logo

HAUSA

Dr. Bashir Ahmed Safiyo: Shugabanci nagari shi ne sirrin ci gaban kasar Sin

2020-06-02 16:08:45 CRI

Dr. Bashir Ahmed Safiyo: Shugabanci nagari shi ne sirrin ci gaban kasar Sin

Dr. Bashir Ahmed Safiyo, wani dan Najeriya ne wanda ya shafe shekaru 10 yana zama a kasar Sin, musamman a birnin Shenyang dake arewa maso gabashin kasar. Bayan da ya kammala karatunsa a nan kasar, ya bude wani kamfani yana gudanar da harkokin kasuwanci a fannin na'urorin kiwon lafiya. A zantawarsa da Murtala Zhang, Dr. Bashir Ahmed Safiyo ya ce Sin kasa ce dake cike da damammakin kasuwanci, kana, ya ga manyan sauye-sauye da babban ci gaban da kasar ta samu a 'yan shekarun nan, musamman a inda yake wato birnin Shenyang, sakamakon shugabanci nagarin da ake tafiyarwa.

Kana, Bashir Ahmed Safiyo ya bayyana ra'ayinsa kan dalilin da ya sa kasar Sin ta iya shawo kan yaduwar annobar COVID-19 cikin saurin haka.(Murtala Zhang)