logo

HAUSA

Dokar tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong da aka kafa za ta ba da tabbaci wajen aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" yadda ya kamata a yankin

2020-06-03 14:26:07 cri

A karshen watan Mayu, yayin taron shekara-shekara na hukumar kafa dokoki ta koli ta kasar Sin, aka zartas da kudurin kafa da kyautata dokokin kare tsaron kasa da tsarin gudanarwa dake shafar yankin Hong Kong na musamman, wanda aka tsara yayin taron majalissar wakilan jama'ar kasar Sin. Kana aka umarci zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama'ar kasa da ya kafa dokokin da abin ya shafa domin kafa da kyautata dokokin kare tsaron kasa da yadda za a aiwatar da ita a yankin Hong Kong na musamman.

Wannan kuduri da aka zartas yana da muhimmanci wajen kyautata dokokin kare tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong, da tabbatar da aiwatar da manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" yadda ya kamata a yankin Hong Kong. Hakan ya nuna babbar aniyar kasar Sin wajen kare 'yanci da tsaron kasa, da kuma nuna adawa kan yadda kasashen ketare ke tsoma baki a harkar yankin Hong Kong.

A baya kasar Burtaniya ta yi mulkin mallaka a yankin Hong Kong har tsawon shekaru 100, sa'an nan, aka dawo da yankin Hong Kong karkashin ikon kasar Sin a shekarar 1997, inda aka kafa yankin musamman na Hong Kong. A sa'i daya kuma, an fara aiwatar da babbar dokar yankin musamman na Hong Kong ta jamhuriyar jama'ar kasar Sin, karkashin ka'ida ta 23 dake cikin babbar dokar, ya kamata yankin Hong Kong ya kafa dokokin da suka shafi aikace-aikacen cin amanar kasa, neman raba kasa, rura wutar tashin hankali, da bayyana sirrin kasa, da hana kungiyoyin siyasa na kasashen ketare gudanar da harkokin siyasa a yankin Hong Kong, da kuma hana kungiyoyin siyasa na yankin Hong Kong mu'amula da kungiyoyin siyasa na kasashen ketare. Amma, ba a aiwatar da wannan ka'ida kamar yadda ake fata a yankin Hong Kong ba, yadda bangarorin kasashen ketare masu adawa da gwamnatin kasar Sin suka tsoma baki a harkokin yankin, lamarin ya kawo barazana ga tsaron kasar Sin.

A lokacin barkewar babbar matsalar kudi ta duniya a shekarar 2008, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta ba da goyon baya da taimakawa gwamnatin yankin Hong Kong, ta yadda yankin ya sami gaggarumin ci gaba. Amma, a shekarar 2019, ma'aunin tattalin arzikin na GDP a yankin Hong Kong ya ragu da kaso 1.2 idan aka kwatanta da na shekarar 2018, sakamakon tashe-tashen hankula da aka yi fama da su na tsawon watanni da dama a lokacin zafi na bara a wannan yanki.

Shugaban cibiyar nazarin harkokin yankunan Hong Kong da Macao ta kasar Sin, Liu Zhaojia ya bayyana cewa, an tsara "dokar tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong", ba kawai domin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin ba, har ma, domin magance matsalar tsaron kasa baki daya sakamakon batun Hong Kong. Matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka domin sanar wa gamayyar kasa da kasa cewa, Sin na tsayawa tsayin daka wajen kare 'yancin da tsaron kasa.

Al'ummomi daga bangarori daban daban na yankin Hong Kong sun yi maraba da kudurin majalissar wakilan jama'ar kasar, suna ganin cewa, kudurin ya dace da bukatun al'ummar Hong Kong, zai kuma tallafa musu, wannan shi ne fatan dukkanin al'ummomin Sin.

Kuma, dukkanin kasashen duniya sun yi maraba da aniyar kasar Sin ta kare tsaron kasarta.

Kasashe da dama da suka hada da, Koriya ta Arewa, Pakistan, Vietnam, Laos, Rasha, Serbia da Iran da sauransu sun nuna goyon baya ga kafa dokar kare tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong, inda suka jaddada cewa, batun yankin Hong Kong, batu ne na cikin gidan kasar Sin, ya kamata a martaba dokokin kasa da kasa, na daina tsoma baki a harkokin gidan kasashen ketare. Sun kuma nuna fatan samun zaman lafiya da wadata a yankin Hong Kong, da nuna kiyayya ga wadanda suke son bata manufar "kasa daya, tsarin mulki iri biyu".

Amma, kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya su kan tsoma baki cikin harkokin kasar Sin, ko da a ranar 27 ga watan Mayu, ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, daftarin kundin dokar dake shafar yankin Hong Kong da majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da shi, ya sa halin yanzu, yankin Hong Kong ba shi da 'yancin cin gashin kansa, har ya ce, kasarsa za ta soke matsayin musamman na yankin Hong Kong. Sa'an nan, a ranar 28 ga watan Mayu, ministocin harkokin wajen kasashen Amurka, Burtaniya, Australia da Canada sun fidda sanarwar hadin gwiwa, inda suka zargi kasar Sin cewa, wai dokar tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta kafa za ta lalata 'yancin yankin Hong Kong.

A hakika dai, kasar Amurka ita kanta ta taba gabatar da dokokin tsaron kasa a kalla guda 20, amma, a ganin 'yan siyasan kasar Amurka, bai dace Sin ta tsara doka a yankin Hong Kong ba. Wannan ya nuna fuska biyu da Amurka ta nuna kan wannan batu.

Wadannan 'yan siyasa sun musanta 'yancin kan kasar Sin, da musanta yankin Hong Kong a matsayin wani bangare na kasar Sin, domin tilastawa yankin Hong Kong bin umurnin kasashen yamma, wajen matsa wa kasar Sin lamba, ta yadda wadannan kasashen yammacin duniya za su cimma muradunsu da ba su dace ba.

Wasu sun nuna damuwa cewa, ko dokar za ta haddasa janyewar masu zuba jari daga yankin Hong Kong? Dangane da wannan batu, dan kasuwar kasar Switzerland, Angelo Giuliano ya bayyana cewa, 'yan kasuwan kasashen ketare, da kamfanoni masu jarin waje za su iya barin yankin Hong Kong, saboda tashe-tashen hankula dake faruwa, amma dokar tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong ba za ta haddasa illa ga yankin Hong Kong a matsayinsa na cibiyar hada-hadar kudi ta duniya ba. (Maryam)