logo

HAUSA

Ziyarar shugaba Xi Jinping a Ningxia

2020-06-26 11:21:48 CRI

Daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Yunin shekarar 2020 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai rangadi zuwa sassa daban daban na jihar Ningxia ta kabilar Hui mai zaman kanta da ke arewa maso yammacin kasar. A yayin rangadinsa zuwa unguwar Jinhuayuan da ke birnin Wuzhong na jihar, ya ce, "Dukkan kabilu al'ummar kasar Sin ne, kuma ba za a bar kowace kabila a baya ba, a kokarin da ake na saukaka fatara da gina al'umma mai matsakaiciyar wadata, da kuma zamanantar da harkokin rayuwa." Kalaman da ya karfafa gwiwar mazauna yankin.

Ziyarar shugaba Xi Jinping a Ningxia

Jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta, daya ce daga cikin jihohin kasar Sin 5 masu cin gashin kansu, kuma akwai kabilu da dama a jihar kamar Han, da Hui, da Uygur da dai sauransu. Unguwar Jinhuayuan na birnin Wuzhong da shugaba Xi ya ziyarta, na da mazauna na dindindin 13,850, ciki har da 'yan kabilun Han da Hui da Man da Mongoliya da Tibet da sauransu, wadanda suke zauna lafiya da juna. Bisa jerin manufofin shugabanci da kirkire-kirkire, yankin ya zama wani abun misali na hadin kai da ci gaban kabilun kasar Sin.

Ziyarar shugaba Xi Jinping a Ningxia

Kasar Sin kasa ce da ke da kabilu 56. Bana ita ce shekarar da kasar ta ayyana don fitar da dukkanin al'ummar kasar daga talauci. Sai dai a sakamakon yadda dinbin al'ummar 'yan kananan kabilu suke rayuwa a sassa da ke matukar fama da talauci, shi ya sa kawar da talauci daga yankunan 'yan kananan kabilu ya zama wani muhimmin aikin da ake sanyawa gaba wajen saukaka fatara.

A kokarin da ake yi na fitar da dukkanin al'ummar kasar Sin daga kangin talauci, ba za a bar wata kabila a baya ba. Wannan ita ce al'adar al'ummar Sinawa, haka kuma abu ne da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin ya bukata. (Saminu/ Ibrahim/ Sanusi Chen)