logo

HAUSA

Mu ainihin abokan juna ne

2020-06-15 21:26:11 CRI

 

Zhaxicuomao, 'yar kabilar Tibet da ta fito daga yankin Yushu na lardin Qinghai na kasar Sin, wadda shekarunta na haihuwa suka kai 19, a 'yan kwanakin nan tana ta mayar da hankali kan labaru game da tawagar kwararru a fannin likitanci wajen yakar cutar COVID-19 ta kasar Sin dake ba da tallafi a Brazzaville, hedkwatar jamhuriyyar kasar Congo.

 

Mu ainihin abokan juna ne

 

Daga tudun Qinghai-Tibet zuwa fadamar Congo, akwai nisan kilomita dubun-dubata a tsakanin tsawonsu bisa tebur din teku, kuma akwai nisan kilomita kusan dubu 10 wajen tafiya da jirgin sama. Amma, ana sada zumunci a tsakanin wuraren biyu. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da haka.

Za mu soma watsa muku wannan labari ne a shekaru 10 da suka gabata, a lokacin aka samu wani hadari mai tsanani a nan kasar Sin.

A ranar 14 ga watan Aflilu na shekarar 2010, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai maki 7.1 a ma'aunin Richter, a karamin yanki mai cin gashin kansa na Yushu na kabilar Tibet na lardin Qinghai. Makarantar firamare ta Wen Le dake gundumar Chengduo ta yankin Yushu tana da nisan kilomita kimanin 100 da wurin da aka fi fama da girgizar kasa, don haka ta lalace sosai. Makarantar da Zhaxicuomao ta yi karatu na wurin. har zuwa yanzu dai, tana tunanin yadda makarantarsu take bayan girgizar kasar. Ta bayyana cewa,

"A lokacin farko da muke karatu a makarantarmu bayan girgizar kasa, lallai halin karatu ba shi da kyau, dukkanmu mun yi karatu da cin abinci a cikin tantuna, kuma ba mu da isassun kayayyakin koyarwa. A lokacin, mun yi fatan sake komawa aji don yin karatu a gaban tebur."

Da ya samu labarin hadarin da aka samu a yankin Yushu, shugaban jamhuriyar kasar Kongo Denis Sassou-Nguesso, wanda ya halarci bikin baje koli na kasa da lasa da aka shirya a birnin Shanghai na kasar Sin, ya bayyana cewa, ya yi fatan ba da tallafin gina wata makarantar firamare a yankin Yushu, a cewarsa "duk yawan kudin da za a kashe, jamhuriyar Kongo za ta dauki alhaki ."

 

Mu ainihin abokan juna ne

 

A ranar 22 ga watan Yuli na shekarar 2012 aka shirya bikin kammala aikin gina wannan makarantar firamare, a yayin bikin kuma ana yayyafi a yankin Yushu, ministan harkokin wajen jamhuriyar Kongo a lokacin Basile Ikouébé wanda ya tafi Yushu don halartar bikin, ya ce, "A kasarmu, ruwa na nufin fatan alheri da lafiya a nan gaba." Tun daga wannan rana kuma, makarantar firamare ta Wenle, wadda ta kasance makarantar marayu daaya kacal a gundumar Chengduo ta yankin, ta kulla alaka da wannan kasar dake nahiyar Afirka. A gaban kofar makarantar dai, an rataye wani allon sanarwa, inda aka rubuta kalmomi kamar haka "Makarantar firamare ta sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da jamhuriyar Kongo". Bayan Zhaxicuomao da abokan karatunta sun koma makarantarsu, gine-ginen zamani sun ba su mamaki sosai, sun yi farin ciki kwarai da gaske, ta ce, "Bayan tallafin da jamhuriyar Kongo ta ba mu, yanzu muna da azuzuwa masu fadi, da sabbin teburori da kujeru, har ma da dakin litattafai da dai sauransu. Gaskiya wannan babban tallafi ne gare mu, ba za mu manta da irin taimakon ba." Shekarar 2014 shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da jamhuriyar Kongo. A ranar 13 ga watan Yuni na shekarar, an gayyaci wasu daliban Makarantar firamare ta sada zumunci tsakanin kasashen Sin da jamhuriyar Kongo don halartar bikin murnar a matsayinsu na masu shaida zumunci tsakanin kasashen biyu, ciki har da Zhaxicuomao. Wannan ne kuma karo na farko da suka fita daga yankinsu dake tudu. A masaukin baki na gwamnatin kasa na Diaoyutai dake nan birnin Beijing, shugaban jamhuriyar Kongo Denis Sassou-Nguesso ya yi mu'amala tare da wadannan yara. Game da wannan, Zhaxicuomao ta ce, "A yayin da muke halartar bikin murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da jamhuriyar Kongo a shekarar 2014, mun yi farin ciki sosai, ba mu taba tunani mu yara za mu iya samun damar hira da shugaban kasar Kongo ba."

 

Mu ainihin abokan juna ne

 

Yara da yawa dake yankin Yushu, an haife su a shekarar 2010 da aukuwar girgizar kasar. Don haka, tun da suke kakanan yara, sun san cewa, suna da alakar musamman da wancan kasar mai nisa. Watan Satumba na ko wace shekara watan godiya ne na makarantar sada zumunci tsakanin kasashen Sin da jamhuriyar Kongo, shugaban makarantar Song Gang ya ce, "Yaranmu ba za su manta da wadanda suka ba mu tallafi a lokacin can ba." Yanzu dai, ana fuskantar yaduwar cutar COVID-19 a duk duniya, ciki har da nahiyar Afirka, wadda ta fi yin hasara sakamakon annobar. Kasar Sin ta cimma nasara bisa mataki na farko wajen dakile cutar, kana ta samu fasahohi masu inganci na tinkarar annobar.

Mu ainihin abokan juna ne

 

Wata rana, a yayin da Zhaxicuomao ke kallon talibijin, ta samu labari game da yadda tawagar kwararru a fannin aikin jinya ta kasar Sin ke gudanar da ayyukansu a Brazzaville na jamhuriyar Kongo. Tun da tawagar ta isa Brazzaville a ranar 23 ga watan Mayu har zuwa ranar 31 ga watan Mayu, kwararrun kasar Sin sun ziyarci hukumomin aikin jinya guda 6, da halartar taro har sau 18, da ba da horo sau 30, da kuma ba da jagoranci kan fasahohi sau 6 da dai sauransu.

A ganin masu aikin jinya na wurin, kwararrun kasar Sin suna cike da fasahohi masu yawa wajen ba da jinya, wannan ne abubuwan da suke bukata cikin gaggawa.

 

Mu ainihin abokan juna ne

 

A yayin da yake ganawa da kwararru na tawagar kasar Sin, firaministan jamhuriyar Kongo Clément Mouamba ya ce, kwararrun kasar Sin sun zo kasarsa ne a lokacin da ya dace, a cewarsa, "A yayin da muke fuskantar wahala, wace kasar ce ta tsaya tare da mu, wace kasa ce ta kasance abokiyarmu ta gaskiya, ai mun fahimci batun nan sosai."