logo

HAUSA

Chissano: Duk lokacin da Mozambique ke gamuwa da matsala, kasar Sin na tare da ita

2020-06-26 14:18:09 cri

 

Chissano: Duk lokacin da Mozambique ke gamuwa da matsala, kasar Sin na tare da ita


Jiya Alhamis, rana ce ta cika shekaru 45, bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Mozambique. Albarkacin wannan rana ta musamman, wakilin CRI ya yi hira da tsohon shugaban kasar Mozambique, Joaquim Chissano, don jin ra'ayinsa dangane da huldar dake tsakanin kasashen 2.

An kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Mozambique a ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 1975, daidai lokacin da Mozambique ta samu 'yancin kanta. A cewar mista Joaquim Chissano, kasar Sin ta dade tana kokarin rufa ma kasar Mozambique baya.

"Abokanmu Sinawa sun fara ba mu taimako a lokacin da mutanen Mozambique ke kokarin neman samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Kasar Sin ta dade tana nuna goyon baya ga kasashen Afirka, musamman ma kasar Mozambique."

A cewar mista Chissano, ana ta kokarin karfafa zumunta da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Mozambique cikin shekaru 45 da suka wuce, har ma ya kai ga kulla huldar hadin kai da ta shafi manyan tsare-tsare na dukkan fannoni tsakanin kasashen 2, a shekarar 2016. Mista Chissano ya ce, duk lokacin da kasar Mozambique ke da butaka, kasar Sin ta kan samar da taimako, "Kasar Sin ta ba mu taimako sosai, yayin da kasar Mozambique ke fama da bala'u daga Indallahi. Misali, a lokacin da mahaukaciyar guguwa da ambaliyar ruwa suka afka wa kasar Mozambique, kasar Sin ta kai mana dauki cikin gaggawa. Sa'an nan likitocin da kasar Sin ta tura zuwa kasar mu, sun riga sun kula da majiyyata fiye da miliyan daya a nan. Ban da haka kasar Sin ta samar da tallafi mai kunshe da abinci, da kayayyakin sufuri ga kasar Mozambique, inda ta cancanci matsayinta na wata babbar kasa dake kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta."

Ban da haka, tsohon shugaban kasar Mozambique ya kara da cewa, tun bayan da aka samu bullar cutar COVID-19 a kasarsa, kasar Sin tana tsayawa tare da kasar Mozambique a kokarinta na dakile annobar. A cewarsa,

"Kasar Sin ba ta nade hannunta ba yayin da muke fama da cutar COVID-19. Ta samar mana da na'urorin kandagarkin cuta, da sauran kayayyakin da muke bukata. Ban da haka, kasar Sin ta ba mu dimbin fasahohin da ta samu a ayyukan tinkarar annobar, wadanda suka taka muhimmiyar rawa cikin aikinmu na hana yaduwar cutar."

Sa'an nan, a fannoin tattalin arziki da ciniki, kasashen Sin da Mozambique su ma suna ta kokarin hadin gwiwa da juna. A cewar mista Chissano, wannan huldar hadin kai ta haifar da alfanu ga jama'ar kasashen 2.

"Ana ta samun ci gaba kan hadin gwiwar Mozambique da Sin ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Kasar Sin tana kokarin zuba jari a Mozambique, da raba mana fasahohi, gami da neman kulla huldar hadin kai tsakanin kamfanonin bangarorin 2."

A cewar mista Chissano, kamfanonin kasar Sin suna taimakawa kasar Mozambique yin amfani da ma'adinanta, gami da albarkatun iskar gas. Sa'an nan a fannin aikin gona, kamfanonin kasashen 2 suna yin hadin gwiwa wajen dasa shinkafa a kasar Mozambique. Wannan aiki, a cewar tsohon shugaban, zai sa kasar Mozambique ta samu isasshen hatsi na ciyar da mutanen kasar, har ma ta sayar da wasu zuwa kasashen waje. Sa'an nan a fannin kayayyakin more rayuwa, kamfanonin kasar Sin na kokarin gina wata hanyar mota, da wata babbar gada ta tsallake teku, a jihar Maputo na kasar Mozambique.

Haka zalika, mista Chissano ya ce, kasar Mozambique ta more matuka da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" da kasar Sin ta gabatar. Ya ce wannan shawara nufinta shi ne neman hada kasashe daban daban, ciki har da kasashen Afirka a waje guda, don samun saukin cudanyar kayayyaki, da ciniki, wadda za ta sanya dukkan wadannan kasashen samun moriya sosai. Sa'an nan, kasar Mozambique, bisa matsayinta na cibiyar sufurin kayayyaki, za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da wannan shawarar. (Bello Wang)