logo

HAUSA

Sama da zuriyoyi hudu: Ruhin aikin sa kai na dashe cikin wani iyali dake yankin Xicheng a Beijing

2020-05-12 16:00:18 CRI

 

Sama da zuriyoyi hudu: Ruhin aikin sa kai na dashe cikin wani iyali dake yankin Xicheng a Beijing

Akwai wata kungiyar mata masu aikin sa kai da ke yankin Xicheng na birnin Beijing, wadda ake kiranta "Xicheng Dama". Wadannan masu aikin sa kai na sanya jar riga da hula da jan kyalle a damtse, wadanda suke taimakawa wajen kiyaye tsaron al'umma da hidimtawa al'umma, ta yadda za su yi rayuwa hankali kwance. Galibin 'yan kungiyar "Xicheng Dama" sun fito daga irin ko wane iyalai da aka saba gani. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da labarin kan zuriyoyi hudu na iyalin Wang Huili, wadanda dukkansu 'yan kungiyar ne.

Kalmar "Dama" da Sinanci na nufin "Goggo". Shin dukkan 'yan kungiyar "Xicheng Dama" Goggonni ne? Madam Wang Huili ta yi bayanin cewa, idan ana zancen 'Xicheng dama', ana nufin alama, kuma wannan alama na nufin kungiyar masu aikin sa kai dake hidimtawa unguwanni a yankin Xicheng. A gaskiya, masu aikin sa kai na kungiyar Xicheng Dama sun hada da mata da maza. Galibin 'yan kungiyar mata ne da suka yi ritaya, kamar ita. Amma akwai wasu matasa. "Xicheng Dama" na nufin kungiyar masu aikin sa kai, da a shiye suke su samar da hidimomi daban-daban domin kyautata rayuwar mazauna yankin Xicheng. Madam Wang Huili ta kara da cewa, 'Yan kungiyar "Xicheng Dama" na iyakar kokarinsu wajen yin komai da kyau, duk kankantarsa. Masu tasowa na gadon ruhin "ka yi duk abun da za ka iya, kuma ka yi shi iya yinka". Kakanta Wang Zhichao, shi ne zuriya na farkon zama 'yar kungiyar "Xicheng Dama" a cikin iyalinta.

Sama da zuriyoyi hudu: Ruhin aikin sa kai na dashe cikin wani iyali dake yankin Xicheng a Beijing

A shekarun 1970, Wang Zhichao ya yi aiki a matsayin daraktan kwamitin unguwar Shuguang, wanda a yanzu ake kira Unguwar Baiwanzhuang ta gabas. A wancan lokaci, Wang Huili 'yar makaranta ce. Bisa abun da ta tuna, ta ce ayyuka sun yi wa kakanta yawa.

Wang Huili ta tuna da cewa, "an saba makwatanmu na ziyartarmu a gida da yamma. Wani lokaci, suna da 'yan uwa, wadanda suka kawo musu ziyara daga wasu wurare daban. Suna bukatar kakana ya taimaka musu da takardar shaidar zama, don 'yan uwansu su zauna a unguwar a Beijing. Akwai kuma wadanda 'yan uwansu ke zuwa Beijing don ganin likita. Su kan nemi kakana ya taimaka musu idan irin wadannan kananan bukatun sun taso. A shirye kakana yake ya taimaka musu a ko da yaushe. Har ma ya taimakawa wajen gina wata karamar masana'anta, ta yadda matan unguwar za su sarrafa jankunan yadi na zuba fulawa domin su samu kudi." Mahaifiyar Wang Huili, Liu Guifen, ita ce zuriya ta biyu da ta yi aiki a kungiyar "Xicheng Dama". A shekarun 1990, Liu ta fara aiki a kwamitin unguwa. Aikin Liu shi ne kula da muhallin unguwar da kuma taimakawa wajen kula da tsaro. Wang Huili ta ce ta koyi daukar aiki da muhimmanci, da jajircewa a matsayin mai aikin sa kai ne daga wajen mahaifiyarta, da kuma kakanta.

Sama da zuriyoyi hudu: Ruhin aikin sa kai na dashe cikin wani iyali dake yankin Xicheng a Beijing

Bisa ka'idar raya unguwannin al'umma, 'yan kungiyar "Xicheng Dama" sun dauki gagarumin alhakin taimakawa mazauna yankin Xicheng kara rayuwa cikin amince da kwanciyar hankali a cikin unguwarsu. Baya ga tabbatar da tsaron al'umma, masu aikin sa kai na bada muhimmanci sosai ga rayuwar tsoffi. Sun tsara shirye-shirye da dama na kyautata rayuwarsu bayan sun yi ritaya.

Wang Huili dake cikin shekaru 60, ita ce zuriya ta 3 a kungiyar "Xicheng Dama" daga iyalinta. Tun daga shekarar 2002, ta ke aiki a kwamitin unguwar titin Wenxing, karkashin yankin Zhanlanlu. Yanzu, ita ce mataimakiyar Sakatare Janar na kungiyar tsoffin yankin Zhanlanlu. Cikin shekarun da suka gabata, Wang Huili ta yi aiki tukuru, kana ta fahimci kowanne iyali dake unguwar. Ta yi ta karanta bayanan da aka adana na kowanne iyali dake da rajista a unguwar sau da dama. Idan 'yan unguwar suka zo neman taimako, Wang ta kan yi saurin lalubo bakin zaren matsalolinsu. Ta ce masu aikin sa kai na kungiyar "Xicheng Dama" na da nauyi da dama a wuyansu, ciki har da taimakawa wajen tabbatar da tsaro da kiyaye gobara da kula da tsoffi da shiga cikin ayyukan kare muhalli. Wang Huili kan lika sanarwa a wajen shiga gidaje domin tunatar da mazauna su rika duba kofofi da tagogi da makunnin gas da na ruwa da na lantarki kafin su fita. Idan aka yi sabbin zuwa a unguwar, Wang kan ziyarce su, ta kuma ba su lambobin masu aikin sa kai, don su san wanda za su kira in suna bukatar taimako. A kai a kai Wang ke duba kayyakin samar da wuta a unguwar don tabbatar da suna aiki da kyau. Ban da haka, Wang Huili na iyakar kokarin kyautata rayuwar tsoffi. Ta kan tsara yadda tsoffin za su shiga shirye-shiryen gargajiya, kamar shirye shiryen fasahohin fenti da na rubutu da na yanka takarda da fasahohin hannu da sauransu. Har ila yau, ta kan tsara yadda masu aikin sa kai za su kula da mazauna tsoffi, wadanda ba sa tare da 'ya'yansu. Wang Huili ta ce, "muna da wani ayari na masu aikin sa kai a kungiyarmu. Ayarin na dafa abinci masu dadi, wanda ake kai wa gidajen tsoffi dake unguwar. Muna ziyartar gidajen tsoffi a lokutan hutu, kuma mu yi hira da su don sanya su farin ciki. Idan suka yi rashin lafiya, mu kan kai su asibiti don su samu kulawa da wuri". A lokacin Bikin Bazara na bana, yayin da mutane a fadin kasar Sin ke yaki da annobar Corona, kungiyar kula da tsoffi ta titin Zhanlanlu, ta tattara zanen fenti da rubutun da tsoffin unguwar suka yi. Wang Huili ta wallafa wasu daga cikin zanen fentin wadanda ke bayyana yadda masu aikin sa kai ke aiki a cikin unguwar wajen kiyaye lafiyar mazauna, a shafinta na WeChat. Madam Wang ta furta cewa, "ina son yin iya kokarina wajen yin dukkan ayyukan yau da kullum da kyau. A matsayin 'yar kungiyar masu aikin sa kai ta "Xicheng Dama", ina son kasancewa tare da tsoffin dake unguwarmu, don sanya su farin ciki." Tsoffin unguwar suna yaba kirkinta, inda suke daukarta tamkar 'yar uwarsu.

Sama da zuriyoyi hudu: Ruhin aikin sa kai na dashe cikin wani iyali dake yankin Xicheng a Beijing

Wang Huili na jin dadin ayyukanta, da rayuwarta. Ayyukanta sun yi tasiri a kan 'yarta Lou Shanshan, wadda ita ma ta zama mai kula da walwalar jama'a, a kwatimin yankin Zhanlanlu, a shekarar 2018. Lou ita ce zuriya ta 4 na iyalinta a kungiyar "Xicheng Dama". Ita ce aikin kula da tsoffin unguwar Baiwanzhuang ta yamma, ya rataya a wuyanta.

Lou ta fahimci yanayin unguwar yayin da take tasowa. Yayin da take intabiyun neman aiki, an tambaye ta ko ta san me ake bukatar mai kula da walwalar jama'a ya yi, kuma ko ba za ta damu ba idan ana bukatar ta kara lokacin aiki. Lou ta amsa ba tare da wani jinkiri ba cewa, "sosai, na sani. Hakika, na san yanayin tun ina karama, saboda mamata ta yi wannan aikin". Zuriyoyi 4 na iyalin Wang Huili sun fahimci juna sosai, kuma suna iyakar kokarinsu wajen taimakawa juna. Iyalin sun yi ammana cewa, aikin sa kai na taimakawa unguwar da suke zama, kara samun aminci da kwanciyar hankali. Ruhin 'yan kungiyar "Xicheng Dama" wanda ke jaddada jajircewa da sadaukarwa, na dashe a cikin zukatansu.

"Aikin sa kai alama ce mai muhimmanci ga ci gaban al'ummarmu. Iyalina na aiki tukuru wajen nuna kaunarmu ga kasarmu. Za mu ci gaba da bin kyawawan al'adun iyalinmu, wajen gina babban iyali mai aminci a unguwarmu," Cewar Madam Wang Huili. (Kande Gao)