logo

HAUSA

Lawal Saleh: zartas da dokar kare tsaron kasa na yankin Hong Kong na da babbar ma'ana

2020-07-07 14:44:02 CRI

Lawal Saleh: zartas da dokar kare tsaron kasa na yankin Hong Kong na da babbar ma'ana

Masu iya magana na cewa, karya ta kare, wai bori ya kar boka. Yanzu dai an kawo karshen duk wani guna-guni da gutsiri tsoma game da dokar tsaron kasa na yankin musamman na Hong Kong, bayan da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin ya jefa kuri'ar amincewa da dokar tsaron kasa da aka samar, domin tabbatar da tsaro a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Lawal Saleh: zartas da dokar kare tsaron kasa na yankin Hong Kong na da babbar ma'ana

Sai dai a yayin da wasu kasashe da ma wadanda suka san ya kamata ke maraba da kafa wannan doka a yankin musamman na Hong Kong, a hannu guda kuma wasu 'yan siyasar Amurka da 'yan barandansu dake neman fakewa da guzuma domin su harbi karsana ke adawa da dokar.

Lawal Saleh, wani masanin harkokin kasashen waje ne dake birnin Abuja na tarayyar Najeriya. A zantawarsa da Murtala Zhang, Lawal Saleh ya ce, zartas da dokar kare tsaron kasa na yankin Hong Kong na da matukar muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da bunkasuwa a Hong Kong da ma fadin kasar Sin baki daya. A cewarsa, sanin kowa ne, Hong Kong wani yanki ne na kasar Sin, wanda ba za'a iya balle shi ba, kuma bai kamata wasu kasashe su yi shisshigi ko kuma nuna yatsa ga harkokin cikin gidan kasar Sin ba.(Murtala Zhang)