logo

HAUSA

Hadin gwiwar Sin da Afirka na yaki da COVID-19

2020-05-14 08:37:02 CRI

Alkaluma na baya bayan nan da cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta (Africa CDC) ta fitar sun nuna cewa, adadin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya kai 69,578, baya ga sama da mutane 2403 da cutar ta hallaka a sassan nahiyar.

Alkaluman cibiyar ta Africa CDC sun nuna cewa, kasashen da annobar COVID-19 ta fi yin kamari a nahiyar Afrika sun hada da Masar, Afrika ta kudu, Morocco da Algeria. Kuma wannan bai hana kasar Sin da kamfanonin kasar da ke nahiyar Afirka hada kai wajen ganin bayan wannan annoba tare ba.

Ya zuwa yanzu, Africa CDC ta karbi kashi na uku na gudummowar kayayyakin kiwon lafiya daga gidauniyar attajirin kasar Sin Jack Ma da Alibaba domin taimakwa kasashen wajen yaki da annobar COVID-19, matakin da ke kara bayyana alakar kasashen Sin da Afirka na yaki da wannan annoba. Bugu da kari, gwamnatin kasar Sin ta tura tawagogin ma'aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka don ganin bayan wannan annoba, da shirya taruka ta kafar bidiyo tsakanin masana'an lafiyar kasashen biyu, kan matakai da fasahohin yaki da cutar COVID-19. Baya ga tallafi a bangaren gwamnati da kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka kan yaki da wannan annoba, shi ma kamfanin Huawei ya yi alkawarin taimakawa kokarin nahiyar Afrika, wajen dakile yaduwar cutar COVID-19.

Cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar Standard, shugaban kamfanin mai kula da yankin kudancin Afrika Chen Lei, ya ce tsarin kamfanin na kiran taro da kafar bidiyo dake hada mutane da dama, ya taimaka wajen inganta tsarin sadarwa a asibitoci.

Ya kara da cewa, sun kuma fara amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wajen saukaka ayyukan duba marasa lafiya a asibitoci. Yana mai cewa, za a iya nazarin hoton CT Scan cikin mintuna 2, abun da ya kara saurin aikin da kaso 80, lamarin ke da muhimmanci wajen ceton rayuka.

Ya ce kamfanin sadarwar na kasar Sin, zai ci gaba da amfani da karfin fasahar sadarwa wajen taimakawa kokarin nahiyar na yaki da COVID-19. Duk wadannan sun kara shaidawa duniya cewa, babu abin da zai taba zumuncin dake tsakanin sassan biyu. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)