logo

HAUSA

Muhimman taruka biyu na kasar Sin na shekarar 2020

2020-05-21 08:56:34 CRI

Yanzu ta tabbata cewa, zaman zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ya gudana tsakanin ranakun 26 zuwa 29 ga watan Afrilu, ya amince da bude taron shekara-shekara, na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin NPC karo 13, tun daga ranar 22 ga watan Mayu a nan birnin Beijing.

Sakamakon tabbatar da wannan kuduri, za kuma a bude taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin al'ummar kasar Sin CPPCC karo 13, a ranar 21 ga watan na Mayu.

Zaman shugabancin kwamitin koli na CPPCC na baya bayan ya tabbatar da goyon baya ga wannan kuduri. A bisa wannan ci gaba, majalisar gudanarwar kasar Sin, ta ce ma'aikatu da sassan dake karkashinta, sun kammala nazartar sama da kaso 85 na shirye-shirye da shawarwari da 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC) da na 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar (CPPCC) suka bayar a 2019. Yayin wani taron manema labarai da ya gudana, Kakakin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, Xi Yanchun, ta ce hukumomin sun amsa shirye-shirye 7,162 ko kuma kaso 87.8 na jimilar shirye-shiryen da 'yan majalisar wakilan jama'ar kasar suka bayar da kuma shawarwari 3,281 ko kaso 85 na jimilar shawarwari da 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa suka bayar yayin zaman taron shekara shekara na majalisun biyu da ya gudana a watan Maris na 2019.

Sama da shirye-shirye da shawarwari 3,000 sassan majalisar gudanarwar suka amince da su, kana an aiwatar da sama da dabaru da matakai 1,500.

Ta kara da cewa, 'yan majalisar wakilan jama'a da 'yan majalisar bada shawara kan harkokin siyasa, sun gabatar da sama da shirye-shirye da shawarwari masu amfani 400 yayin da ake fama da cutar COVID-19, da nufin inganta tsarin kiwon lafiyar al'umma.

Muhimman tarukan biyu na bana dai, za a gudanar da su ne ta kafar bidiyo, a wani mataki na yaki da COVID-19, bayan da aka dage tarukan biyu da watanni 2 da 'yan kwanaki, biyowa bayan barkewar cutar COVID-19. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)