Masu fama da fatara na rukunin karshe na kauyen Zhongba sun kaura zuwa sabbin gidajensu
2020-06-29 14:18:24 cri
Gundumar Xide ta yankin Liangshan da ke lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin tana daya daga cikin gundumomi 7 da har yanzu suke fama da talauci a lardin, inda ake iya samun kauyuka masu fama da fatara guda 28, ciki har da wani kauye mai suna Zhongba, wanda ya kasance kauye daya tilo da ke da mazauna masu fama da fatara fiye da 1000 a duk gundumar Xide. Amma a 'yan kwanakin nan, mazauna kauyen masu fama da talauci na rukunin karshe, sun kaura zuwa sabbin gidajensu.
Shuotizelun daya ne daga cikinsu, shi da iyalansa guda shida sun yi zama cikin wani tsohon daki har na tsawon shekaru fiye da goma. Bisa manufar kaura zuwa wani sabon wurin don kau da talauci da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa, ya samu wani sabon gida mai fadin murabba'in mita 100. A sassafen ranar 15 ga watan nan, Shuitizelun ya fara tattara kayayyakinsa. Ya furta cewa,
"Ina tattara kayayyaki da tufafi da kayayyakin masarufi zan kaura zuwa sabon gida. Gwamnatinmu za ta taimaka mana wajen daukarsu. Bayan na ga sabon gidana, na yi murna sosai, iyalanmu ma sun yi farin ciki matuka."
Wadannan mazauna kauyen Zhongba daga gidaje 14, za a kaurar da su zuwa wani wuri mai nisan kilomita 10. Liu Chao, daraktar Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke kauyen ta bayyana cewa, kwamitin kauyen ya nemi kungiyoyi don taimakawa masu fama da talaucin kaura. Liu ta kara da cewa,
"Wasu mazauna kauyenmu ba su da mota, don haka mun taimaka musu wajen kaura. Yau mun nemi kungiyoyin jin dadin jama'a guda biyu, wadanda ke da motoci goma, domin kai su sabbin gidajensu da gwamnatin ta shirya musu."
Wadannan sabbin gidajen na kusa da kwamitin kula da harkokin kauyen Zhongba, inda ake iya samun gidaje 105 da aka samar wa jama'a da suka kaura daga sauran wurare, da dakunan kwana 50 da birnin Foshan ya taimaka wajen ginawa, da wata makaranta, da wani asibiti, da wata kasuwar shanu da dawaki da tumaki, da ma wata kasuwar amfanin gona. Kereheti, wani dan kauyen Zhongba ya furta cewa, sabon gidansu ya sha bamban sosai da na da, har ma ya wuce zatonsa. Yana mai cewa,
"Bangon tsohon gidana an gina shi ne da kasa, ya kan yi yoyyo yayin da ake ruwan sama. Amma yanzu muna zaune a cikin ginin zamani, lallai babban canji ne, har ma ina tsammanin ko ina mafarki ne."
Bayan da wadannan mazauna kauyen Zhongba masu fama da talauci daga gidaje 14 suka kaura zuwa sabbin gidajensu, dukkan gidaje 410 masu fama da talauci na kauyen sun samu dakunan kwana masu inganci. Liu Chao ta yi tsokaci cewa, a mataki na gaba, za a yi kokarin taimakawa 'yan kauyen wajen fita daga kangin talauci bisa hanyar raya wasu ayyukan farfado da kauyen. Liu ta ce,
"A nan gaba, za mu ba da horo ga wadannan mazauna kauyen kan al'adun zamansu, ta yadda za su iya jin dadin zamansu a nan. Daga baya kuma za mu fara raya sana'o'in kauyenmu, kamar sana'ar shuka shinkafa, aikin sarrafa dankali, da ma aikin sarrafa nama. Bugu da kari, muna fatan za a kaddamar da wasu karin ayyukan farfado da kauyuka a kauyenmu."
Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa ranar 15 ga wata, an riga an kammala aikin gina sabbin gidaje don masu fama da talauci na gundumar Xide, wadanda za a kaurar da su ya zuwa karshen watan nan. Bisa shirin da aka tsara ma dai, za a kau da talauci daga kauyuka 28 na gundumar a shekarar 2020, aikin da zai shafi gidaje 4070 da mutane 17053. Ta hakan za a cimma burin kawar da talauci daga dukkan fannoni a gundumar Xide.(Kande Gao)