Wasan kwaikwayo Peking Opera da Kun Opera na kasar Sin
2020-05-21 11:34:36 CRI
Peking Opera, kungiyar wasan kwaikwayon gargajiya ce ta kasar Sin, wasa ne mai kayatarwa da ake gudanarwa da wani nau'in kida da waka da kayan ado da 'yan wasa ke sakawa, yana kuma cike da al'adun Sinawa. Wasan Opera yana nunawa 'yan kallo al'adun Sinawa, gami da wasu labarai, ta hanyar caba kwalliya da launuka daban-daban da kuma fasahohi.
Ganin yadda wasan ya samu karbuwa fiye da sauran wasannin kwaikwayon gargajiya na kasar Sin, kusan kowa ne lardi a kasar Sin, yana da sama da kungiya ko tawagar 'yan wasan Opera guda. Wasan Opera ya shahara tsakanin Sinawa, musamman tsoffi, wannan ne ma ya sa aka ayyana "Wasan Peking Opera".
Wasan Opera yana da tarihin kusan tsawon shekaru 200. Salon Wakar da ake amfani da ita a wasan, ya samo asali ne daga Xipi dake lardin Anhui da kuma Erhuang a lardin Hubei. Sannu a hankali aka rika sanya wasu dabaru daga sauran kananan wasannin Opera.
Kun Opera wani salo ne na rera wakoki, wanda aka ce wani Basine mai suna Wei Liangfu ya kirkire tun a zamanin daular Ming, a tashar bakin ruwa ta Taicang, amma salon na da kusanci da salon wakokin Kunshan dake da kusanci da tashar.
Salon gudanar da Kun Opera yana da kusanci da yadda ake gudanar da wakoki na dandali, a dakunan nuna fasahohi da dama na kasar Sin, ciki hadda irin su Peking opera, wadda ke da salo makusanci sosai da tsarin gudanar da Kun Opera.