logo

HAUSA

LARDIN SHAANXI NA SHIRIN MAYAR DA WASU WASANNI KAN YANAR ZIGO

2020-05-15 13:39:59 CRI

LARDIN SHAANXI NA SHIRIN MAYAR DA WASU WASANNI KAN YANAR ZIGO Mahukunta a lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin, sun bayyana aniyar su ta aiwatar da wata manufa ta mayar da wasu gasanni da ake gudanarwa zuwa yanar gizo, a wani mataki na tabbatar da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma tabbatar da kare lafiyar masu shiga wasannin. Bisa tsarin da aka tanada, hukumar wasanni a lardin ta ce, za a fara gasanni da a abaya aka dage, tun daga watan nan na Mayu da muke ciki. Da yake cutar COVID-19 ta fara sauki kwarai a lardin na Shaanxi, hukumar wasannin lardin ta sanar tun a ranar 19 ga watan Maris cewa, za a bude wuraren gudanar da wasanni, za kuma a koma gudanar da su tare da ci gaba da aiwatar da matakan kandagarkin yaduwar cutar. Bugu da kari lardin Shaanxi, zai karbi bakuncin gasar kasa ta Sin karo na 14 a shekarar 2021 dake tafe, don haka ne hukumar wasannin lardin ta ce, za ta tabbatar an mayar da wasu daga gasannin da za a buga zuwa yanar gizo, yayin da shirye shiryen karbar bakuncin wannan gasa ke kara kankama. Baya ga karbar bakuncin gasanni ta yanar gizo, lardin zai kuma gayyaci wasu taurari a fannin wasanni, domin su jagoranci wasannin motsa jiki kan yanar gizo a azuzuwa da aka tsara, ta yadda mutane dake gidajen su za su yi koyi, su kuma motsa jiki a gida. BIRANEN SIN SUN BAIWA AL'UMMA DAMAR AMFANI DA WURAREN MOTSA JIKI KYAUTA A RANAR HUTUN MA'AIKATA Guo Liru ta yi mamaki mai faranta rai, a lokacin da ta isa zauren buga wasan badminton dake jihar Mongolia ta gida a karshen mako, inda ta je domin buga wasa tare da abokan ta. Guo Liru ta ce "Mun yi farin ciki da kasancewa za mu buga wasa yau kyauta a nan, mu kan biya yuan 40, kwatankwacin dalar Amurka 5.67 a kowace sa'a, a duk karshen mako" a irin wannan fili daya, na buga wasan badminton. A raneku 5 na hutun ranar ma'aikatan nan, wannan cibiyar wasanni ta ba mu damar buga wasa kyauta, tsakanin karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma. Da yake karin haske game da hakan, daya daga ma'aikatan wannan cibiya Wang Danfeng, ya ce "Mun samar da wuri da kayan wasa, ciki hadda wadanda ake yi a rufaffen wuri kamar badminton, da kwallon tebur ko table tennis, da sauran kayan motsa jiki, da ma wadanda ake yi a waje kamar kwallon Kwando ko basketball, da filin kwallon kafa, tun daga ranar 1 zuwa 4 ga watan Mayu. Wang Danfeng ya kara da cewa "Muna fatan karfafa gwiwar karin mutane don su shiga motsa jiki, muna ba su karin damammakin yin wasu abubuwa a wannan lokaci na hutu,". Akwai karin cibiyoyin wasanni da filayen motsa jiki da dama a kasar Sin da suka dauki irin wannan mataki, na bada damar amfani da wuraren kyauta ga masu motsa jiki a lokacin na hutu. Cibiyar motsa jiki ta Nantong dake lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin, ita ma ta dauki wannan mataki na baiwa masu wasan badminton, da kwallon tebur, damar wasa kyauta tsakanin ranekun 1 zuwa 3 ga wana Mayu, ta kuma samar da takardun shiga wasan ninkaya 200, da na motsa jiki ga al'ummar yankin da cibiyar take. Kaza lika filin wasa na Xiamen, shi ma ya ba da damar shiga wuraren motsa jiki dake cikin sa kyauta a wadannan raneku na hutu. GHANA (FA) TA CE ZA A CI GABA DA DAGE WASANNI SABODA COVID-19 Hukumar gudanar da wasannin kwallon kafa na kasar Ghana ko GFA a takaice, ta sanar da cewa, za a ci gaba da dage wasannin kakar kwallon kafa ta 2019 zuwa 2020, saboda kokarin da mahukuntan kasar ke yi na dakile yaduwar cutar COVID-19. GFA ta dage wasannin ne tun a ranar 16 ga watan Maris, inda ta ce sai wani lokaci nan gaba za a sanar da lokacin sake komawa gasar kakar ta 2019 zuwa 2020, bayan da gwamnati ta sanar da umarnin rufe dukkanin wasu tarukan al'umma a kasar. Hukumar zartaswa ta GFA ta ce za a ci gaba da aiwatar da wannan mataki ne, yayin taron manema labarai da ya gudanar a tsakiyar makon jiya. Hukumar ta ce za ta ci gaba da sanya ido kan yanayin da ake ciki, ya zuwa ranar 30 ga watan Yuni, lokacin da za a sake nazartar halin da ake ciki, a kuma dauki mataki gwargwadon hali. GFA ta ce za ta lura da dukkanin yanayi a lokacin da ya dace, su kuma dauki matakai mafiya dacewa domin tabbatar da cewa, dukkanin masu shiga gasannin kwallon kafar kasar sun kammala gasar lami lafiya. A halin da ake ciki dai GFA na gudanar da gangamin wayar da kan al'umma game da yaki da cutar COVID-19, tun lokacin da aka samu bullar cutar a Ghana. 'YAN WASAN FLAMENGO 3 SUN HARBU DA CUTAR COVID-19 Yanzu haka dai an shiga wani yanayi na rashin tabbas, game da komawa gasar ajin kwararru ta kwallon kafar kasar Brazil, bayan da aka tabbatar da harbuwar 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Flamengo su 3 da cutar COVID-19. Cikin wata sanarwa, kungiyar Flamengo ta ce an gwada mutane 293 tsakanin ranar 30 ga watan Afirilu zuwa 3 ga watan Mayun nan, inda aka samu cikin su 38 sun harbu da cutar. A cewar Flamengo, cikin wadanda aka samu da cutar, 36 ba su nuna alamu ba, sai kuma 2 da suka nuna alamun fama da cutar. Ba a dai bayyana sunayen 'yan wasan da suka harbu da cutar ba. Baya ga 'yan wasan an kuma ce, akwai wasu karin masu taimakawa 'yan wasa su 6 da suka kamu da cutar, da kuma wasu ma'aikatan kungiyar daban su 2 da suke aiki a wani kamfani da kungiyar ke mu'amala da shi, da kuma iyalan 'yan wasan da ma'aikatan kungiyar mutum 25. Kungiyar wadda ke rike da kofin kalubale na gasar Serie A da Copa Libertadores na Brazil, ya ce za a umarci wadanda suka harbu da cutar su killace kan su har sai lokacin da gwaji na gaba ya nuna sun warke daga cutar. Sanarwar ta kara da cewa "Kungiyar mu tana hadin gwiwa da gwamnatoci da mahunta, domin tabbatar da kiyaye ka'idoji da doka, za su kuma ci gaba da aiki kafada da kafada, domin tabbatar da an koma kwallon kafa nan ba da jimawa ba,". An dai dakatar da taka leda a Brazil tun tsakiyar watan Maris, lokacin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar COVID-19 a matsayin cutar da ta zamo ruwan dare game-duniya. Flamengo ta gudanar da gwaji ga 'yan kungiyar ta, bayan da hukumar kwallon kafa ta Rio de Janeiro ta bawa kulaflika damar komawa horo. Kuma Flamengo ta ce nan gaba cikin makon nan za su fara horo. A farkon makon jiya ne dai daya daga dadaddun masu yiwa 'yan wasan Flamengo tausa mai suna Jorge Luiz Domingos, ya rasu yana da shekaru 68 a duniya, bayan da ya harbu da cutar COVID-19.

Kawo yanzu Brazil na da masu dauke da COVID-19 har mutum 126,000, ciki hadda mutane 8,588 dake cikin mawuyacin hali sakamakon harbuda da ita. (Saminu Alhassan, Amina Xu)