logo

HAUSA

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

2020-05-20 11:30:54 CRI

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Bayan kwanaki sama da 100 da suka wuce da ake ba da darussa ta yanar gizo sakamakon bullar cutar COVID-19, daliban dake aji na uku na makarantun midil na birnin Beijing, wadanda yawansu ya wuce dubu 84 sun soma komawa makaranta. Kafin haka kuma, malaman makarantu daban daban sama da dubu 13 sun riga sun koma makaranta, inda suka yi kokari tare da sauran ma'aikatan makarantu wajen shiryawa sosai, don ba da tabbaci ga tsaron lafiyar dalibai. To, wane irin ayyuka ne suka yi? Kuma wane irin matakai suka dauka don maraba da komowar dalibai yadda ya kamata? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da yadda ake tabbatar da lafiyar dalibai a yayin da suke karatu a makaranta.

 

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Bayan mun shiga wata makarantar midil, mun gano cewa, an kafa wani dakin bincike na wucin gadi a gaban kofar makarantar, kuma akwai hanya daya tilo don shiga makaranta, ma'aikatan makarantar suna auna zafin jikin dukkan dalibai. Ban da wannan kuma, shugabanni da malamai da kuma masu aikin jinya suna tsayawa a kofar, don maraba da komowar dalibai, kana suna koya musu yadda za su nuna alamar lafiyar jiki ta wayar salula.

Bayan shiga makaranta, dalibai suna tafiya yankin koyarwa bisa hanyar da aka tsaida, kuma suna tabbatar da nisan kimanin mita 1.5 a tsakaninsu. Wata daliba ta gaya mana cewa, "Bayan mun shiga makaranta, akwai alamar dake nuna mana wace hanya za mu bi don zuwa azuzuwanmu. Ana iya ganin irin alamar kusan mita 2 zuwa 3. Hakan za mu iya shiga azuzuwa daban daban bisa hanyoyi daban daban, ta yadda za a hana taruwar dalibai."

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Domin biyan bukatun ka'idojin kwamitin ba da ilmi na birnin Beijing game da yakar cutar COVID-19 a yayin koyarwa. Dukkan makarantun birnin sun raba ko wane aji zuwa kananan azuzuwa guda biyu, amma ba a canja malamai da tsare-tsaren kwasa kwasai ba.

Malama Gao, shugabar makarantar midil da sakandare ta 19 ta bayyana cewa,

"Bisa tsarin da muka yi, duk azuzuwan da yawan dalibansu ya wuce 40, sai mu raba su zuwa azuzuwa guda biyu, hakan zai dace da bukatun kwamitin koyarwa, wato yawan daliban wane aji ba zai iya zarce 25 ba."

 

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Irin tsare-tsaren da aka yi, ya nuna cewa, malami guda daya zai ba da darasi ga azuzuwa guda biyu a lokacin guda, to, ta yaya za a tabbatar da ingancin koyarwa? Mataimakiyar shugabar makarantar malama Wan ta ce,

"Muna tabbatar da hakan ne ta hanyar amfani da manhajar ba da darasi kai tsaye ta yanar gizo, malami yana koyarwa a wani aji, daliban dake aji na daban sun iya kallo ta yanar gizo. Mun ajiye kamara a dukkan kamputan dake azuzuwa, ta hakan malamai suna iya bude bidiyo, don duba yadda wadannan daliban suke, har ma su musu tambayoyi game da ilmin da aka koyar, ta yadda za a cimma burin ba da darasi ga daliban dake azuzuwa guda biyu kamar dukkansu na samun ilmi a ajin bai daya, ta hakan ake tabbatar da ingancin koyarwa."

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Ban da koyarwa, kuma batun ingancin abinci shi ma wani muhimmin aiki ne na makarantu. Ba kamar yadda aka yi a da ba, yanzu akan kunshe abincin, kuma kafin a raba, dole ne a tabbatar da zafin abinci ya kai sama da gidiri 60, ta yadda za a iya hana yaduwar cututtuka a cikin abinci.

Lokacin cin abincin tana ya yi, mun gano cewa, dalibai sun shigo dakin cin abinci daga kofofi daban daban, kuma babu mu'amalar jikinsu ko kadan ba. An ajiye hankicin takardun fida kwayoyin cuta, tsinken cin abinci na Sinawa da ba za a sake amfani da shi ba, ruwan sha da kuma wata takardar gargadin tsaron lafiya. Ban da wannan kuma, an rubuta sunayen dalibai a kan teburi, bayan sun zauna, sai su cire marufin baki da hanci, daga baya sai su soma cin abinci.

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Daraktan ofishin makarantar malam Wang ya bayyana cewa,

"Mun zana layi a cikin dakin cin abinci, don tabbatar da nisa a tsakanin dalibai. Bayan sun shigo, sai su wanke hannu tukuna, daga baya sai su dauko abinci da kuma zama a kujerun da aka ajiyewa kowannensu. Baya ga haka, ma'aikata za su gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta sau da dama akan lokaci." Bisa labarin da muka samu, an ce, nan gaba hukumomin sa ido za kuma su kara karfin bincike kan kasuwanni ko kantuna masu sayar da abinci dake dab da makarantu, don tabbatar da ingancin abinci, ta hakan za a iya tabbatar da lafiyar dalibai a dukkan fannoni.

Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing

 

Gaskiya tun rana ta farko da dalibai suka koma makarantu, duk abubuwa sun canja bisa na da. Game da haka, wata daliba ta gaya mana cewa,

"An dade ban ga abokai na dalibai ba, yanzu ina farin ciki sosai saboda zan iya karatu tare da su. Ina fata za mu iya kokari tare da malamanmu, don cimma nasarar shiga makarantar sakandare da muke so." Wata mahaifiya ta ce,

"Muna ta zura ido kan bude makarantu. Lallai makarantar ta yi shari sosai, hakan ya sa na kwantar da hankali na."