logo

HAUSA

Kantonmar yankin Hong Kong ta yi kira ga kasa da kasa da su mutunta ikon kasar Sin na kare tsaron kasa

2020-07-01 15:27:32 cri

Kantonmar yankin Hong Kong ta yi kira ga kasa da kasa da su mutunta ikon kasar Sin na kare tsaron kasa

A jiya Talata ne aka kaddamar da taron hukumar kare hakkin dan Adam na MDD karo na 44 a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda babbar kantomar yankin Hong Kong na kasar Sin Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, ta yi jawabi ta kafar bidiyo.

A yayin taron, kasar Cuba ta yi jawabi a madadin kasashe 53, inda suka yi maraba da matakin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na sanya hannu kan dokar tsaro a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Ga karin bayani daga Maryam Yang…

Cikin jawabinta, babbar kantomar yankin Hong Kong na kasar Sin Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor ta bayyana cewa, batun tsaron kasa 'yanci ne na gwamnatin tsakiyar kasar Sin. Kuma yankin Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin, mai cin gashin kansa, wanda yake karkashin ikon gwamnatin tsakiya. Ta ce, "Ya zuwa yanzu, yankin Hong Kong bai kammala aikin kafa dokar tsaron kasar Sin a yankin ba, lamarin da ya hana yankin aiwatar da nauyin dake kansa yadda ya kamata. Batun tsaron kasa wani muhimmin batun dake shafar al'ummomin kasar Sin biliyan 1.4, ciki har da al'ummomin yankin Hong Kong miliyan 7.5. Shin za a iya ci gaba da yin hakuri kan matsalar da ake fuskanta a fannin tsaron kasa?"

Ta ce, a halin yanzu, akwai matukar bukatar kafa dokar tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Ganin yadda tashe-tashen hankula a yankin Hong Kong suka kara tsananta tun daga watan Yuni na bara sakamakon rura wutar da wasu kasashen waje suka yi. Masu zanga-zanga dake neman raba kasa, sun zubar da kimar kasa da kai hare-hare kan gine-ginen hukumomin gwamnatin tsakiya dake yankin Hong Kong. Wasu 'yan siyasan yankin ma sun yi ikirarin cewa wai za su dakatar da ayyukan gwamnatin yankin, har ma wasu sun roki kasashen ketare da su tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong, da kuma kakaba wa yankin takunkumi. Madam Carrie Lam ta ce, "Abubuwan da suka yi babban kalubale ga tsaron kasa, kuma babu wata gwamnatin kasa a duniya da za ta yi hakuri kan wannan lamari. Wajibi ne a dauki matakai yadda ya kamata domin kare cikakken yankunan kasar Sin."

Haka kuma, Madam Carrie Lam ta ce, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ita ce hukumar koli a kasar Sin dake da ikon kafa dokoki, tana da iko da nauyin kafa dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong. Tana mai cewa, "An kafa dokar tsaron kasa ne, domin hana wadanda suke neman raba kasa da juyin mulki, da yaki da 'yan ta'adda, da kuma hana 'yan kanzagin wasu bangarorin kasashen waje domin bata yanayin tsaron kasar Sin. An kafa wannan doka ce, don mutane kalilan masu aikata wadannan laifuffuka. Game da yawancin mazauna yankin Hong Kong ma, za a iya tabbatar da rayukansu da dukiyoyinsu da hakkokinsu da ma 'yancinsu."

Madam Carrie Lam ta kara da cewa, Yadda aka kafa dokar tsaron kasa a Hong Kong ba zai kawo illa ga manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" da 'yancin yankin Hong Kong ba. Hong Kong na da al'adu iri daban daban, wanda ke mutunta ra'ayoyi daban daban. Amma ba za a iya yin hakuri ko kadan ba batun da ya shafi manufar kasancewar kasa daya, sabo da, in babu wannan manufa, ba za a iya tabbatar da aiwatar da manufar kasancewar tsarin mulki iri biyu a Hong Kong ba. Hakan zai kawo barazana ga zaman karko da wadatar yankin. Dangane da yadda wasu gwamnatoci da 'yan siyasan kasashen ketare suke nuna fuska biyu da kiyayya kan kafuwar dokar, ta ce, lalle sun bata ran al'ummomin Sin. Ta ce, "Duk wadanda suke zargin kasar Sin kan kafa wannan doka, ai su ma suna da dokar tsaron kasa a kasashen su, a don haka, mene ne dalilin da ya sa ba su son ganin yadda kasar Sin ta kafa dokar domin tsaron kanta da ma tabbatar da zaman lafiyar al'ummominta?"

A karshe, Madam Carrie Lam ta ce, muddin aka tsaya tsayin daka wajen aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu", da kuma bin dokar tsaron kasa, tabbas za a dawo da zaman lafiya a yankin Hong Kong, da ma kara samun bunkasuwa. A nan gaba, ita da gwamnatin yankin za su ci gaba da amfani da fifikon da Hong Kong ke da shi, da ma damammakin bunkasuwa da kasar ta samar, domin kyautata zaman rayuwar al'ummomin yankin.(Maryam)