Mazauna kauye na kasar Sin na kokarin nuna al'adun gargajiyarsu ta intanet
2020-06-29 16:33:12 CRI
Kwanan baya, a yayin da yake rangadin aiki a lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin, shugaban kasar Xi Jinping ya jaddada muhimmancin amfanin sayar da kayayyaki ta intanet wajen taimaka wa aikin kawar da talauci. A cewarsa, sayar da kayayyaki ta intanet ba taimakawa jama'a wajen kawar da talauci kadai zai yi ba, har ma da inganta farfado da kauyuka. Yanzu dai a wurare daban daban na kasar Sin, ana iya gano cewa, gudanar da cinikayya ta intanet na kara taka rawa kan kawar da talauci da tabbatar da zaman al'umma mai matsakaicin karfi. "'Yan uwanmu, ga wane irin 'ya'yan itatuwa mai suna apricot da turanci, halinsu na dacewa da jigila zuwa wurare masu nisa. A 'yan kwanakin da suka wuce, idan an dandana akwai tsami kadan, amma yanzu akwai dadi sosai, kuma ya na cike da ruwa." Wannan ne yadda Cui Shuxia ke sayar da kaya kai tsaye ta intanet. Cui Shuxia 'yar shekaru 80 a duniya, wadda ke zama a kauyen Taipingpu na garin Taiping na lardin Shaanxi dake yammacin kasar Sin. Jikanta ya kafa wata cibiyar sayar da kayayyakin aikin gona ta intanet, da ma ta kan taimaka masa gudanar da wasu ayyuka, amma tun daga karshen watan Mayun bana, ta soma sayar da kaya ta intanet. "Shekaru na na haihuwa sun kai 80, amma idan na ga apricot, to sai inji ina son cin su, ina sha'awar cin 'ya'yan itatuwa masu dadi. Kamata ya yi ku sayi irin apricot dinmu, ku sayawa mamanku da ma iyayenta." Domin nuna ingancin apricot na garin Taiping, ko da yake kaka Cui ba ta da hakora, amma ta kan yi gwajin cin apricot ga masu kallo, tare kuma da yin hira da su kan labaru game da apricot na garin, da labarun mazauna wurin, har ma da labaru masu ban sha'awa da suka faru a garin. Maganganun da kaka Cui take fada masu ban dariya ne, kuma suna dacewa da halin da ake ciki, don haka, a cikin kwanaki uku kawai bayan ta soma sayar da kaya ta intanet, ta jawo hankalin masu kallo sama da dubu daya, a cikin mako guda, mutanen da suka kalli bidiyon nata game da sayar da kaya sun wuce miliyan goma, kana kuma apricot da ta sayar a ko wace rana yawan kudinsu ya wuce RMB yuan dubu goma. Masu kallo sun yabawa kaka Cui: "Kaka mai kirki ce." "Kaka Cui mai ban dariya ce, ina son yin hira da ita a kan intanet." "Ina son in karfafa mata gwiwa, tabbas apricot da ta sayar suna da dadin ci." "Ga yadda take kokari, gaskiya ta kasance abin koyi ga matasa." Mazauna kauyen kuma sun yabawa kaka Cui: "Yanzu dai ita tsohuwa ce da ta shahara a intanet, wadda ke wakiltar kauyenmu. Idan babu ita, farashin apricot na kauyenmu ba zai karu ba, gaskiya tattalin arzikin kauyenmu na samun bunkasuwa sakamakon kokarinta." Garin Taiping, ya shahara sosai a nan kasar Sin saboda 'ya'yan itatuwa masu dadin ci. An shuka dabino da wasu 'ya'yan itatuwa iri daban daban kusan muraba'in mita miliyan 20, tarihin garin na shuka apricot ya wuce shekaru 300. A shekarar 2015, Wang Yalou, wato jikan kaka Cui ya kammala karatu a jami'a, ba tare da bata lokaci ba sai ya koma garinsu kauyen Taipingpu, don kafa wani kamfanin sayar da 'ya'yan itatuwa ta intanet. Bisa dogaro da kamfanin na Wang Yalou, garin Taiping ya kafa cibiyar kawar da talauci ta hanyar sana'ar sayar da kaya ta intanet. Bisa kudurin da Wang Yalou ya yi, yayin da kamfaninsa ke sayen 'ya'yan itatuwa daga wajen masu fama da talauci, zai kara biya yuan 0.4 kan ko wani kilogram. Ban da wannan kuma, kamfanin ya sanya hannu da iyalai masu fama da talauci 14 game da samar da ayyukan yi, ta hakan matalautan wurin sun samu hanyar kara kudin shiga. Sakamakon tasiri da yaduwar annobar COVID-19 ke kawowa, Wang Yalou ya damu da halin sayar da apricot, don haka, ya yi gwajin sayar da kaya kai tsaye ta intanet. Ya ce, masu kallo sun tambaye shi game da tarihin apricot na garin Taiping, amma shi ma bai fahimta sosai ba. Da ganin haka, kakarsa ta ce, "tambayar ba wuya, bari in gaya musu." Wang Yalou ya gaya mana cewa, "Na soma sayar da kaya kai tsaye ta intanet tun daga ranar 24 ga watan Mayu, da farko ban dace da irin hanyar sosai ba, amma kaka ta da ma tana sha'awar cinikayya, sai ta gaya min cewa, bari in gwada." Game da wannan, kaka Cui ta ce, "A lokacin, jika na yana zaune a can, an tambaye shi shekaru nawa ne tarihin apricot na garinmu, amma bai iya ba da amsa ba, don haka na ce, bari in taimake ka." Kaka Cui ta ce, tun da take yariniya take son cin apricot, da shekarunta na haihuwa suka kai 20 ta yi aure zuwa kauyen Taipingpu, wanda ke da dogon tarihi wajen shuka apricot. Kaka Cui tana son cin apricot, a waje guda kuma ta sani sosai cewa, ba da sauki ba ake shuka apricot. "Na karbi 'ya'yan itatuwan dukkan mazauna kauyenmu, musamman ma wadancan masu fama da talauci. Dukkanmu mazauna garin Taiping, a gani na, ba iyalinmu kadai ne ya kamata ya kara samun kudin shiga ba, kamata ya yi dukkan mazauna wurinmu su samu wadata." Kaka Cui tana aiki ne tun daga karfe 6 da safe har zuwa karfe 9 da dare a ko wace rana, kuma tana sayar da kaya kai tsaye ta intanet ko da safe ko kuma da yamma. Labarinta da sahihanci da ta nuna sun burge masu kallo masu yawa, ana ta kara yin oda har ma kamfanin Wang Yalou ya kara samun aiki sosai. "Bayan kaka ta shahara a intanet, a gani na, kamar yawan oda na karuwa a ko wane dakika, bisa irin halin da ake ciki, na yi kiyasin cewa, yawan kudin shiga da za mu samu a bana zai ninka sau biyar bisa na da." Game da sayar da kaya ta intanet, kaka Cui ta ce, "Hanyar tana da kyau kwarai, yanzu zaman al'ummar kasarmu na samun ci gaba, kuma tsarin sufuri na samar da sauki wajen jigilar kayayyaki, don haka, bayan na yi bayani kan kayayyakinmu a intanet, sai ake yin oda nan da nan, ba tare da bata lokaci ba sai mu daure kaya, idan ba nisa, a yau in muka aika kaya, to gobe za a karbi kayan." Kaka Cui ta ce, ko ana sayar da kaya a kasuwa ko kuma a intanet, abun mai muhimmanci shi ne, a tabbatar da ingancin kayayyaki, tana fatan ganin za ta yi kokari tare da jikanta don neman hanya mafi dacewa ta sayar da apricot na garinsu.
Idan an ce, kamfanin sayar da kaya ta intanet na Wang Yalou ya bude wata babbar kofa ga apricot na garin Taiping wajen shiga kasuwar daukacin kasar Sin, to, samun karbuwa a intanet da kaka Cui ta yi, ya nuna mana irin gwajin da mazauna kauye suke yi wajen nuna al'adun gargajiyarsu. Sakamakon ci gaban sana'ar sayar da kaya ta intanet, aka karfafa ayyukan kawar da talauci da farfado da kauyuka a nan kasar Sin.