logo

HAUSA

La Liga ta rattaba hannu kan kwantiragi da kamfanin Douyin na Sin mai mallakar dandalin sada zumunta

2020-04-30 17:06:29 CRI

Hukumar dake kula da gasar kwallon kafa ajin kwararru ta Italiya La Liga, ta amince da yin hadin gwiwa da kamfanin Douyin na Sin dake mallamar dandalin sada zumunta, matakin da zai baiwa kamfanin damar kasancewa abokin huldar La Liga a hukumance, daga yanzu zuwa watan Maris na shekarar 2021 dake tafe. La Liga na fatan wannan yarjejniya za ta bata damar samun Karin karbuwa tsakanin Sinawa, kasar da kawo yanzu ke da mabiyan kafar kamfanin sama da miliyan guda. Wata takardar bayani da La Liga ta fitar ta ce "Da wannan yarjejeniya La Liga ta kara matsawa gaba, a kokarin ta na fadada harkokin ta a Sin, wadda kasuwa ce mai daraja a wurin mu, kuma kasa inda karbuwar mu ta ninka a kakar wasanni ta bara." Takardar bayanin ta ce "Muna matukar farin ciki da kasancewa tsarin gasar kwallon kafa ta farko a duniya, wadda ta shiga irin wannan yarjejeniya da kamfanin Douyin, wanda hakan zai sa mu kai ga Karin masu cudanya da mu, mu kuma samu Karin kallon wasannin mu ta kafar bidiyo." A cewar wata sanarwa da daraktan sashen tsare tsare a fannin yanar gizo na La Liga ya fitar "Karin kulaflikan La Liga na fatan kulla irin wannan alaka da kamfanin Douyin; Tuni dai kulaflikan Atlético Madrid, FC Barcelona, RCD Espanyol, Barcelona, Real Madrid, Real Sociedad da Valencia CF suka samu damar hawa dandalin sada zumunta na kamfanin. Da yake tsokaci kan hakan, dakartan wasanni na kamfanin Douyin Ye Jueming, ya ce kamfanin sa na fatan habaka bangaren wasanni ta hanyar amfanin da fasahohin sadarwa, wadanda za su ba da dama amfani da bayanai, da kayayyaki da za su taimakawa wasannin su sadu da karin jama'a, ta yadda za su kara sabawa da gasar ta La liga." Jami'in ya kara da cewa, hadin gwiwar zai sanya LaLiga shiga gaban tatakwarorinta ta fuskar tsare tsaren fadada harkoki ta yanar gizo a kasar Sin, inda da ma ta fara samun karbuwa tsakanin al'umma.

A yanzu haka dai an dakatar da gasannin kwallon kafar Sifaniya, sakamakon yaduwar cutar COVID-19, amma La Liga na fatan sake komawa buga wasanni a karshen watan Mayu, ko farkon watan Juni, duk da dai cewa mai yiwuwa za a buga sauran wasannin ba tare da 'yan kallo ba, ya zuwa karshen wannan shekara.