logo

HAUSA

Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin

2020-07-01 21:51:27 cri

Ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2020, ake cika shekaru 99 da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta Sin, jam'iyya mafi yawan mambobi a duniya.

Da farko dai, jam'iyyar ta fara ne da mambobi fiye da 50 kacal, amma ya zuwa yanzu da jam'iyyar ke cika shekaru 99, tana mulki har na tsawon shekaru 71 a kasar Sin, ta kai ga samun mambobi fiye da miliyan 90, da daukacin al'ummun kasar Sin wajen samar da gudummawar tattalin arziki ga duniya, wanda ya kai kashi 30 cikin dari bisa adadin tattalin arzikin duniya. Don haka ta maida kasar Sin ta zama muhimmiyar kasa da ta sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Masu amfani da yanar gizo su kan kira jam'iyyar da sunan "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi".

Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin

Bisa burinta da aka tsara tun da farko, wato neman zaman jin dadi ga jama'ar kasar Sin, da neman farfadowa ga al'ummar kasar Sin, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta kiyaye gudanar da ayyukanta na kokarin samun ci gaba.