'Yan kasuwan Kenya suna mai da hankali kan babban taron baje kolin harkokin ciniki na birnin Guangzhou da ake yi ta yanar gizo
2020-06-18 10:36:32 cri
An bude babban taron baje kolin harkokin ciniki a birnin Guangzhou na kasar Sin karo na 127 ta yanar gizo, sakamakon yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. A yayin taron, ana amfani da fasahohin zamani, ta yadda 'yan kasuwa za su iya yin oda da ciniki ta yanar gizo. 'Yan kasuwa da shugabannin kamfanonin kasar Kenya, suna mai da hankali matuka kan babban taro na wannan karo.
Shugaban kawancen kamfanoni masu mallakar kansu na kasar Kenya Timothy Odongo, ya bayyana cewa, gudanar da taron ta yanar gizo, zai samar da sauki ga 'yan kasuwan kasarsa, wajen yin oda da sayan kayayyaki, zai kuma kafa dandalin mu'amala a tsakanin shugabannin kamfanonin kasar Sin da na kasar Kenya, yayin da ake samar da sabbin damammaki ga hadin gwiwar ciniki a tsakanin kasashen biyu a lokacin annoba. (Maryam)