logo

HAUSA

Dalilin da ya sa aka ga bayan COVID-19 a birnin Wuhan

2020-05-08 21:12:54 CRI

A kwanakin baya, Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi maraba da labarin dake cewa, babu wani mai dauke da cutar COVID-19 dake kwance a asibitin birnin Wuhan na kasar Sin, inda ta jinjinawa namijin kokarin da kasar ta yi wajen dakile annobar.

Bayan shafe sama da watanni 3 ana yaki da cutar, yanzu a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar Sin, da ya taba kasancewa inda cutar COVID-19 ta fi kamari, an sallami dukkan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 dake kwance a asibiti, bayan sun warke, to, sai dai mene ne dalilin da ya sa ake samun wannan nasara a birnin. Sani Ibrahim, dalibi dake karatun digiri na 3 a birnin zai yi mana karin bayani dangane da batun.