logo

HAUSA

Ba za a iya bata huldar dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin ba

2020-06-16 13:10:25 cri

A halin yanzu, cutar COVID-19 na bazuwa cikin sauri a nahiyar Afirka. Sa'an nan, bisa matsayinta na aminiyar kasashen Afirka, kasar Sin ta yi kokarin samar da dauki ga kasashen Afirka. Amma duk da haka, wasu mutane suna neman bata huldar dake tsakanin Afirka da Sin.

Alkaluman da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta nahiyar Afirka ta gabatar, sun nuna cewa, ya zuwa ranar 14 ga watan da muke ciki, an gano masu kamuwa da cutar COVID-19 dubu 230 a kasashe 54 dake nahiyar Afirka, inda yawan mutanen da suka mutu ya kai 6200. Ban da wannan kuma, babban magatakardan MDD Antonio Guterres, ya bayyana a cikin wani rahoto cewa, annobar COVID-19 za ta tsananta yanayin da ake ciki na fama da rashin daidaito tsakanin al'umma, da matsalolin yunwa, da tamowa, gami da tsananin talauci.

Sa'an nan, a nata bangare, kasar Sin ta dade tana kokarin kulla huldar hadin kai tare da kasashen Afirka. A lokacin da kasar Sin ke cikin wani hali mai wuya a kokarin fama da cutar COVID-19, shugabannin kasashen Afirka fiye da 50 sun nuna tausayi da goyo baya ga kasar Sin. Don haka yayin da nahiyar Afirka ke jin radadin annobar, kasar Sin ta aike da dimbin kayayyakin kandagarkin cutar zuwa kasashen Afirka, gami da tura wasu tawagogin masanan ilimin aikin likitanci, don taimakawa kasashen Afirka gudanar da ayyukan dakile cutar COVID-19.

Kafar watsa labarai ta DW wato Muryar Jamus, ta watsa wani labari dake cewa, kusan dukkan kasashen dake nahiyar Afirka na bukatar samun tallafi daga kasar Sin, a kokarinsu na tinkarar annobar. Zuwa yanzu, tawagogin masanan ilimin aikin likitanci na kasar Sin, suna ba da taimako a fannin aikin jinya a wasu kasashe 45 dake nahiyar Afirka, inda suka gudanar da kwas na horaswa ta fuskar kandagarkin cutar fiye da 400, aikin da ya shafi ma'aikata masu kula da aikin jinya fiye da dubu 10 na kasashen. Abin da ya sanya mista Francisco Obama Asue, firaministan kasar Guinea Bissau, bayyana kasar Sin a matsayin wata aminiya ta gaske, wadda kasashen Afirka ba za su iya rasa ta ba.

Sai dai a nasu bangare, wasu 'yan siyasar kasar Amurka ba sa jin dadi game da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Inda suke ta kokarin neman rusa huldar dake tsakanin bangarorin 2, ta hanyar yada jita-jitar cewa kasar Sin ta sa kasashen Afirka tsunduma cikin tarko na yawan bashi, da shafa kashin kaji ga shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar. Amma hakikanin abun da suka faru na karyata jita-jitar da aka yada. A shekarun fiye da 10 da suka wuce, kasar Sin ta taimaka wajen gina hanyoyin mota a kasashen Afirka, wadanda tsawonsu ya kai fiye da kilomita dubu 10, da layin dogon da tsawonsa ya kai fiye da kilomita dubu 6, da sauran kayayyakin more rayuwar jama'a da yawa, da suka hada da laburare, da makarantu, da asibitoci.

Game da batun bin bashi, bankin duniya da sauran hukumomi masu kula da aikin hada-hadar kudi sun bayyana cewa, yadda ake samar da bashi bisa shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" hakika ba zai kara nauyi a wuyan kasashen Afirka ba, a fannin cin bashi, musamman ma ta la'akari da wani yanayi na daidaiwa daida tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, ta fuskar yin muhawara kan batun bashi, da yadda kasar Sin take matukar girmama kasashen Afirka, da lura da ra'ayoyinsu. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta riga ta yi alkawarin dage basussukan da take bin wasu kasashe marasa karfin tattalin arziki 77, ciki har da kasashen Afirka da yawa.

Moussa Faki Mahamat, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka AU, ya taba bayyana cewa, kasashen Afirka da kasar Sin aminai ne, kuma wadanda suke rufa ma juna baya a fagen yaki, ko kuma yayin da ake fuskantar mawuyacin hali, don haka ba wani abu da zai iya lalata huldar dake tsakanin bangarorin 2.

A shekarar 2019, yawan darajar cinikayyar da aka yi tsakanin Afirka da Sin ta kai dala biliyan 200. Kana kasar Sin ta zuba dalar Amurka biliyan 110 zuwa kasashen Afirka, yayin da kamfanonin kasar Sin fiye da 3700, suna gudanar da harkokinsu a kasashen Afirka daban daban. Zai fi dacewa, a ba jama'ar kasashen Afirka damar bayyana ra'ayinsu, dangane da huldar dake tsakanin Afirka da Sin, maimakon a yada jita-jitar da wasu 'yan siyasan kasar Amurka suke yi. (Bello Wang)