logo

HAUSA

Me ya sa kasa mafi ci gaba ta kasa dakile cutar COVID-19?

2020-07-06 14:22:33 cri

Cikin 'yan kwanakin nan, yanayin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ya tsananta a wasu yankunan kasar Amurka, inda adadin masu kamuwa da cutar cikin yini daya a kasar ke ci gaba da kasance mafi yawa a duk fadin duniya. Wannan adadin ya kai 54,375 a ranar 2 ga wata, wanda ya kasance mafi yawa bisa karuwar masu kamuwa da cutar cikin yini daya.

Bisa binciken da jami'ar Johns Hopkins ta yi, ya zuwa karfe 5 na yammacin jiya Lahadi, agogon gabashin Amurka, gaba daya, akwai masu dauke da cutar COVID-19 2,874,396 a kasar Amurka, ciki har da mutane 129,870 da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Me ya sa kasa mafi ci gaba ta kasa dakile cutar COVID-19?

Wani likita dake aiki a jihar South Carolina, ya bayyana cewa, yaduwar cutar COVID-19 tamkar mahaukaciyar guguwar da karfinta ya kai matsayi na 6 ne, wadda ta zarce matsayin koli, wato matsayi na 5. Ya ce, "ba za mu iya barin wannan wuri ba, don haka ya kamata mu zama mun yi nesa da sauran mutane, mu kaucewa taruwar mutane, wadanda mai iyuwa ne za su kawo mana hadari." Haka kuma, ya yi kira ga al'ummomi da su mai da hankali kan yaduwar annobar, yana mai cewa, ya kamata kowa da kowa ya gane cewa, wannan babbar matsala ce, kuma muna cikin wani lokaci mai hadari. Ya ce yanzu, muna fuskantar wata babbar matsala ta fuskar kiwon lafiya, wadda ba mu taba gamuwa da irin ta ba cikin shekaru 40 da suka wuce.

Amma, wasu Amurkawa sun kyale kiran da masana, da jami'an gwamnati suke yi musu, suna ci gaba da yin kome da suke so. Ranar 4 ga watan Yuli ranar 'yancin kai ce ta kasar Amurka, kuma lokacin hutu ya kawo karin barazana ga aikin dalike yaduwar cutar COVID-19. Mutane da yawa sun fita yawo a yankunan rairayin bakin teku a jihar Maryland. Ban da haka kuma, jiragen sama dake tafiye-tafiya cikin kasar Amurka, suna cike da fasinjoji, inda wasu fasinjojin ma ba sa daukar matakan yin kandagarki, da dalike yaduwar cutar, kamar yadda kamfanonin jiragen sama suka bukata ba.

Me ya sa kasa mafi ci gaba ta kasa dakile cutar COVID-19?

Masana sun yi kira ga al'umma, da su rika sanya abun rufe hanci da baki idan suna waje, domin magance yaduwar cutar COVID-19, amma, yadda Amurkawa ke yi na haifar da damuwa sosai. A yayin da shugaban kasar Amurka ya kai ziyara tsaunin Rushmore dake jihar South Dakota, wanda aka fi sani da "tsaunin shugabanni", domin taya murnar ranar 'yancin kai, mutane da dama a wurin ba su sanya abin rufe hanci da baki, ko kuma yin nisa da juna ba.

Matukar karuwar masu dauke da cutar COVID-19 a kasar Amurka ya matsa wa tsarin kiwon lafiya na kasar lamba kwarai da gaske, har ma wani likita a jihar Arizona ya bayyana cewa, za su fuskanci wani babban kalubale, wato, zabar wadanda za su shiga dakin kula da marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali ko (ICU), da kuma wadanda ba za su iya shiga ba.

A hannu guda kuma, an hana shigar Amurkawa cikin wasu kasashen duniya. Tun daga ranar 1 ga wata, kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU, ta bude iyakokinta ga kasashe da dama, amma ban da kasar Amurka, sabo da yadda ta kasa dakile yaduwar cutar COVID-19 cikin gida.

Ban da haka kuma, a ranar 3 ga wata, gwamnatin kasar Burtaniya ta gabatar da jerin sunayen kasashe ko yankuna, inda babu bukatar yin zama a gida, idan za a shiga kasar Burtaniya daga wadannan kasashe da yankuna, a cikin jerin kuma, babu kasar Amurka.

Me ya sa kasa mafi ci gaba ta kasa dakile cutar COVID-19?

Haka kuma, a ranar 3 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta WHO ta yi kira ga kasashen da suke fin fama da matsalar yaduwar cutar COVID-19 cewa, ya kamata su waye kansu, domin dakile yaduwar cutar yadda ya kamata, a maimakon ci gaba da zargin wani ko wata.

Cikin taron manema labaran da aka yi a wannan rana a birnin Geneva, shugaba mai kula da ayyukan gaggawa ta hukuwar WHO Michael Ryan ya bayyana cewa, nahiyar Amurka nahiyar da ta fi fama da matsalar yaduwar annoba a nan duniya, kuma kasar Amurka ita ce kasa mafi samun yaduwar cutar COVID-19. Kasa mai da hankali kan wannan annoba da shugabannin kasar suka yi, ya haddasa yanayin da kasar take ciki a halin yanzu. Ya ce, wasu kasashe masu fama da yaduwar cutar suna son farfado da tattalin arzikinsu da sauri, amma, ba su dauki matakan yin kandagarki da dakile yaduwar cutar yadda ya kamata ba, har wasu shugabanni sun ce, cutar za ta bace da kanta a wani lokaci, shi ya sa, ana ci gaba da taruwar mutane, har wasu suna yin shakku kan matakan sanya abin rufe hanci da baki da ma zama nesa da juna, wadanda aka riga aka tabbatar da su ne matakai masu amfani wajen dakile yaduwar cutar, lamarin da ya sa, cutar na ci gaba da yaduwa da sauri a wasu wurare.

Ko gargadin da hukumar WHO ta yi wa kasar Amurka zai sa kasar ta gane halin da take ciki, da kuma daukar matakai yadda ya kamata?

Dangane da wannan batu, mataimakiyar shugaban sashen nazarin manyan tsare-tsaren kasa da kasa na cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin, Su Xiaohui ta bayyana cewa, gyarawar matakan da kasar Amurka take yi bisa bukatun da aka yi mata, ba su iya hana yaduwar cutar a kasar Amurka ba, balle ma kawar da cutar baki daya a kasar.

Ta ce, kwanan baya, kasar Amurka ta fara mai da hankali kan amfanin abin rufe hanci da baki, amma, sabo da, masu dauke da cutar sun yi yawa a kasarta, wannan mataki ba zai ba da amfani sosai ba.

Haka kuma, ta ce, karuwar sabanin dake tsakanin jam'iyyun biyu na kasar Amurka a wannan lokaci, zai samar da karin barazana ga ayyukan dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar Amurka. (Maryam)