logo

HAUSA

Xi ya zanta da takwarorinsa na Koriya ta Kudu da Sri Lanka

2020-05-14 11:45:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in ta wayar tarho da yammacin jiya Laraba. Yayin zantawarsu, Xi ya jaddada cewa, duba da irin matukar kokarin da aka yi, cutar numfashi ta COVID-19 na yin sauki sosai a Sin da Koriya ta Kudu.

Ya ce yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar, kasashen biyu sun zama tsintsiya madaurinki daya, wajen baiwa juna taimako da goyon-baya. Kaza lika kasar Sin na son ci gaba da hada kai tare da Koriya ta Kudu, a fannonin da suka shafi kandagarkin annobar, da nazarin magani da allurar rigakafin cutar, da marawa hukumar WHO baya, don taka rawarta yadda ya kamata, da kara tuntubar juna a karkashin tsarin MDD, da kungiyar kasashen G20, da kungiyar ASEAN, da tsarin hadin-gwiwar kasashen Sin da Japan, da Koriya ta Kudu, a wani kokari na fadada hadin-gwiwarsu, a fannin yaki da yaduwar cutar.

A dai wannan rana, shugaba Xi ya kuma zanta da takwaransa na kasar Sri Lanka Gotabhaya Rajapaksa. (Murtala Zhang)