logo

HAUSA

Zhou Fang: Basiniya ta farko da ta yi kokarin daukar bidiyo don nuna albarkatu masu ban sha'awa karkashin ruwa a fadin kasar Sin

2020-07-07 13:05:32 CRI

A watan Satumban 2019, aka watsa wani shirin Documentary mai suna "Underwater China," shirin, wanda aka shirya a cikin ruwa, ya nuna wasu albarkatu masu ban sha'awa da yanayi da gine-ginen karkashin ruwa a fadin kasar Sin. Babbar mai bada umarnin shirin wata Basiniya ce mai suna Zhou Fang, wadda ta fito ne daga lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Cikin shekaru 3 da suka gabata, Zhou ta jagoranci tawagarta wajen daukar daddadun abubuwan dake karkashin ruwa a biranen kasar Sin 24.

Zhou Fang, 'yar asalin Changsha, babban birnin lardin Hunan, na son wasannin motsa jiki sosai. A shekarar 2012, Zhou ta fara sha'awar linkaya, bayan ta ga wasu hotuna da wata kawarta ta dauka a karkashin ruwa. Daga nan ta fara koyon linkaya, kuma a karshe ta ci nasarar gwajin zama kwararriyar 'yar linkaya. A duk lokacin da ta shiga kasan teku, ta kan ji ta kamar "aljanar ruwa" wadda ke cikin farin ciki, da kwanciyar hankali da nutsuwa a lokacin da take shawagi cikin kifaye a tsakanin hallitun karkashin ruwa.

Zhou Fang: Basiniya ta farko da ta yi kokarin daukar bidiyo don nuna albarkatu masu ban sha'awa karkashin ruwa a fadin kasar Sin

Zhou Fang ta kwashe kusan shekara 1 tana zagaye duniya, tana neman wuraren da suka dace da bukatarta na linkaya da daukar hotuna a karkashin ruwa. A shekarar 2012, ta kammala shirin documentary na farko a karkashin ruwa mai suna "Looking for Whale Shark". Manufar daukar shirin ita ce, wayar da kan jama'a game da bukatar kare Mafi babban kifi wato Shark, da halittun ruwa dake fuskantar barazanar bacewa da kuma muhallin teku. Zhou Fang ta yi waiwaya da cewa,

"Shekaru 3 da suka gabata, na hadu da wani koci dan Rasha, wanda ya tambaye ni ko na san tafkin Fuxian na lardin Yunnan, kuma ko na taba tunanin gano albarkatu da yanayin karkashin ruwan kasar Sin? Gaskiya dai, kalamansa ya sa na ji kunya sosai. A matsayina na wata Basiniya mai daukar bidiyo na karkashin ruwa, har yanzu ban san abubuwan da ke karkashin ruwa a kasa mahaifata ba". A wancan lokacin, Zhou Fang tana daya daga cikin ayarin dake shirya wani shiri mai babuka 25 mai suna "Dive the World". Daga nan sai ta tsai da kudurin fara shirin daukar shirin "Underwater China" na wata duniya da a baya ba a san da ita ba. The Blue Planet, wani shirin da kamfanin watsa labarai na Birtaniya na BBC ya shirya, ya zama abun misali ga shirye-shiryen dake dauke da muhallin halittun karkashin ruwa. Masu kallo da dama ne duniyar karkashin ruwa ta burge su bayan sun kalli shirin Blue Planet. Da Zhou ta fara daukar shirin Underwater China a shekarar 2017, ta yi fatan shirin zai gano tare da gabatar da abubuwan ban sha'awa dake karkashin ruwa a kasar Sin.

Zhou Fang: Basiniya ta farko da ta yi kokarin daukar bidiyo don nuna albarkatu masu ban sha'awa karkashin ruwa a fadin kasar Sin

Tawagar daukar shirin Underwater China na kunshe da mambobi 6, mata 2, maza 4. Kowanne mamba na da gogewar daukar hotuna a karkashin ruwa na a kalla shekaru 10. An fara daukar shirin ne a lokacin zafi na shekarar 2017.

Bangare mafi tattare da kalubale shi ne linkaya cikin kogo. Masu linkaya ba su taba shiga galibin kogunan ba. Akwai bukatar tawagar su samu hanyoyi mafi aminci da kansu. Zhou ta yi bayanin cewa, idan hanyar shiga kogo ta yi kadan, sai sun sauke kurtun iska dake taimaka musu numfashi, su tura cikin kogon, sai kuma su shiga ciki su dauki kurtun. Zhou ta yi kasada a lokacin daukar wani makahon jatan lande, wanda ke rayuwa cikin kogo a yankin Guangxi na kabilar Zhuang mai cin gashin kansa dake kudancin kasar Sin. Zhou tana mai cewa, "Ni da wata mun yi farin cikin ganin jatan landen. Mun bi shi cikin kogo ba tare da la'akari da cewa igiyar dake daure a jikinmu, wanda ke tabbatar da cewa za mu iya komawa wurin da babu hadari, ya fadi ba tare da mun san ta ba. Daga baya kuma, mun gano cewa, mun kasa ganin komai. Babu murya ko kadan, sai amon numfashinmu kawai. A wancan lokacin, na ji kamar zan mutu." Daga baya Zhou ta gaya wa kanta cewa, kada a tada hankali, sai dai kokarin neman mafita. A karshe dai, mun samu nasarar fita daga kogon. Duk da kasadar, 'yan tawagar sun yi farin cikin ganin bidiyon makahon jatan lande da aka dauka.

Zhou Fang: Basiniya ta farko da ta yi kokarin daukar bidiyo don nuna albarkatu masu ban sha'awa karkashin ruwa a fadin kasar Sin

Tawagar Zhou ta tafi tafkin Qiandao a lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, domin gano garuruwa biyu da ruwa ya mamaye saboda tashar samar da lantarki da aka gina a lardin. Zhou da tawagarta sun ziyarci wani mai fasahar zane da ya taba zama a garin, da nufin fahimtar yanayin garin na ainihi. "tsohon ya shafe shekaru 10 yana tattara bayanai daga mutanen da suka zauna a garuruwan. Ya zana wani hoto da ya yi kama da taswirar dake nuna tsoffin gine-ginen garin da tituna," cewar Zhou. Tawagar ta yi kofin hoton ta yadda ruwa ba zai bata ba, ta kuma tafi da shi garuruwan. Zhou ta yi mamakin ganin har yanzu wasu gine-ginen dake cikin hoton suna nan, duk da kasancewarsu a karkashin ruwa. Zhou ta kara da cewa,

"Abin da ya fi burge ni shi ne tsohuwar kofar tunawa da aka sassaka kan dabbar Long a kanta, wadda na gano a karkashin tafkin Qiandao. Lallai na yi farin ciki kwarai da gaske da yadda muke iya gano dadadden tarihin kasar Sin da ke karkashin ruwa. A wancan lokaci abin da nake ji a rai shi ne, komen wahala da muka sha ba damuwa ko kadan ba." A tafkin Fuxian dake Yunnan, tawagar ta gano wani gini mai fadin murabba'in kilomita 2.4. Ginin na kunshe da wani abu mai kama da dala dake da ban al'ajabi, wanda aka kawata da wasu zane da alamomi, wadanda kawo yanzu ba a yi bayanin ma'anarsu ba.

Zhou Fang: Basiniya ta farko da ta yi kokarin daukar bidiyo don nuna albarkatu masu ban sha'awa karkashin ruwa a fadin kasar Sin

Zhou da tawagarta, sun shafe shekaru 2 da watanni 7 suna ziyartar birane 24 tare da kammala daukar shirin "Underwater China". Shirin mai babuka 6, ya yi fice tare da samun yabo, bayan an sake shi a ranar 29 ga watan Satumban 2019. Zhou ta furta cewa,

"A ganina, akwai dimbin dukiyoyi a karkarshin ruwa a kasar Sin, amma dukiyoyin ba zinariya da lu'ulu'u ba ne. Al'adun kasar Sin su ne mafi daraja. Don haka, ina ji na a matsayin mai sa'a, saboda ban yi kasa a gwiwa ba wajen shirya shirin domin nuna al'adun Sin dake karkashin ruwa. "(Kande Gao)