logo

HAUSA

Najeriya za ta maida hankali kan wasan tseren dogon zango a shekarar 2021

2020-05-29 08:56:53 CRI

Najeriya za ta maida hankali kan wasan tseren dogon zango a shekarar 2021 Ministan wasanni na tarayyar Najeriya Sunday Dare, ya ce ma'aikatar sa za ta maida hankali sosai ga horas da 'yan wasa masu gudun dogon zango a shekarar 2021 dake tafe. Cikin matakai da za a dauka a cewar ministan, akwai kara kyautata filayen wasa dake sassan kasar daban daban. Mr. Dare wanda ya zanta ta kafar bidiyo da tawagar masu horas da 'yan wasan kasar, ya ce "Akwai karancin kayayyakin wasa, amma duk da haka ma'aikatar wasanni za ta ware wani kaso na kasafin kudin ta, domin samar da wuraren wasa masu inganci a shekarar ta badi. Zan yi duk mai yiwuwa domin ganin an maida hankali ga kyautata harkar wasan tseren dogon zango. Ministan ya kuma umarci masu horas da 'yan wasan tseren dogon zango da su bullo da tsare tsaren gyaran wuraren horas da 'yan wasa dake Pankshin na jihar Plateau ta tsakiyar kasar, da kuma na Mambila dake jihar Taraba a arewa maso gabashin kasar. Baya ga gyaran filayen gudun dogon zango, ministan ya kuma dorawa masu horas da 'yan wasan nauyin zakulo 'yan wasa masu hazaka, da wadanda a yanzu haka ke yin wasan, kana su shirya fara gudanar da horo ga daukacin masu gudanar da wannan wasa. Ya kuma bukace su da su nazarci yanayin filayen wasan guda 2, domin tantance gyare gyaren da ake bukata, domin daga martabar filayen, ta yadda za su dace da bukata. Mr. Dare ya ce yana fatan masu horas da 'yan wasan za su zo da cikakken tsari, ciki hadda yadda za a gudanar da horo bisa mizani na kasa da kasa. Ko Dortmund za ta iya cin gajiya daga salon wasa ba 'yan kallo? Muhimmin sauyi da aka samu a fannin taka leda a baya bayan nan a bayyane yake, wato dai batun ci gaba da buga wasannin ajin kwararru na Bundesliga na kasar Jamus ba tare da 'yan kallo ba. Wasa ba 'yan kallo, ba shi da armashi a cewar da yawa daga masu sharhi a fannin wasanni, hakan ne ma yasa wasu ke wa salon wasan lakabi da "Wasannin fatalwa." Tun bayan sake bude wasannin kwallon kafa zangon farko da na biyu, mutane da yawa na cewa abun ba armashi. Maimakon shewa, da wakokin magoya baya da aka saba ji, yanzu filayen wasan ba a jin komai na motsin 'yan kallo. To amma yaya tasirin hakan yake kan shi kan sa wasan? Gabanin shiga zagaye na 2 na wasannin Bundesliga ba tare da 'yan kallo ba, magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar kasar na ta tambayar shin ko wadanne kungiyoyi ne za su amfana daga wannan yanayi? Shin ko kungiyar Borussia Dortmund dake matsayi na 2 a kan teburi za ta iya samun nasara kan kungiyar Bayern Munich dake saman teburin? Kafin kammala sauran wasanni 8 dake gaba, Bayern Munich na kan gaba da maki 4. Wasu masu hasashen yanayin wasanni dai na ganin rashin 'yan kallo yayin da ake buga wasanni na iya dakile karsashin da kananan kungiyoyi kan samu a lokacin da suke buga wasa. Ko da 'yan wasan su kan su ma na bayyana irin wannan tunani. A baya bayan nan, mai tsaron gidan Bayern Munich Manuel Neuer ya bayyana cewa, 'yan wasa na iya gamuwa da sauyi ta fuskar yanayin lafiyar kwakwalwa a irin wannan hali. Shi ma dan wasan gaba na Bayern Munich Thomas Mueller, ya yi tsokaci game da wannan sabon kalubale, yana mai cewa "dole mutum ya zabi rungumar wannan yanayi ko kuma ya shiga damuwa. Wannan nauyi ne dake wuyan mu. Batu ne na yin karfin hali, da halayyar 'yan wasa, da ma fadakarwa game da yanayin wasannin dake tafe,". A cewar Neuer, mai yiwuwa ne ma akwai wani karin sabon kalubalen dake gaban 'yan wasa, kari kan wanda aka gani yayin sake bude wasannin. "Har yanzu ba mu kai ga ganin karshen wannan matsala ba." A kalaman Neuer, Akwai ma alkaluma da aka tattara daga sakamakon gwajin yanayin tunani, wadanda ke nuna mai yiwuwa, salon wasannin na yanzu, su shafi sakamakon da ake samu. A daya bangaren jami'an dake horas da 'yan wasa na maida hankali ga yawan karin kwallaye da kungiyoyi masu buga wasa ba a gida ba za su rika ci. Har ma a yanzu ana ganin adadin irin wadannan kwallaye sun sauka zuwa maki 1.63 a kan matsakaicin mizani, sabanin maki 1.5 da ake da shi kafin dakatar da wasannin. A daya hannun kuma, alkaluman yawan kwallaye da kungiyoyin dake buga wasa a gida ke ci, ya yi kasa daga maki 1.75 zuwa maki 1.13. Wannan adadi ya nuna cewa, kungiya daya wato Dortmund ce kadai ke iya cin kwallaye 4 da nema a wasa daya, kamar dai yadda ta cimma nasarar hakan a wasan da kungiyar ta buga da kungiyar Schalke. Game da salon buga wasa kuwa, sakamakon yanayin gasar ta wannan karo, 'yan wasan kungiyoyi dake sahun gaba sun rage yawan rike kwallo da wasa da ita daga kusan maki 19.5 zuwa maki 14.5. Ga alama 'yan wasa a yanzu sun rage yin kasada yayin wasannin. Tsawon lokacin gudu da 'yan wasa ke kwashewa shi ma ya ragu daga taku 2200 zuwa 2018, yayin da gogayyar 'yan wasa daidaiku ta ragu daga kusan maki 223 zuwa 205. Kaza lika 'yan wasan kungiyoyin sun rage yawan gudun su zuwa kusan kilomita 115.5 bisa matsakaicin mizani. Alkaluman da kungiyar Dortmund ta samu sun yi kasa daga 116.3 zuwa 109. Bisa jimilla dai, yawa-yawan 'yan wasan kungiyoyin sun rage yawan gudun da sukan yi a kakar wannan shekara. Bugu da kari, an ba da damar sauya 'yan wasa har sau 5 a wasa daya, wanda hakan ya haifar da sauyin 'yan wasa da yawan sa ya kai 79. Mafi yawa daga kungiyoyin dake buga Bundesliga sun yi amfani da wannan dama wajen sauya 'yan wasa sama da 3 da a baya suke da ikon yi. Da yawa daga masu horas da 'yan wasan na cewa, har yanzu 'yan wasan su ba su kai matsayin gogewa da suke da ita a baya ba, bayan shafe watanni 2 ana zaman gida. Yawan zallar lokacin buga kwallo ya karu daga mintuna 55 zuwa mintuna 57. An kuma samu karuwar kason mika kwallaye tsakanin 'yan wasa da kaso 25 bisa dari. A yayin wasa na farko da aka yi ba 'yan kallo, ba a baiwa wani dan wasa ko daya katin gargadi ko "yellow card" sakamakon korafin wani dan wasan na daban ba. Sabanin hakan, yayin wasanni zagaye 25 na baya, an samu irin wadannan kati na gargadi har 65. Kwararru a fannin taka leda na cewa, kungiyar Dortmund ce kungiya ta farko da ta lashe wasanta a gasar da ake ci gaba da bugawa ba 'yan kallo, inda bayan doke Schalke, ta kuma samarwa kan ta sakamo mafi gamsarwa cikin sauran sakamako da ragowar kungiyoyi masu buga gasar Bundesliga suka samu. 'Yan wasan Man Utd Marcus Rashford da Paul Pogba sun shirya komawa tamaula Marcus Rashford ya ji rauni a bayansa lokacin wasan zagaye na uku na cin Kofin FA da suka fafata da Wolves a watan Janairu 'Yan wasan Manchester United biyu Marcus Rashford da Paul Pogba za su kasance cikin wadanda za a zaba domin buga tamaula idan aka komo Gasar Premier, a cewar kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer. Rashford da Pogba sun yi doguwar jinya lokacin da aka dakatar da gasar saboda annobar korona a watan Maris. Dukkan 'yan wasan sun koma atisaye na rukunin wasu 'yan wasa marasa yawa inda suka hadu da sauran 'yan wasan United a makon jiya. Solskjaer ya ce: "Sun ['yan wasan biyu] warke sosai." Paul Pogba 'zai koma Juventus, Bayern Munich za ta ɗauko Sancho' Marcus Rashford zai yi jinya "Sun bi sahun masu yin atisaye yanzu kuma sun yi duk abin da sauran 'yan wasan suke yi. Ya zuwa yanzu babu wata matsala da suka fuskanta. "Idan muka koma buga gasa, za mu samu cikakkiyar tawaga inda za mu zabi wanda muke so." Rashford ya yi fama da ciwon baya tun watan Janairu yayin da Pogba bai buga galibin wasannin da United ta fafata a cikinsu ba na kakar wasa ta bana saboda ciwon kafa. Aaron Ramsdale: Golan Bournemouth ya kamu da coronavirus Aaron Ramsdale ya buga wa Ingila wasa bakwai a gasar 'yan kasa da shekara 21 Golan Bournemouth Aaron Ramsdale ya ce yana cikin mutum biyu da suka kamu da cutar korona bayan gwajin da hukumomin Gasar Premier suka yi masa. A makon jiya an yi wa 'yan wasa da ma'aikata 996 gwajin cutar korona a zagaye na biyu na gwaje-gwajen da ake yi wa 'yan kwallon. Sai dai ba a fadi mutum na biyu da ya harbu da cutar ba. An tabbatar mutum takwas da ke Gasar Premier sun kamu da korona cikin mutum 1,744 da aka yi musu gwajin cutar. Ramsdale, mai shekara 22, wanda gwajin da aka yi masa ranar Litinin ya nuna ba ya dauke da cutar, ya shaida wa jaridar told the Sun cewa bai nuna alamar kamuwa da cutar ba. Makomar Allan, Todibo, Henderson, Coutinho, Icardi Ighalo yana shirin komawa China "Wannan lamari ya yi matukar girgiza ni. Ban yi mu'amala da kowa ba amma ga shi yanzu ina dauke da cutar," a cewar dan wasan na Ingila, wanda za a killace tsawon kwana bakwai. A gwajin da aka yi na zagayen farko an gano mutanen da dama sun kamu da cutar, ciki har da dan wasan Watford Adrian Mariappa da kuma mataimakin kocin Burnley Ian Woan. Ana sa ran za a fitar da sakamakon gwaji zagaye na uku ranar Laraba. Zlatan Ibrahimovic: Dan wasan AC Milan ya ji rauni a ƙafarsa Ibrahimovic ya zura kwallo hudu a wasa 10 da ya buga wa AC Milan AC Milan ta ce dan wasanta Zlatan Ibrahimovic ya ji rauni a ƙafarsa lokacin da yake atisaye ranar Litinin. Rahotanni sun nuna cewa raunin da dan wasan mai shekara 39 dan kasar Sweden ya ji zai iya barazana ga sana'arsa ta kwallon kafa amma Milan ta shaida wa BBC Sport cewa za a yi masa gwaji ranar Talata. Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce "Za mu san girman matsalar a lokacin." Tsohon dan wasan na Manchester United Ibrahimovic ya koma Milan a watan Disamba a yarjejeniyar wata shida kuma ya zura kwallo hudu a wasa 10 da ya buga wa kungiyar. Serie A: Ibrahimovic ya koma AC Milan Odion Ighalo: Mai yiwuwa dan wasan zai koma China daga Man Utd A bangare guda, gwamnatin Italiya za ta yanke shawara ranar Alhamis kan ranar da za a ci gaba da gasar Serie A. An bai wa kungiyoyi damar komawa atisaye ranar 19 ga watan Mayu, kuma sun kada kuri'ar amincewa a koma gasar Serie A ranar 13 ga watan Yuni.

Hukumar kula da kwallon kafar Italiya ta kebe ranar 20 ga watan Agusta domin a kammala gasar sanna a soma kakar wasa mai zuwa ranar 1 ga watan Satumba.