logo

HAUSA

Ya kamata Sin da Afirka su yi hadin gwiwa don kafa tsarin kiwon lafiya na Sin da Afirka na bai daya

2020-06-18 14:12:44 cri

A daren jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya shugabanci taron kolin Sin da Afirka na musamman, kan hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19, tare da yin jawabi mai taken "Yin hadin gwiwa don kokarin yaki da cutar COVID-19 tare", inda ya jaddada cewa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga Afirka, wajen yaki da cutar COVID-19, da yin kokarin tabbatar da lafiyar jama'a, da yin hadin gwiwa a tsakaninsu, da sada zumunta da juna, don kafa tsarin kiwon lafiya na Sin da Afirka na bai daya. Kana an gabatar da hadaddiyar sanarwar taron, inda aka shaidawa kasa da kasa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka mai karfi.

Kasashen Sin da Afirka ta kudu, wadda ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka(AU), da kasar Senegal dake shugabancin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) ne suka shirya wannan taron cikin hadin gwiwa ta kafar bidiyo.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, da shugaban kasar Senegal, da sauran shugabannin kasashen Afirka, da kuma shugaban kwamitin kungiyar AU sun halarci taron. Kana babban sakataren MDD, da babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, su ma sun halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya ba da shawarar nuna juyayi ga wadanda suka mutu a sakamakon cutar, da jajantawa iyalansu. Shugaba Xi ya yi nuni da cewa,

"A halin yanzu, ana ci gaba da samun yaduwar cutar COVID-19 a dukkan duniya. Sin da Afirka suna fuskantar yanayin yaki da cutar, da kiyaye bunkasuwar tattalin arziki, da kuma zaman rayuwar jama'a. Ya kamata a maida rayuwar jama'a a gaban komai, da yin amfani da albarkatunsu, da hadin gwiwa, don tabbatar da tsaron rayuwar jama'a da lafiyarsu, da kuma kokarin rage illar da cutar ta kawo."

Xi Jinping ya bayyana cewa, ya kamata Sin da Afirka su yi hadin gwiwa wajen yaki da cutar COVID-19 tare. Ya ce Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan yaki da cutar na kasashen Afirka, da samar da gudummawar kayayyaki, da tura tawagogin masanan likitanci ga Afirka, da kuma taimakawa kasashen Afirka, don zuwa kasar Sin sayen kayayyakin yaki da cutar. Kaza lika Sin za ta fara gina cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka kafin lokacin da aka tsara, a kokarinta tare da Afirka, wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya, bisa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka. Kana za a gaggauta gina asibitocin sada zumunta na Sin da Afirka, da yin hadin gwiwa a tsakanin asibitocin kasashen biyu, don yin kokarin kafa tsarin kiwon lafiyar Sin da Afirka na bai daya. Sin ta yi alkawari cewa, bayan da aka gama nazari da yin amfani da allurar rigakafin cutar COVID-19, za ta baiwa Afirka ita da farko.

Bugu da kari, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu matakai na inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da jaddada cewa, Sin da Afirka za su tsaya tsayin daka, kan ra'ayin bangarori daban daban, da nuna adawa ga siyasantar da annobar COVID-19, da nuna wariyar launin fata, da kuma nuna goyon baya ga adalci a duniya. Sin tana son yin kokari tare da Afirka, wajen tabbatar da tsarin sarrafa harkokin duniya a karkashin tsarin MDD, da nuna goyon baya ga hukumar kiwon lafiyar duniya, da samar da gudummawa wajen yaki da cutar, da tabbatar da moriyar Sin da Afirka, da kasashe masu tasowa, da kuma sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka zuwa wani sabon matsayi. Shugaba Xi ya jaddada cewa,  

"Yau mun gudanar da wannan taro, don cika alkawarin da aka tsara a gun taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da samar da gudummawa wajen yin hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 a duniya. Na yi imani cewa, za a kawo karshen wannan cuta, ta yadda jama'ar Sin da Afirka za su kara jin dadin zaman rayuwa."

Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, yayin da cutar COVID-19 take yaduwa a duniya musamman a Afirka, an gudanar da wannan taro, wanda ke da babbar ma'ana. Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa,

"Wannan taro yana da ma'ana ta musamman, wanda ya shaida kokarin Sin da Afirka kan inganta hadin gwiwarsu. A madadin jama'ar nahiyar Afirka, ina godiya ga shugaba Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin, domin Sin ta samar da na'urorin asibitoci, da kayayyakin rigakafin cutar da sauransu ga nahiyar Afirka." (Zainab)