyu da nufin hana faruwar yake-yake a nan gaba. A ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 1945, gwamnatoci kimanin hamsin (50) sun gana a San Fransisco na kasar Amurka, don tattauna yadda za a tsara daftarin dokokin da za su kai ga kafa majalisar, wadda aka amince da shi a ranar 25 ga watan Yunin shekarar 1945, kana ya fara aiki a ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 1945, lokacin da MDD ta fara aiki.

Rawar majalisar dinkin duniya na tabbatar da zaman lafiya a duniya

Manufar kafa MDD ita ce tabbatar da zaman lafiya a duniya, biyo bayan yakin cacar baka da ya kaure tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet da kawayensu.

Rawar majalisar dinkin duniya na tabbatar da zaman lafiya a duniya

MDD tana da manyan rassa guda shida (6) da suka hada da babban zauren majalisar, da kwamitin sulhu, da hukumar kula da harkokin tattalin arziki da jin dadin jama'a da kotun kasa da kasa, da sakatariyar majalisar da sauransu. Haka kuma majalisar na da hukumomi kamar bankin duniya da hukumar lafiya ta duniya (WHO) da shirin samar da abinci na duniya WFP, da UNESCO da UNICEF da makamantansu, duk da nufin inganta rayuwar al'ummar duniya. Haka kuma MDD tana da mambobin kasashe na dindindin guda biyar da sauran kasashe da ba na din-din-din ba da ake zaba daga lokaci zuwa lokaci na tsawon wani karamin wa'adi, ta yadda za a kara janyo kasashen mambobin majalisar a jika, don sanin bukatunsu da ma hanyar warware dukkan matsaloli da suke fuskanta. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)