Yadda Sinawa suke kokarin kare al'adun gargajiya tare da taimakawa matalauta
2020-06-19 16:30:46 CRI
Kasar Sin wata kasa ce mai dimbin tarihi, inda aka gano abubuwan da suka shaida al'adun kasar na wasu shekaru fiye da 5000 da suka wuce. Sa'an nan Sinawa suna kallon tarihi da al'adun su a matsayin abubuwa masu daraja matuka, don haka har zuwa yanzu mutanen kasar na kokarin yada fasahohin al'adunsu daga zuriya wasu wata. Kana a wannan zamanin da muke ciki, yayin da kasar ke daukar manufar kawar da talauci a kasar, an samu damar hada wannan manufa na taimakawa matalauta, da aikin kare al'adun gargajiya tare.