Taurarin Intanet mata na kabilar Dong sun taimakawa wajen fitar da kauyensu daga talauci
2020-05-26 13:15:50 CRI
Wata tawagar mata daga kabilar Dong na kauyen Gaibao, dake yankin kabilun Miao da Dong na Qiandongnan mai cin gashin kansu a lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, na amfani da shirin bidiyo na kai tsaye da gajerun bidiyo, wajen yayata al'adun kabilarsu da amfanin gona da wuraren yawon bude ido. Lokacin da suke daukar bidiyon, suna karba-karba wajen taka rawar aljanu bakwai na kabilar Dong da ke cikin tatsuniyoyin al'ummar Sin, kuma wasu daga cikin shirye-shiryensu na samun karbuwa sosai a kafar intanet. Sanye da suturun gargajiya ta kabilar, matan kabilar Dong sun nunawa masu kallonsu fannoni daban daban na rayuwar mutanen kabilar, kamar yadda suke abubuwan makulashe, da yadda ake kiwon kifi a fadama, da yadda ake aikin zubi da ayyukan gona. Shirye-shiryen bidiyon na kai tsaye da gajerun bidiyon, sun ja hankalin jama'a zuwa kauyen, kuma sun taimaka wajen fitar da kauyen daga kangin talauci. Wani bidiyo dake nuna matan Dong na kamun kifi a fadama ya samu sama da mutane miliyan 7.2 da suka kalla, kuma sama da mutane 40,000 sun so shirin tare da yin tsokaci, tun bayan wallafa shi a manhajar bidiyo ta Kuaishou ta kasar Sin, a ranar 9 ga watan Yuli na 2019. Amma an samu wannan babban ci gaba ne bayan da Wu Yusheng ya je kauyen Gaibao a matsayin sakataren farko na reshen JKS da ke kauyen, wanda ya bada shawarar amfani da gajerun bidiyo wajen nuna yadda mazauna wurin ke zaman rayuwarsu a 2018, domin sada kauyen da sauran sassan duniya. Duk da kauyen mai tsaunuka na da shimfida mai kyau, hanyar zuwa kauyen ba ta da kyau, saboda rashin kyan yanayin tsarin kasa. A kan shafe sama da sa'o'i 4, kusan kilomita 100 wajen tafiya gundumar Liping daga kauyen Gaibao. Sai dai, rashin kyan hanya ya taimaka wajen alkinta al'adun kabilar Dong. An kare tsarin gidajen katako irin na gargajiya da albarkatu da al'adun gargajiya na wurin. A ranar 14 ga watan Fabrairun 2018, rana ta farko da Wu Yusheng ya kama aiki a matsayin sakataren kauyen, ya karbi alhakin jagorantar fitar da kauyen daga kangin talauci. Daga nan, ya dauki wata 1 wajen gudanar da bincike a kauyen. Wu ya bayyana cewa, "A farkon zuwana kauyen nan, na yi zaton cewa, kawar da talauci wani aiki ne da ba zai yiwu na kammala ba. Bayan na yi bincike har na tsawon wata guda, na gano cewa, raya ayyukan gona na salon gargajiya ba zai taimaka wajen cimma burin kawar da talauci ba, sai mun yi amfani da hanyar zamani ta watsa shirin bidiyo na kai tsaye da ma gajeren bidiyo a kan shafin intanet." Haka kuma Wu ya gano cewa, za a iya yayata dukkan abubuwa masu daraja na kauyen, kamar kayayyakin hannu da kuma wakokin gargajiyar kabilar Dong da aka rera yayin buga kayan kida na gargajiya mai suna Pipa, a dandalin bidiyo na kafar intanet cikin sauki da rahusa, wanda kuma za su amfanawa tattalin arziki.
Kuma, yana da wata dabara ta gina kauyen zuwa wani kayataccen wuri. Sai dai shirin na sa bai samu karbuwa daga sauran jami'an kauyen ba, wadanda 'yan gargajiya ne da ba su iya amfani da wayoyin zamani ba, bare kuma amfani da wayoyinsu wajen samun kudi. Ba su amince da shirin Wu ba, sun nace cewa, kiwo ya fi ma'ana a kan daukar bidiyo. Wu ya kara da cewa,
"Hakika, a farko, na gamu da wahalhalu masu dimbin yawa, ba su da tunani irin na zamani, har ma su kan kira ni 'Sakatare mai wasa da aiki'. Suna son gwada wasu sabbin hanyoyin bunkasuwa, amma ba su son gamuwa da hadari. Ganin hakan, sai na fada musu, ba matsala, ni zan cika gibin da za a iya samu idan shirin bai yi nasara ba." Daga baya Wu ya ranci yuan 50,000 kwatankwacin dala 7,143 daga kwamitin kauyen, inda ya yi alkawarin za a ba kwamitin ribar shirin. Ya kuma yi alkawarin cike gibin da za a iya samu idan shirin bai yi nasara ba. An yi ta ganinsa akai-akai yana daukar gajerun bidiyo da wayoyi biyu da kuma sandunan rike kyamara. Kyan yanayin kauyen, da abinci mai dadi, da fadan shanu na gargajiya da kuma nau'in tsarin gini na kabilar Dong, su ne abubuwan da bidiyon nasa suka fi mayar da hankali a kai. Sai dai, bidiyon ba su samu masu kallo sosai ba. Shafin nasa na da mabiya kimanin 1,000 kawai. Daga nan, sai rana ta musammam ta iso. Wu ya furta cewa, "Na samu labarin tatsuniya mai ban al'ajabi ta 'Aljanu Bakwai na kabilar Dong', wadda ta ba ni kwarin gwiwa sosai. Me zai hana ni neman wata tawagar mata ta kabilar Dong domin su zamo fuskokin kauyen?" Game da aikin zabar matan da suka dace, Wu ya ce ya kamata wadanda ke son shiga, su yi shiga mai kyau, kuma kada su nuna damuwa a gaban kyamara. Amma kaddamar da aikin ya ba shi wahala, babu wadda take gaskata shi, a ganinsu, Wu wani mayaudari ne. Wata mambar tawagar mata ta Aljanu Bakwai ta yi tsokacin cewa, "A lokacin da Sakatare Wu ya gayyace mu shiga cikin tawagar, lallai ba mu gaskata ba. Daga baya, da muka san cewa, ya zo kauyenmu ne don taimaka mana wajen fita daga kangin talauci, sai muka amsa gayyatarsa tare da shakku." Yang Yanjiao, babbar "aljanar" ita kadai ce matar aure a cikin tawagar. Karamar ciki kuma ita ce Wu Meiqiong mai shekaru 13, wadda ke zama da kakanninta. Duk da an musu lakabi da "Aljanu Bakwai na kabilar Dong", tawagar na da mambobi fiye da 7, wasu daga cikinsu dalibai ne. A dandalin bidiyo na Kuaishou, akwai sama da bidiyo 130 dake nuna ayyukan gona na tawagar, da suka hada da nome gona a lokacin bazara da shuka da girbi. Wu Yusheng ya yi bayanin cewa, "akwai abubuwa da dama da suka cancanci a dauka, amma tsarin rayuwa mai inganci na mazauna kauyen ne ya fi jan hankalin mutane". Kiwon kifi a fadama daddaden abu ne na gargajiya, dabarar noma irin ta kabilar Dong. Idan furen Shinkafa ya fada ruwa, kifin kan cinyesu, don haka, ake kiran kifin da Kifin Furen Shinkafa. Wu Lanxiang, mambar tawagar, ta ce bidiyo na farko da aka dauka kan yadda 'yan tawagar ke kamun kifin, ya samarwa kauyen sama da yuan 6,000, kwatankwacin dala 857, na kudin odar kifi. A ranar, kauyen ya sayar da dukkan kifayen.
Yanzu, dukkan mambobin tawagar na da shafi a manyan dandalin wallafa bidiyo na kasar Sin, ciki har da Douyin da Kuaishou da Huoshan, cewar Wu Yusheng. Ya sanya tawagar don yayata albarkatu da al'adun kauyen, ta hanyar shirin bidiyo na kai tsaye, kuma wannan na fadada kasantuwar kauyen a kafar intanet. Wata mambar tawagar ta furta cewa,
"Wani shirin bidiyonmu na dakika fiye da goma kawai na iya samu masu kallo fiye da miliyan goma, lallai lamarin ya kara mana kwarin gwiwa sosai. Haka kuma ta shirye-shiryenmu na bidiyo, ana iya kara fahimtar kauyenmu da al'adunmu, da ma zamansu, lallai aikinmu na da ma'ana sosai." Tawagar Aljanu Bakwai na kabilar Dong ta samu mabiya sama da 362,000 a dandalin Kuaishou. Aikin nasu ya samar da ribar sama da yuan miliyan 1, kwatankwacin dala 142,857, ga kauyen cikin shekara 1 da rabi da ya wuce. An samu kudin ne daga yawon bude ido da cinikin kayayyakin kauyen, kamar tufafin gargajiya da amfanin gona, kamar citta. Da yawa daga cikin iyalai masu fama da talauci sun samu tagomashi daga talar ta kafar intanet. Wu Meixiu, wata mazauniyar kauyen ta ce, "Iyalina da ma sauran iyalai 14 na kauyenmu mun hada kai wajen shuka citta a gona mai fadin murabba'in fiye da kadada daya, amma ba mu da dabarar sayar da su. Wannan shirin daukar gajerun bidiyo ya taimaka mana sosai, har ma mun sayar da dukkan citta kimanin kilogiram dubu 30 cikin wata guda kadai." Yanzu mambobin tawagar sun zama taurari a kafar intanet, kuma ba fice kawai suka yi ba, ta hanyar gajerun bidiyon, sun ba matan kauyen kwarin gwiwar fara kasuwanci, ciki har da bude dakunan cin abinci da na tufafi da shagon zubi da talla ta intanet. A baya, galibin matan kauyen manoma ne, ko kuma ma'aikata a birane. Kauyen ya kuma tara yuan 200,000 kwatankwacin dala 28,571, daga mazaunansa. An raba kudin zuwa hannayen jari 200, wanda kowanne ke da darajar yuan 1000, kwatankwacin dala 143. Kwamitin kauyen ya ce za a yi amfani da kudin wajen daukar gajerun bidiyo da raya bangaren yawon bude ido da aikin gona da sana'o'in hannu na kauyen.
Alfanun da shirin Aljanu Bakwai na kabilar Dong ya kawo ga tattalin arziki, ya yi gagarumin tasiri a kan mazaunan kauyen, cewar Wu Yusheng. Misali, karin mutane sun koma kauyen don neman damarmakin kasuwanci. Wu ya kara da cewa,
"Idan muka ambaci sakamako mafi kyau da aka samu a cikin shirin Aljanu Bakwai na kabilar Dong, to a ganina, shi ne yadda shirin ya wayar da kan mazauna kauyenmu masu fama da talauci, har ma suke da aniyar raya ayyuka bisa karfinkansu. " Amfani da dandalin gajerun bidiyo don yayata al'adun kabila da kayayyakin gargajiya da kuma taimakawa iyalai matalauta fita daga kangin talauci, abu ne da ake yayi yanzu, kuma shi ma yake bin yayin", cewar Wu Yusheng. Burinsa shi ne, tabbatar da al'adun kabilar Dong sun darsu a zukatan al'umma, kuma sun samu wurin zama a intanet, ta hanyar dandalin wallafa gajerun bidiyo.
Zuwa karshen bana, Wu Yusheng zai kammala wa'adin aikinsa a matsayin jami'in yaki da talauci a kauyen. Amma shirin Aljanu Bakwai na kabilar Dong zai sake farowa daga farko, maimakon zuwa karshe. Bayan cimma aikin fitar da kafatanin kauyen daga talauci, mataki na gaba zai mayar da hankali ne kan farfado da kauyen. Wannan kuma wani nauyi ne da ke bisa wuyan mambobin tawagar Aljanu Bakwai na kabilar Dong, wadanda ke nuna aniyarsu ta ci gaba da zama a kauyen don ci gaba da kokarinsu na gadon al'adun Dong da farfado da kauyen.(Kande Gao)