logo

HAUSA

Sirrin nasarorin 'ya'yan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin

2020-07-02 16:44:09 CRI

A ranar Laraba 1 ga watan Yulin shekarar 2020 ne, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta cika shekaru 99 da kafuwa. Daga jam'iyyar da ta fara da mambobi sama da 50 kawai a farkon kafuwarta zuwa jam'iyya mafi girma a duniya yanzu, shin yaya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin take ta ci gaba duk da matsalolin da ta fuskanta? Yaya kuma take rike tagomashinta a cikin shekaru kusan 100 da suka wuce? Amsar wadannan tambayoyi ita ce bautawa jama'a.

Sirrin nasarorin 'ya'yan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin

A ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2017, babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya kai ziyara biranen Shanghai da Jiaxing na kasar tare da sabbin zaunannun mambobin hukumar siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar, inda suka ziyarci wurin da aka gudanar da taron wakilan jam'iyyar karo na farko a birnin na Shanghai da kuma wani jan jirgin ruwa da ke birnin Jiaxing da aka sanar da kafuwar jam'iyyar, don waiwayen tarihin jam'iyyar da kuma alkawuran da aka dauka lokacin shiga jam'iyyar, lamarin da ya shaida niyyar sabbin shugabannin jam'iyyar.

A kokarin da ake yi na yaki da annobar, kasar Sin ta tara ma'aikatan lafiya da suka fi kwarewa da kuma na'urorin kiwon lafiya da suka fi inganci, kana ta hada karfin kowane bangare na kasar, don kare lafiyar al'ummar kasar.

Sirrin nasarorin 'ya'yan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin

Farfadowar kasar Sin, na da alaka da ci gaban jam'iyyar kwaminis. Daga wata karamar jam'iyya a farkon kafuwarta zuwa jam'iyya mai karfi na yanzu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin mai mulkin kasar da ke da al'umma biliyan 1.4, tana ta ci gaba duk da kalubalen da ba za a rasa ba.(Saminu,Ibrahim/Sanusu Chen)