logo

HAUSA

Prof. Isa Sadiq Abubakar: Jihar Kano ta dukufa wajen dakile yaduwar COVID-19

2020-05-05 14:32:38 CRI

Prof. Isa Sadiq Abubakar: Jihar Kano ta dukufa wajen dakile yaduwar COVID-19

Kwanan nan, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da Prof. Isa Sadiq Abubakar, babban darekta a cibiyar nazarin cututtuka dake yaduwa tsakanin al'umma a jami'ar BUK dake jihar Kano a tarayyar Najeriya. Prof. Isa Abubakar ya ce, yanzu cutar mashako ta COVID-19 na bazuwa zuwa arewacin Najeriya, kuma gwamnatin jihar Kano tana daukar kwararan matakai daban-daban domin dakile yaduwar cutar.

Prof. Isa Sadiq Abubakar: Jihar Kano ta dukufa wajen dakile yaduwar COVID-19

Har ma ya bada shawarwari ga al'ummar arewacin Najeriya don dakile yaduwar annobar a daidai wannan lokaci na watan azumin Ramadan. Prof. Isa Abubakar ya fara ne da bayyana yadda arewacin Najeriya ya samu kansa game da yanayin yaduwar annobar numfashi ta COVID-19.(Murtala Zhang)