logo

HAUSA

Kamfanonin kasar Sin suna kokarin taimakawa rage talauci a kasar

2020-06-05 16:33:16 CRI

 

Idan mun nazarci manufar kasar ta fuskar kawar da talauci, za a ga cewa gwamnati ta raba ayyukan ga sassa daban daban na kasar. Misali, idan a wani wuri ana samun matalauta. To, hukumomin wurin, gami da kamfanonin mallakar kasa, ko kuma masu zaman kansu, kowanensu zai dauki nauyi na taimawa wasu daga cikin matalautan, inda suke neman daukar wadannan matalauta domin su yi aiki a wajensu, ta yadda za su samu albashi a kai a kai, da karin kudin shiga. Don neman samun cikakken bayani kan yadda ake gudanar da manufar a matakin kamfani, Bello Wang ya yi hira da wasu jami'ai na wani banki da ake kira CBC, ko kuma banki na aikin raya kasa na kasar Sin. Wadannan jami'ai sun gaya mana yadda bankinsu ke kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansa don taimakawa matalauta.