Hong Kong na murnar cika shekaru 23 da dawowarta kasar Sin
2020-07-02 13:55:16 cri
Ranar 1 ga watan Yulin bana, rana ce ta cika shekaru 23 da dawowar yankin Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin, inda bangarori daban-daban a yankin suka shirya bukukuwan murnar zartas da dokar kare tsaron kasa na yankin.
Jiya 1 ga wata, an fara nuna wani fim na musamman a yankin Hong Kong. Fim din mai suna "Taken Kasa", wanda aka dauka a shekara ta 1999, ya bayyana yadda aka samo taken kasar Sin, musamman yadda al'ummar kasar suka yi gwagwarmayar yaki da makiya. Kafin a fara nuna fim din, masu kallo sun tashi tsaye, inda suka rera taken kasa, domin murnar cika shekaru 23 da dawowar Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, da zartas da dokar kare tsaron kasa. A nasa bangaren, shugaban kungiyar hadin-gwiwar matasan Hong Kong ta majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin, Tam Chan Kwok ya ce, yana da yakinin cewa Hong Kong za ta samu makoma mai haske bayan da aka zartas da dokar, inda ya ce:
"Ban da murnar cika shekaru 23 da dawowar yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin, ya kamata mu yi bikin murnar amincewa da dokar kare tsaron kasar yankin, al'amarin da ya ba mu kwarin-gwiwa sosai. Ni kaina ina matukar goyon-baya gami da godewa gwamnatin kasarmu saboda muhimmanci da ma amincewar da ta nuna wa Hong Kong, kuma ina da yakinin cewa Hong Kong za ta dawo hanya madaidaiciya nan ba da jimawa ba."
A nasa bangare, memban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasar ta kasar Sin na yankin Hong Kong, kana shugaban kungiyar hadin-gwiwar bangarori daban-daban ta tsibirin Hong Kong, So Cheung Wing ya bayyana cewa, a daidai lokacin da ake bukukuwan murnar cika shekaru 23 da dawowar yankin Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin, kallon fim din mai suna "Taken Kasa" yana da ma'ana ta musamman, kuma muna alfahari sosai saboda zama 'yan kasar Sin. Ya ce:
"A matsayinmu na mazauna yankin Hong Kong, muna farin-ciki sosai a wannan rana ta cika shekaru 23 da dawowar Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin, haka kuma muna kara kishin kasarmu. A ganina, ta hanyar kallon irin wannan fim mai karfafawa gwiwa, mazauna Hong Kong za su kara alfahari da zama 'yan kasar Sin."
Stanley Ng Chau-pei, memban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na yankin Hong Kong, ya bayyana cewa, zartas da irin wannan doka zai taimaka wajen tabbatar da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong. Ng Chau-pei ya ce:
"A ganina zartas da wannan doka na da ma'ana sosai, ina kuma farin-ciki kwarai da gaske, musamman lokacin da aka zartas da ita. A ganina ma'anarta ita ce, a da babu irin wannan dokar ta kare kasa, amma yanzu akwai dokar da ta tabbatar da tsaronmu gami da zaman lafiya a yankin Hong Kong."
Tam Kam Kau, shi ne zaunannen memban majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin shirya bukukuwa na bangarori daban-daban a Hong Kong. Ya jaddada cewa, tsara dokar kare tsaron kasa na Hong Kong, ya zama dole ga kowace kasa gami da al'ummarta baki daya. Kuma yana fatan fim din "Taken Kasa" zai kara fadakar da al'ummar Hong Kong kan tarihin kasa gami da yadda take bunkasa a halin yanzu. Tam Kam Kau ya bayyana cewa:
"Tsara dokar, wata dabara ce da aka bullo da ita, da nufin fadakar da al'umma kan muhimmancin mutunta kasa. Ya kamata mu zama tsintsiya madaurinki daya, domin ba da gudummawarmu ga gina kasa, da tabbatar da bunkasuwa da zaman lafiya a Hong Kong. Girmama kasarmu gami da nuna kishin kasa, abu ne da ya kamata kowa da kowa ya yi, ko ba haka ba? A sabili da haka, muna fatan fim din 'Taken Kasa' zai ilmantar da mazauna Hong Kong kan tarihin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, ta yadda za mu gamsu da makomarmu."
A jiyan ne kuma, aka shirya bukukuwa kala-kala domin murnar cika shekaru 23 da dawowar Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin.(Murtala Zhang)