logo

HAUSA

Gina filayen wasan kankara zai kawo babban canji ga jama'ar dake karkarar birnin Beijing

2020-07-02 10:58:32 CRI

Gina filayen wasan kankara zai kawo babban canji ga jama'ar dake karkarar birnin Beijing

Bayan da kasar Sin ta yi nasarar daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunkuru ta shekarar 2022, wasannin kankara sun kara samun karbuwa a tsakanin jama'ar kasar Sin. Hukumar raya yawon shakatawa ta birnin Beijing ta bayyana cewa, yawan masu yawon shakatawa da suka ziyarci filayen wasan kankara na birnin Beijing a hutun bikin bazara na shekarar 2017 ya kai dubu 84, wanda ya karu da kashi 8.6 cikin dari bisa na shekarar 2016, ta yi imani da cewa, yawansu zai ci gaba da karuwa. Daya daga cikin ayyukan da aka yi alkawari yayin da kasar Sin take neman samun iznin daukar bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunkuru, shi ne ganin mutane miliyan 300 sun halarci wasanni a kan kankara. Bayan da birnin Beijing na kasar Sin ya yi nasarar daukar bakuncin shirya gasar ta shekarar 2022, ana ganin mutane dake kara son shiga wasannin kankara. Yawan masu yawon shakatawa da suka zabi yin wasanni a kan kankara a kasar Sin ya karu sosai, ciki har da yara da dama da suka koyi fasahohin yin wasa a kan kankara. A sakamakon damar da kasar ta samu ta daukar bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunkuru, jama'ar kasar Sin za su kara shiga wasanni a kan kankara. An shafe fiye da shekaru 10 ana wasanni a kan kankara a birnin Beijing, mutane da dama sun cewa, irin wannan wasa ba ya bukatar kashe kudi da dama, kana gwamnatin birnin ta kara Ilimantar da jama'a game da wasan, don haka mutane da dama suna son yin wannan wasa, musamman matasa. Mr Gu ya fara yin wasan a shekarar 2013, domin kamfaninsa ya shirya wasan kankara tare da sanya dukkan ma'aikatan kamfanin yin wasan tare a wani filin wasan kankara dake karkarar birnin Beijing. Ya ce, da ma ya kan kalli wasan ta kafar telebijin, lokacin da ya samu damar yin wasan, abin ya ba shi sha'awa. Ya ce, ya yi wasan ba tare da wani ya horas da shi ba, ya ce wasan yana da ban sha'awa, amma akwai wuya kadan. Game da filin da ake wasan kankara, ya ce, kankarar dake wurin tana da inganci, kana ban da wasan, akwai sauran kayayyakin yawon shakatawa a filin. Ya ce,   "A lokacin sanyi, mutane su kan yi wasan kankara mai taushi a wannan wuri, kana akwai wuraren yawon shakatawa a kewayensa, da otel-otel da wuraren cin abinci, mutane su kan ji dadin wasa da yawon shakatawa a nan. Kuma a lokacin zafi, akwai wuraren kayan lambu da 'ya'yan itatuwa a nan, su ma su iya jawo hankalin masu yawon shakatawa da su zo wurin." Ya kara da cewa, a kokarin da ake yi na ganin Beijing ya samu bakuncin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunkuru ta shekarar 2022, an kara gina filayen wasan kankara mai taushi a kewaye ko karkarar birnin. Hakan ya taimakawa mazauna wuraren samun damar kawar da talauci da kara samun kudin shiga. Ya ce, "Bayan da aka gina karin filayen wasan kankara mai taushi a kewayen birnin, jama'ar dake karkarar birnin sun samu babban canji, ta hanyar inganta sha'anin yawon shakatawa, da karin kudin shiga, da kuma kyautata zaman rayuwarsu." Mr Dong ya fara yin wasan ne tun daga shekarar 2017, a matsayinsa na dan yankin arewa maso gabashin kasar Sin, wato yankin da aka fi samun kankara, yana son ya samu damar yin wasan. Bayan da ya zo birnin Beijing, ya ga filayen wasan kankara da dama da ake da su a karkarar birnin, da wuraren yawon shakatawa dake kewayen filayen. Don haka, ya zabi wani fili don jin dadin hutunsa. Game da garin Chongli, ya ce, ba don filayen wasan kankara da aka gina a wuri ba, ba zai samu babban ci gaba a wurin kamar hakan ba. Ya ce, "Idan ba a gina filin wasan kankara a garin Chongli ba, a ganina, garin ba zai samu ci gaba sosai ba. Domin wannan wuri ba shi da wuraren yawon shakatawa a kewayensa, mazauna garin basu samu damar inganta sha'anin yawon shakatawa ba, kana kudin shiga da suke samu ba shi da yawa. Bayan da aka gina filin wasan kankara, sun samu babban canji a zaman rayuwarsu da kuma karin kudin shiga." Ya kara da cewa, bayan da Beijing ya samu iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru, karin mutane sun fara sanin wasan kankara, kana Chongli ya fara gina filayen wasan kankara a kan wanisu duwatsu da ke filinsa, kana an gina sauran kayayyakin yawon shakatawa a kewayensu don biyan bukatun masu sha'awar wasan da suka zo wurin don yin wasan da yawon shakatawa. Ya ce,

"Ban da filayen wasan kankara da aka gina a garin Chongli, an kara gina otel-otel da wuraren yawon shakatawa a kewayensu, sai dai masu sha'awar wasan za su jin dadin wasan, tare da jin dadin yawon shakatawa a wurin."(Zainab)