logo

HAUSA

Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

2020-07-03 14:31:01 cri



Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

 

Rashin ci gaba a fannonin tsarin kiwon lafiya, tsarin aikin jinya, manyan ababen more rayuwa, su ne abubuwan da nahiyar Afirka ke fuskanta, yanzu ana samun yaduwar annobar COVID-19 a duniya baki daya, hakan ya sa kwararru a fannin kiwon lafiya masu yawa suke damuwa kan nahiyar.

Kwanan baya, sashen kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma na MDD ya shirya wani taro ta intanet game da shirin kasashen Afirka na amfani da fasahar bayyanai da sadarwa da kirkire-kirkire kan harkokin siyasa wajen tinkarar annobar COVID-19. 

 

Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

Taron da aka shirya ta intanet ya hallara kwararru daga wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da MDD, kungiyar EU, Afirka ta kudu, Kenya, Sin da dai sauransu, inda suka mayar da hankali kan yadda za a habaka matakan dakile annobar COVID-19, da yadda ake tabbatar da ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma a yayin da ake yakar annobar. Wani Kwararre daga kasar Sin ya more fasahohin da kasar ta samu kan tinkarar annobar ta fasahar zamani, wadanda suka jawo hankulan mahalartan taron.

Cuta ba ta san iyakar kasa. Ko kasashen Afirka za su iya cimma nasarar tinkarar kalubalen da yaduwar annobar ke kawowa ko a'a, wannan ya dogara ga ko za a iya cimma nasarar yakar annobar a daukacin duniya ko a'a.

Kamar yadda mataimakin shugaban zartaswa na kamfanin Tencent Liu Shengyi ya fada a yayin taron, "Mu da kasashen Afirka muna da makomar bai daya, muna fatan ganin za mu cimma nasarar yaki da annobar ta hanyar kimiyya da fasaha." 

 

Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

Game da haka, ministar sadarwa da fasahar zamani ta kasar Afirka ta kudu Stella Tembisa Ndabeni Abrahams ta gabatar da hakikanan matakai guda uku, da farko a yi kokarin inganta amfani da fasahar zamani don hana yaduwar annobar, na biyu, a ba da tabbaci kan gudanar da harkokin sadarwa yadda ya kamata, na uku, a karfafa gwiwar kamfanonin da abin ya shafa su kara ba da hidima ga jama'a don taka rawa wajen yaki da annobar.

A waje guda kuma, jami'an wasu kasashen da suka hada da Kenya, Ghana, Habasha da dai sauransu sun jaddada cewa, yadda za a tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki da ba da ilmi da sauran ayyuka yadda ya kamata, wannan sabon batu ne dake gaban duniya baki daya, ciki har da kasashen Afirka.

Ndabeni Abrahams ta ce, yanzu gwamnatin kasar Afirka ta kudu na kokarin inganta kamfanonin sadarwa ta yadda za su dauki alhakin dake bisa wuyansu kan al'umma, da kuma rage nauyinsu, hakan zai ba da tabbaci ga jama'ar kasar su samu hidimar intanet yadda ya kamata.

Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

A nasa bangaren, Liu Shengyi yana ganin cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta iya tinkarar annobar cikin sauri, shi ne domin cin gajiya daga shirin yin kirkire-kirkire kan yanar gizo wanda aka soma gudanarwa a shekarar 2015, sannu a hankali fasahar zamani ta riga ta kasance daya daga cikin sabbin ababen more rayuwar jama'a a cikin kasar. A cewar Liu Shengyi, sana'ar intanet ta kasar Sin ta zama ginshiki na matsakaita da kananan kamfanonin kasar wajen samun bunkasa bayan annobar.

Kasar Afirka ta kudu ita ce kasar da ta fi fama da annobar COVID-19 a nahiyar Afirka, inda aka tabbatar da cewa, wadanda ke fama da cutar a kasar sun wuce kashi daya cikin kashi uku na wadanda cutar ta kama a nahiyar.

Ndabeni Abrahams ta bayyana a yayin taron cewa, kamata ya yi mu shirya sosai kan halin da za mu fuskanta, wato dokar zaman gida. Ya kamata jama'a su shirya wannan doka. 

 

Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

Liu Shengyi ya amince da ra'ayin Ndabeni Abrahams, ya ce, a yayin da ake dakile annobar, tilas al'umma su tashi tsaye wajen shiga a dama da su a wannan aiki. Ya ba da misalin cewa, ya zuwa watan Yuni na bana, kamfanin Tencent ya taimakawa jihohi da larduna guda 21 na kasar Sin, wadanda suka hada da birane da gundumomi sama da 400 don su gudanar da ayyukan kandagarkin annobar, ya kuma fitar da sabbin manhajoji fiye da 100 don ba da hidima game da annobar. Masu amfani da manhajan Wechat na kamfanin da yawansu ya wuce miliyan 300 suna iya samun sabbin bayanai kai tsaye a kowane lokaci da suke bukata.

A nahiyar Afirka, ana amfani da hanyar kimiyya da fasaha don taimakawa al'umma suka shiga ayyukan yakar annobar.


 

Fasahar zamani na taimakawa kasashen Afirka wajen kara tinkarar annobar COVID-19

A kasar Kenya, gwamnati ta yada bayanai game da annobar COVID-19 ga jama'arta ta yanar gizonta. A kasar Habasha kuma, wasu hukumomin da abin ya shafa sun kafa dandalin samar da bayyanai na musamman, don ba da jagoranci ga jama'a. Wani jami'in hukumar ci gaba ta AU Andson Nsune ya bayyana a yayin taron cewa, hukumarsa ta mayar da kafa cibiyar yin kirkire-kirkire kan kimiyya da fasaha a matsayin muhimmin aikinta, inda fasahar sadarwa ta kasance muhimmin sashe na shirinsu bisa manyan tsare-tsare. (Bilkisu)