logo

HAUSA

Labarai game da yadda Sinawa suke kokarin kawar da talauci ta hanyoyi daban daban

2020-07-03 17:11:12 CRI

Wannan shekarar da muke ciki, wata shekara ce mai muhimmanci sosai ga Sinawa, domin gwamnatin kasar ta dau niyyar kawar da talauci baki daya daga kasar cikin wannan shekara. Hakan na nufin za a yi kokarin tabbatar da ganin masu fama da talauci dukkansu za su samu isashen kudin shiga, ta yadda za su samu damar fid da kansu daga kangin talauci.

To, sai dai kuma ko ta wadanne hanyoyi ne za a iya cimma wannan babban burin da aka sanya a gaba?

Cikin shirin yau, zan yi muku bayani bisa wasu labarai game da zaman rayuwar Sinawa, wadanda suke bin hanyoyi daban daban don neman samun kudi, gami da kyautata zaman rayuwar kansu.