logo

HAUSA

Ficewar Amurka daga WHO zai shafi moriyarta

2020-06-11 16:38:51 CRI

A ranar 18 ga watan Mayun shekarar 2020 ne, shugaba Donald Trump ya rubutawa babban darektan hukumar lafiya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus wasika, inda ya yi barazanar cewa muddin hukumar WHO ta gaza yin wasu sauye sauye cikin kwanaki 30 daga wancan lokacin, to ba shakka Amurka za ta dakatar da biyan kudaden mamba ga hukumar, sannan za ta karkatar da kudaden da take baiwa hukumar zuwa wasu fannoni na daban, kana Amurkar za ta sake yin nazarin ko za ta ci gaba da kasancewa mamba a WHO ko akasin haka.

Bayan wannan barzana da Trump ya yi, sai kwatsam ya sanar da cewa, kasarsa ta fice daga cikin WHO, matakan da kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi.

Sai dai a yayin da Amurka ke daukar wannan mataki, a hannu guda kuma, wasu manyan jami'an kungiyar tarayyar Turai EU da kasashen Iran da Rasha suna yiwa Amurkar hannunka mai sanda kan bukatar ta sake tunani kan kudirin da ta dauka na yanke alaka da hukumar ta WHO, domin hakan zai shafi moriyarta.

A yayin da duniya ke fama da wannan kalubalen COVID-19, yanzu lokaci ne da ya dace a hada gwiwa, domin neman mafita tare a maimakon nuna bukatar kashin kai, amma masu iya magana na cewa, mai daki shi ya san inda yake masa Yoyo. (Saminu, Ibrahim/Sanusu Chen)