logo

HAUSA

Sin ta samar da karin damar yaki da talauci karkashin gasar Olympic

2020-06-18 16:22:38 CRI

Wei Fenglian, mai shekaru 82 da haihuwa, na zaune ne a yankin da za a yi wasan kankara na lokacin sanyi a shekarar 2022 dake garin Chongli na nan kasar Sin. A yanzu wannan dattijuwa ba ta bukatar dogaro kan 'ya'yanta 3 a fannin samar mata da kudaden lura da rayuwa, kasancewar ta a yanzu tana karbar kudaden diyyar filin ta na haya dake wannan gari. Kauyen Dongmaokeling inda Wei take, ya samarwa filin wasan kankara na Fulong Ski Resort wuri mai fadi, inda a duk shekara ake gudanar da wasanni na tsawon kwanaki 101, wanda kuma a shekarar 2019 da ta gabata, ya jawo masu yawon bude ido da yawan su ya kai 920,000. Kauyen wanda ke kunshe cikin yankin tsauni, a baya wuri ne dake da yawan matalauta. Dukkanin 'ya'yan Wei sun fice daga wannan kauye domin zuwa neman aikin yi. Li Hai, shugaban jam'iyya na kauyen, ya bayyana cewa Wei na karbar kudi da suka haura kudin Sin yuan 8,000, kwatankwacin dalar Amurka 1,121 a duk shekara a matsayin filin da ta baiwa wurin wasan kankara na Fulong Ski Resort a matsayin haya. A daya hannun, dattijuwar tana samun karin wasu kudaden shiga daga dan alawus da take karba, da fanshon ta na tsofaffi, da wanda ake baiwa mutanen da suka sadaukar da filayen su domin raya gandun daji. Garin Chongli, wanda ke gundumar Zhangjiakou na lardin Hebei dake arewa kasar Sin, yana da nisan kilomita 200 arewa maso yammacin birnin Beijing. Wuri ne da ya shahara a fannin wasan zamiya na kankara, tun bayan da aka zabi wuri a matsayin wuraren da za a gudanar da wasannin kankara na lokacin sanyi da kasar Sin za ta karbi bakunci a shekarar 2022. A shekarar 2015, yankin mai yawan tsaunuka na da kaso 16.8 bisa dari na jimillar mutane sa sama da 100,000, dake rayuwa a kasa da kudin shiga na ajin matalauta, a lokacin ne kuma aka baiwa birnin Beijing damar karbar bakuncin gasar wasannin kankara tare da birnin na Zhangjiakou. A matsayin dama ta cin gajiya daga wasannin lokacin sanyi, biranen Beijing da Zhangjiakou sun hanzarta samar da ababen more rayuwa da suke hade sassan biyu. An riga an kammala manyan ayyuka a wurin, ciki hadda layin dogo na jiragen kasa masu sauri tsakanin Beijing zuwa Zhangjiakou, wanda aka fara aiki da shi a karshen shekarar bara. A Chongli, akwai kusan mutane 30,000 da aka dauka aiki a fannin tallafawa harkokin wasanni da fannin bude ido. A watan Mayu na shekarar 2019, an kammala aikin fitar da gundumar daga kangin talauci. Kari kan wasan kankara, Chongli ya kansace waje da ake gudanar da wasannin kasa da kasa har 168, na "Ultra-Trail Challenge", da na "BMW HTC China Relay", da wasan gudu na juriya wato "world's endurance sport of Spartan Race". A watan Janairun shekarar 2019, mujallar "New York Times" ta zabi Chongli a matsayin daya daga wurare 52 dake sahun gaba, ga masu yawon bude ido na shekarar, sakamakon irin karbuwa da wasan kankarar garin suka yi. Yang Zhiguo, daya daga jami'an dake aikin yaki da fatara a gundumar ta Chongli, ya ce mahukuntan wurin sun tsara yadda masu gudanar da wasanni a wurin, za su dora muhimmanci ga batun samar da guraben ayyukan yi ga matalauta dake zaune a yankin.

Shi Yuping dake zaune a kauyen Xishizigou a garin Chongli, mai shekaru 43 da haihuwa, tana da 'ya'ya 2, tana kuma aiki a matsayin sabis a wurin wasan kankara na Fulong Ski Resort. Ta ce kudaden shiga da take samu a wannan aiki, ya ba ta damar rayuwa kusa da gida.