logo

HAUSA

Prof. Isa Sadiq Abubakar: Dabarun kasar Sin na yakar cutar COVID-19 abubuwan koyi ne

2020-05-12 14:08:54 CRI

Prof. Isa Sadiq Abubakar: Dabarun kasar Sin na yakar cutar COVID-19 abubuwan koyi ne

A makon da ya gabata, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da Prof. Isa Sadiq Abubakar, babban darekta a cibiyar nazarin cututtuka dake yaduwa tsakanin al'umma a jami'ar BUK dake jihar Kano a tarayyar Najeriya, inda Prof. Isa Abubakar ya bayyana matukar kokarin da gwamnatin jihar Kano take yi domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Har ma ya bada shawarwari ga al'ummar arewacin Najeriya don dakile yaduwar annobar a daidai wannan lokaci na watan azumin Ramadan.

Prof. Isa Sadiq Abubakar: Dabarun kasar Sin na yakar cutar COVID-19 abubuwan koyi ne

A ci gaban hirar tasu a wannan mako, Prof. Isa Abubakar ya yi karin haske kan matakai filla-filla da ya kamtata mutane su dauka domin kare kawunansu daga harbuwa da cutar, sa'annan ya jinjinawa gwamnatin kasar Sin saboda namijin kokarin da ta yi wajen kandagarkin yaduwar cutar, gami da goyon-baya da tallafin da Sin ta samar ga kasashen Afirka a wannan fanni.(Murtala Zhang)