Dr. Muhammad Sulaiman Abdullahi: Ina alfahari da koyawa daliban kasar Sin harshen Hausa
2020-06-23 13:26:21 CRI
Dr. Muhammad Sulaiman Abdullahi, malami ne a sashin koyar da harsunan Najeriya dake jami'ar Bayero a jihar Kano ta Najeriya. Kuma a halin yanzu, yana koyar da harshen Hausa ga wasu daliban kasar Sin dake karatu a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, wato BFSU a takaice.
Dr. Muhammad Sulaiman Abdullahi ya bayyana cewa, daliban kasar Sin suna da kwazo matuka wajen koyon yaren Hausa da al'adun gargajiya na Hausawa, kuma a cewarsa, gwamnatin kasar Sin na iyakacin kokarinta wajen karfafa dankon zumunta da kasashen Afirka, ciki har da Najeriya.(Murtala Zhang)