logo

HAUSA

Manyan jami'an gwamnatin Sin za su halarci manyan taruka 2 ta bidiyo

2020-05-14 10:48:54 cri

Manyan jami'an gwamnatin kasar Sin, za su halarci manyan taruka 2 dake tafe nan da 'yan kwanaki ta kafar bidiyo. A yayin tarukan da kasar ta gudanar a baya dai, jami'an hukumomi, da na ma'aikatun gwamnatin kasar, na shiga dakunan gudanar da tarukan majalissar wakilan jama'a, da ta ba da shawara kan harkokin siyasa. To sai dai kuma a wannan shekara, jami'an za su gabatar da bayanai ne ta kafar bidiyo, a wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19.

Taron majalissar zartaswa da firaministan Sin Li Keqiang ya jagoranta a jiya Laraba, ya ce lura da yanayi na musamman da ake ciki, ya zama wajibi gwamnati ta aiwatar da karin matakai mafiya dacewa, na jin ra'ayin jami'an gwamnati, da kuma shawarwarin da suke da su.

Wata sanarwa da taron ya fitar ta bayyana cewa, an amince ta hanyar sadarwar bidiyo, da wayar tarho da yanar gizo, jami'an gwamnati za su bukaci sanin hasashen yanayin kasuwanni da alakar su ga rayuwar jama'a.

A bana dai za a bude zaman majalissa mafi girma ta Sin, wato majalissar wakilan jama'ar kasar Sin a ranar 22 ga watan nan na Mayu, kafin nan za a bude zaman majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasa a ranar 21 ga watan, bayan da aka dage tarukan biyu da watanni 2 da 'yan kwanaki, biyowa bayan barkewar cutar COVID-19.

Sanarwar ta kara da cewa, yayin da ake tunkarar yanayi mai tsanani kuma mai sarkakiya a bana, majalissar zartaswar ta ce, ya wajaba a yi amfani da hikima da basirar 'yan majalissar kasar da ma bangaren mashawartan kasar, wajen inganta ayyukan gwamnati.

Majalissar ta kuma yi fatan ganin an aiwatar da dukkanin manufofin ci gaba zuwa ayyuka na zahiri, wadanda za su warware matsaloli masu wahalar gaske. (Saminu)